Sashe 53
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Gaskiya ko ana samu sai kaɗan yarinyar nan 'yar albarka ce. Shi ya sa duk na yi sallah nake mata addu'ar miji na gari, domin ta haka ne kawai za mu iya biyanta."
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 28

"In sha Allahu za ta samu tana da kyawawan halaye. Kuma aje aikin da kin yi shi ya fi. Yana da kyau ki yi nesa da shi kamar yadda ya buƙata. A yanzu na dawo cikin rayuwarku ba zan ƙara bari ku yi kuka ba. Tun kafin na dawo ni da ogana muka sanya aka yi mana ginin ƙaton gida an saka komai. Yanzu za ku tashi kayan jikin ku kawai za ku ɗauka mu koma gidan. Zan sanya Baba ya sake ki. Ni zan kula da rayuwarki, saboda Mama sam ba ki dace da rayuwarsa ba. Albarkacin haihuwata da ya yi da kuma sauran ƙannina waɗanda muke uba ɗaya zan gyara musu gidan nan, sannan na rinƙa basu abinci, amma ƙwandalata baba ba zai ci ba. Ko abincin da zai rinƙa ci saboda kannina ne. Baba ya cutar da rayuwarmu. Ya yi aure don biyan buƙatar sa ba, wai don ya haihu ya tarbiyar tar damu ranar gobe kiyama Annabi ya yi alhafari da shi ba. Irin wahalar da na sha, kafin na samu na gina rayuwata ya ƙara jefa mini tsanar shi."
Tsananin mamakin siyan gidan da ya faɗa musu ya sanya suka kasa magana, sai kallon sa suke yi cikin rashin hayyaci yana ta zuba. Ganin ashe ba saurarensa suke yi, ba sun shiga duniyar mamaki ya sanya shi kama hannayen su.
"Da gaske na siya mana gida mai kyau, da komai da komai ku tashi ku shirya mu koma."
"Ya Ahmad don Allah ka duke ni, ko zan farka da mafarkin da nake yi tun jiya."
"Ni ma ya haɗa da ni Nasreen." Mama ta ce cikin ruɗani.
"Da gaske ne na siya mana gida daga yau rayuwarmu ta canza."
"Ahmad wane sana'a ka yi ka tara kuɗi ka yi gini a wannan shekaru?" Mama ta ce tana kallon sa.
"Mu je sai a can gidan xan gaya muku."
"Ihun murna suka ɗauka wanda ya janyo hankalin mutanen gidan."
Gwaggo da ta ji abin da suke wa ihun ta ce,"Masha Allahu Allah ya ƙara buɗi."
"Amin, kuma zan sanya a gyara gidan nan kuma zan rinƙa ɗaukar ɗawainiyarku na kula da karatun ƙannina." Murna da koke-koke suke ta yi har na wani lokaci, kafin suka shirya suka gidan cikin farinciki suka tafi inda ya gina gidan
Cikin tsananin mamaki suka kalli juna. Mama da ta fito daga cikin mota ta tsaya tana kallon da ta ce,"Wai kana nufin Ahmad wannan gidan ka gina mana?" Ta karashe maganar tana shafa get ɗin gidan.
"Eh Mama, sannan har da nawa na gida duk a cikin unguwar nan. Ku shiga ciki nan ne za ki yi murna." Ya ƙarashe maganar tare da buɗe get ɗin gidan.
Cikin tsananin mamaki suka shiga gidan. Zuwa yanzu sun daina mamaki sai al'ajabi. Ji suke kamar a mafarki wai yau sune a ciki gidan nan mallakinsu wanda Ahmad ya siya musu. Kai lamarin Ubangiji sai kallo. Sosai suke murna kamar za su shiɗe. Ba su ƙara shiga cikin mamaki ba, sai da suka cikin falon. Sai suka tsaya suna kallon yadda fakon ya sha kujeru, manya da katon plasma ga kuma dinning.
Mama kuka ta saka da shi ta kama shi ta shaƙe."Ba zan kara farinciki ba, har sai ka gaya mini sana'ar da ka yi ka gina gidan nan. Wallahi Ahmad in har wani hanya mummunan ka ji ya sanya ka gudu ka je ka aikata don ka fitar damu cikin ƙangin talauci, ban yafe maka ba." Ta ƙarashe maganar tana jan mjina.
Nasreen ita ma kuka ta saka."Don Allah ka gaya mana yadda aka yi ka samu kuɗin nan."
Hankalinsa ya tashi ganin yadda suka rikice." To shikenan ku zauna zan gaya muku."
Kamasu ya yi ya riƙe ganin yadda suka tayar da hankalinsu."Wallahi Mama, ban taɓa kauce hanya don na samu abin duniya ba."
"To ka ba ni labarin yadda aka yi ka tara kuɗi."
"Shikenan, ku zauna zan ba ku labari, amma sai ogana yana nan, domin ku tabbatar da abin da zan faɗa muku. Ya ce mini yana kan hanya ku jira shi." Jin ya faɗi haka sauri suka zauna suna kallon sa.
