Sashe 11
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin mari da ya yi kukan kura ya kaura mata, ya sanya ta kasa ƙarasa maganar. Lokaci guda ta daina ganin haske, har sai da walƙiya ta gifta mata. Kanta ya yi mata nauyi. Kafin ta gama dawowa cikin hayyacinta ta ji ya rufe ta da duka ta ko ina."Mara mutunci 'yar iska har kin isa ki zagi Mahaifiyata?"
"Iyayenka sun fi nawa ne? Wane irin zagi ne ba ka yi wa nawa ba?" Ta yi masa tambayar cikin kuka.
"Wallahi ai ko ban kashe ki ba sai na kusa banza kaka kawai." Dukanta yake yana haurinta tana ihu amma bai kula ba.
Rashida ganin zai yi kisa, domin a lokacin ta suma sai ta riƙe hannunsa ta ce,"Faruk, za ka yi kisa domin dukan da kake mata ba na wasa bane, kar ka aikata abin da za ka yi nadama." Ta ce masa tare da kama hannunsa.
Huci yake kamar mesa ya ƙara yin kanta. Da sauri ta kama hannunsa tare da ɗaukar ruwa a frij ta yayyafa mata. Ganin ta saki ajiyar zuciya ta farfaɗo, sai ya ce,"Ki bar ni na kashe shegiya tun da har za ta iya zagin iyayena, kuma ki je ba zan ƙara zama dake ba, na sake ki saki ɗaya."
A lokacin da ya furta sakin Rashida ta ɗauka duka zai yi mata, ganin yadda ya harzuƙa yana huci kamar mesa, amma jin ya yi ɗaya sai ta lalle shi kawai.
Nasreen kuwa ji ta yi kamar an yaye mata ƙaya. Furta sakin ya sanya ta cikin farinciki, domin ba ta taɓa tunanin zai aikata ba. Ƙoƙarin miƙewa ta yi amma sai ta ji ta kasa sakamakon ƙafafuwan ta da ya sanya ƙafarsa ya taka.
Hannunsa ya sanya ya ƙara har ƙofar gida, sannan ya kwaso su Raihan da suke kuka. "Ki bar minii gida kuma wallahi tsinke ba zan bari ki ɗauka ba, tun da matsiyacin uban ki bai kawo ki da komai ba, sannan yaran nan ba zan riƙe su ba, saboda ba ina so kika haife su ba." Yana gama faɗin haka ya maimda ƙofa ya rufe.
Kuka ta sakin mawuyacin halin. Raihan ta duƙa tare da kama hannunta."Umma, ba ki da hijabi ya koro ki, kuma mutane suna wucewa. Ki tashi muje gidan Maman Muwaddat ki sanya hijabi." Ta ce tana share mata hawaye.
"Ba zan iya tashi ba, je ki kira mini ita." Ta furta cikin kuka. Da gudu yarinyar ta ruga tana share hawaye.
Tana ƙoƙarin shiga cikin gidan suka ci karo da ita, wacce tun da ta ji ƙarar dukan ta tsaya a harabar gidan tana safa da marwa. Ganin ta sheƙo da gudu sai ta kamata."Raihan, ina ummar ta ƙi daina kuka."
"Ta ce in kira ki tana waje Abba ya kore ta." Yarinyar ta furta tana share hawaye.
Kafin ta gama maganar ta ruga zuwa ƙofar gidan su. Da sauri ta ƙarasa tana faɗin,"Innalillahi wa inna ilahir raju'un?" Anya Faruk ma da hankali?" Kalli yanda ya koro ki babu mayafi, wannan dukan ɓarawo ya kama?"
"Ki taimaka mini akwai lulluɓi a jikinsa ya fisge Faruk Allah kawai zai saka mini." Ta ce cikin muryar kuka tana jin kamar ta nitse ganin yadda mutane suke wucewa suna kallonta, don ma unguwar ta su ba ta da yawan jama'a.
Kamata ta yi suka shiga cikin gidan ta. Tishu ta ɗauka tana goge mata gefen bakinta da ya fasa."Allah ya saka miki Nasreen, amma kin bar gidansa ko?"
"Ya sake ni saki ɗaya."
"Alhamdulillah! Allah mun gode maka, ba a son saki saboda in aka yi Al'arshin Ubangiji sai ta girgiza, amma duk wanda ya ji ya sake ki, dole ya yi miki murna, yau ki zuba ruwa a ƙasa ki sha, duk da saki ɗaya ne, zai iya mayar dake kuma kin san halin mahaifinki."
"Wallahi ko Baba zai yi ba zan dawo ba, na gwammace na shiga duniya akan na dawo gidansa."
"Yauwa ki jajirce sai ka yi jan ido kake samun yanci." Ta ce mata tare da miƙar da ita."Mu je ki yi wanka da ruwan zafi sai ki canza kaya." Ta ƙarashe maganar tana miƙar da ita.
Ba zan yi wanka ba, don Allah ki sa ya mashin ya kai Ni gida, so na ke Baba ya ga abin da ya yi mini, don ya zama hujjar da zan kafe a kanta."
"Kuma haka ne, amma da kin bar masa yaran, saboda kin san mahaifinki ba zai yarda ki zauna da su ba."
"Ya ce baya son su na tafi da su, kuma ina barsu ban san halin da za su kasance ba, baya ƙaunarsu duk abin da Rashida za ta yi musu ba zai kula ba."
"Kai Allah ka nuna wa Faruk iyakansa saboda shi da imani. Har yaran da ka haifa da cikinka ba babu tausayi a tsakani?"
"Ni dai na gode da ya furta mini saki, wallahi ko kashe ni zai yi, ba zan koma ba."
Ganin ba za ta iya zama kan mashin ba sai ta kira napep. Tun a cikin napep take kuka sosai.
Alokacin da ta shiga gidan, Baba yana cikin ɗakinsa kwance yana ta zabga hamma.
Tana shiga cikin gidan ta faɗa kan Mama da take durkushe tana wanke-wanke."Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Nasreen lafiya wa ya yi miki haka?"Ta ce tana share mata jinin da yake fitowa daga bakinta.
"Mama, Faruk ne ya yi mini duka kuma ya sake ni, saboda na ce masa zan je makaranta."
"Kai amma Faruk ba shi da imani dubi yadda ya yi miki, kamar ya kama ɓarawo?" Ta ce hawaye na zuba a ƙuncinta.
Jin abin da suke cewa, kuma an ambaci sakin sai ya fito da sauri yana faɗin,"Saki wace 'ya banzar ta ja aka sake ta?" Ya yi tambayar yana zare ido.
Ganinta ya sanya shi kallonta cikin cikin ɓacin rai."Yanzu Nasreen sai da kika yi abin da ya sake ki ko?"
"Haba Baban Maryam tambayar da za ka yi mata kenan, dubi yadda ya fasa mata jiki? Ko ɓarawo aka duka haka ai yakamata ka ga rashin imanin wanda ya yi dukan, ballantana matarsa uwar 'ya'yansa." Goggo ta faɗi haka tana kallon da cikin mamaki.
"Saki nawa ya yi miki?" Ya yi mata tambayar ba tare da ya amsa abin da ta ce ba.
"Saki ɗaya kenan? Alhamdulillah dole za ki koma.."
"Wallahi Baba, ko kashe ni za ka yi ba zan koma gidan Faruk ba, na gwammace na yi bara a titi da na koma gidansa. Ba ya soma kashe ni yake don yi." Ta ƙarashe maganar cikin kuka
"Kisha kurumin ki Nasreen, a wannan lokacin wallahi sai dai na rabu da mahaifinku, amma sai na tsaya na ga kin rabu da wannan matsiyacin. In har ya tilasta miki, Ni ma zan bar mishi gidansa."
"Ki sa da ni Maman Ahmad, wallahi in har ya kafe sai mu bar mata gidansa."
"Au haka ku ka ce?To sai dai ta mayar da yaran, tun da kun ɗaure mata gindi, amma wallahi ba za ta zauna da yarannan a gidan nan ba."
Don Allah ayi mini haƙuri daga yau zan rinƙa posting page ɗaya, sai bayan sallah na ci gaba da biyu.🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
*_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 7

Jin abin da ya ce sai hankalinta ya tashi matuƙa gaya. Da sauri ta rarrafa ta ƙarasa gurinsa ta dafa ƙafafunsa."Baba, don Allah ka yi hakuri ka bar ni na riƙe yarana, wallahi Faruk ba ya ƙaunar yarannan, kuma matarsa ba ta kirki ba za ta riƙe su ba."
"Oho sai ya kai su ƙauye ban damu ba ko gidan marayu zai kai su. Tun da ya sake ki na rantse ba zan bari 'ya'yansa su zauna mini a gida ba." Ya ce tare da kama hannun Raihan da take ɓoyewa a gurinta jin za a tafi da ita. Musaddik da ya ɗauka ya sanya kuka yana kiran Umma, ganin zai fita da shi.
"Umma, zan zauna dake don Allah kar ki kai ni gurin Abba." Ta ce tana miƙa mata hannunta.
Kuka take yi sosai tana kallon yaran da suke kuka. Hannu ta kai ganin zai fita dasu."Ka taimaka mini rayuwarsu za ta shiga garari. Don Allah ka bar mini su, zan tsaya na jure ruwa da rana na ciyar da su, sannan na inganta rayuwarsu."
"Ba zan bar su ba, in muka barsu ba zai yi dana sanin sakin ki ba. Tun da ɗan iska ne sai ya riƙe 'ya'yansa." Ya ce tare da fita.
Ganin duk haƙurin da suke ba shi, amma kamar tunzura shi su yi, sai suka kama hannunta."Nasreen ki bar kuka ki yi haƙuri Allah zai duba rayuwar su. Yara nawa uwa take fita ta barsu, kuma su rayu? Da baƙiciki a gidansa ya kashe ki gara ki haƙora ki zauna a gidanku, wallahi watarana za su ne ki duk inda kike"
"Mama, wahala za su sha Faruk ba ya ƙaunarsu."
"Allah yana tare da su ki yi haƙuri." Ta ce tare da kamata suka shiga ciki tana kuka sosai.
Tausayi yaranta take yi ta san cewar ba ƙaramin wahala za su fuskanta a gidan ba, watakila abin da za su ci ya gagare su, duk da cewar anan ɗin ma babu tabbacin samu, amma za ta nemo musu duk inda yake.