Ba su jima ba sai ga shi ya shigo cikin gidan. Bayan sun gaisa ya zauna Ahmad ya gyara zama sannan ya gyara murya ya fara da ce wa," A lokacin da muka shiga mota za mu tafi, duk na ƙasa mu kai mu kammala aikin, saboda tunanin Baba zai iya tursasa Nasreen ta koma gida Faruk, tun da babu idanuna. Sai dai abin takaici da muka isa mun kira gayen da ya yi mana hanya, amma wayarsa a kashe. Hankalinmu ya tashi amma sai muka yi masa uzuri, duk da ya san da muka kan hanya. Shiga cikin tasha inda ake sayar da abinci muka yi, sannnan muka samu abin da za mu ci, tare da rama sallolin da yake kanmu.
Muna gurin har zuwa magariba muka ƙara gwada numbarsa. Cikin sama ta shiga ya yi mana alkawarin zuwa ya tafi da mu. Ba tare da ya ɗauki dogon lokaci ya iso muka tafi. Bayan ya kaimu inda za mu huta zuwa gobe ya nuna mana aikin. Da ƙyar na yi bacci duk na ƙasa mu fara aiki.
Abin takaici ko da ya zo muka tafi, ya nuna mana aikin, sai muka shiga cikin tsanannin tashin hankali, domin a yadda muka ƙiyasta kuɗin ko kuɗin motar da za mu koma ba zai biya mana ba. Hankalinmu ya tashi matuƙa gaya muka shiga masa fadan cewar ya san aikin ba shi da yawa zai kira mu? Kawai sai ya hau mu da zagi yana yare. Daga ƙarshe cewa ya yi ya fasa bamu aikin tun da mu Hausawa ba mu da mutunci. Ya yi tsaki ya tafiyarsa. Nan fa idanunmu suka raina fata, saboda duka kuɗin dake hannunmu bai wuce na cin abinci ba.
Na shiga tsananin tashin hankali da damuwa tuna dalilin da yasa a zo aiki, sannan ga bashin da na ci na kuɗin da bar muku abinci. Haka muka wuni cikin rashin dubara. Ogana ya bamu shawarar mu yi dako ko kuɗin mota mu tara sai mu koma gida. Akwai sauran kuɗin da ya bawa matarsa zai jiranta ta tura masa, duk mu haɗa.
Na rasa tunanin da zan yi, domin hanyar na kawai nake tunanin zan samu kuɗin da zan yi wa Faruk hulɗi. Na shiga damuwa da tunanin inda zan samu kuɗi, domin ina jin kunyar na dawo babu kuɗin, na san tijarar Baba da gorin da Faruk zai yi mana sun ishe ni. A raina sai na ji ina har ban samu wannan kuɗin ba, sam ba zan iya ƙara haɗa idanu dake da Mama ba, domin na gaza amatsayina na yayanki."
Muna cikin wannan halin dare ya yi haka muka kwana a waje. Washegari da safe muka zage dako, babu laifi kuma mun samu kuɗi.
Tun a ranar da muka je na ji babu aikin na kashe wayata, saboda bana son ku kira ni ku fahimci halin da na ke ciki. A ranar da muka fara dakon a gurin aka sace mini wayata.
Mun ɗauki tsawon sati muna duk aikin da muka samu sai muka haɗu da wani Tanimu, amma shi ɗan Kano ne ya zo neman kuɗi a can. Take muka fara hirar duniya har muka zama abokai. A nan ne yake sanar mana da cewar zai je inda ake haƙo ma'adai neman kuɗi. Da faru ban kula da labarin gurin dayake bani ba, amma da na ji yace mutum zai iya arziki acan in har ya dace ya haƙo zinare, rayuwar mutum za ta iya canzawa, amma fa gurin akwai tashin hankali, saboda mutum zai iya samu wani ya kashe shi ya kwace, sannan kuma ƙasa na yankewa ta kashe mutum, saboda rami ne zuƙuƙuƙu. Haka ya rinƙa gaya mini tashin hankalin da yake ciki, da kuma hasashen zama mai kuɗi lokaci ɗaya.
Sai na yi shiru, na shiga cikin damuwa ina tunanin halin da na ke ciki na gaba kura baya siyaki. Ba tare da dogon tunani ba xuciyarta ta aminta da na bi shi can. Saboda ku xan iya sayar da rayuwata, kula na gwammace na mutu, da na dawo babu kuɗin da zan yi wa Faruku hulɗi.
A lokacin na kallii ogana nuna masa sha'awar zuwa sai ya zare idanu yana kallonta."Ka da talauci ya sa ka je ka sayar da rayuwarka. Ka san wahalar da ake sha acan kuwa? Wallahi tsaf wahala za ta kashe ka. Mutane nawa suka je ba su yi arzikin ba, sai dai aka dawo da gawarsu."
"Zan je duk abin da Allah y yi daidai ne. In har na yi arziki zan yi farin ciki, in kuma na mutu hakan zai fi mini kwanciyar hankali da bakina gida ba tare da abin da na zo nema ba." Na faɗa masa xuciyata tana karfafa ni.
"To shikenan ni zan koma saboda ina da mata da yara ba xan kashe kaina ba." Ya ce tare da fara tafiya.