Sashe 66
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A falo ya fito don su karya yana ta zuba ƙamshi. Marwana da ta fito daga kicin da fulas a hannunta tana ƙoƙarin isa dinning sai ta tsaya cikin mamaki tana kallonsa.
Mommy ma da take zaune kallonsa take yi."Damir za ka ɗaurin aure ne daga gurin ofis?"
Tambayar da ta yi masa, ya sanya shi kallon jikinsa yana murmushi sai kuma ya kalle su ganin yadda suke kallonsa. Kunya sosai ta kama shi har sai da ya murmusa ya shafa kansa."No mommy I feel like to, shi ya sa na yi."
"Daddy you look so good and handsome."Little Marwana ta ce masa tana dariya.
Mommy ta ji daɗin dariyar da yake yi, har yana tsokanar Marwana da take ta cusa ƙwai a bakinta cewar ta cika ci. Sosai suka yi murnar ganin yadda ya saki. Ya karya ana hira ana raha sannan ya yi musu sallama ya fice.
Rigar Muhsin Marwana ta ja tana kallon sa."Kai ɗan'uwa zo mu yi gulma. Mai ya sa ya Damir yake farinciki kuma ya yi kwalliya haka? Sannan don Allah ka gaya mini dalilin da ya sanya shi fasa fita waje."
"Munafuka ba zan gaya miki ba, sai ki je ki tambaya shi." Ya ce mata tare da yi mata dundu.
"Wayyo Momi to shine har da dukana." Ta ce cikin muryar kuka tana shafa bayanta.
"Sabon kamu ya yi ƙanwar abokin sa..."
"Kan uba! Ai wallahi bai isa ya yi aure ba in ba Nasreen ba."Marwana ta furta lokacin guda fuskarta ta canza.
"To tun da ke kika haife shi sai ki sanya shi." Ya ce mata tare da zabga mata harara ya fara tafiya.
"Muhsin ba za ka gaya mini ba?"
"Mommy sauri na ke yi Ya Damir kin ji yana jira na." Ya ce tare da ficewa.
Marwana ta cika ta batse."Ai wallahi ki gaya masa ba zai auri kowa ba sai ita."
Kasa magana ta yi domin ita kanta ta fi son ya aure ta.
A mota suna tafiya suna hira sosai har da dariya. Sosai Muhsin ya ji daɗin yadda ya canza. Duk da cewar zuciyarsa tana bugu na tunanin yadda zai nuna mata soyayya, amma yarda da ya yi yana sonta, kuma zai gwada sa'arshi sai ya ji ya samu natsuwa.
Da suka isa cikin kampanin, idanunsa na kan inda take aje motarta. Sakin ajiyar zuciya yayi ganin har ta zo. Kalar motarta da numbobinta tuni ya riƙe su aka.
Ofis ɗinsa ya shiga ya zauna yana jin matsanancin frinciki. Bai jima da shigowa ba p.a ɗinsa ta shigo da files ta kawo mishi.
Gama jin bayanin ta ya yi sannan ya kulle ta yace,"Ki kawai Nasreen aikin sannan ki nuna mata, in ta gama kice ta kawo mini da kanta."
Da sauri ta kalle shi jin ya ambaci sunanta, saɓanin da sai dai ya ce yarinya. Ƙara kallon da ta yi, ganin yadda ya yi kyau da fara'ar da yake fuskarsa. Dama tun a ƙasa ta ji ana gulman wankan da yayi kamar mai zuwa zance. Ganin ya haɗe rai, yadda take kallon shi sai ta ɗauka da sauri ta fita.
Nasreen tana zaune a ofis tana cike takaddun ta shiga. Murmushi duk yi wa juna sannan suka gaisa."Oga Damir ya ce na kawo miki, sannan na nuna miki aikin da za ki yi, kuma in kin gama ki kai masa."
Cikin dakewa ba tare da ta firgita ba ta ce,"Ok, ina da aiki sai na gama."
Mamaki sosai ta yi jin abin da ta ce."Na je na gaya masa ne don ban san lokaci da yake so ba."
"You can tell him, tun jiya akan wannan aikin kin ga dole na gama kafin na sa?" Ta yi mata tambayar tana murmushin da ya ƙara bata mamaki.
"Ok, I will inform him." Ta ce tare da juyawa ta fita
Hankalinta kwance ta ci gaba da aikin, har tana mamakin kanta jin babu ɗigon tsoronshi a ranta.
A lokacin da ya shigo wayarsa, a ganinsa yana kallon lokaci yan tunanin lokaci da za ta ɗauka kafin ta gama, domin ya ƙosa ya ganta don idanunsa har wani ƙaikayin son ganinta suke yi.
"Ya dai?" Ya yi mata tambayar ganin ta shigo.
"Ta ce she has a lot of work, sai ta gama za ta yi naka."
Mamaki sosai ya kama shi, sai kuma ya ya ji sam bai ji haushin abin da ta ce ba. Mamakin maganar ya yi har yaushe ta daina jin tsoronsa, amma da ya tuna tun da ta dawo yadda take masa wani gani-gani, sai ya daina mamakin."
"Ok, you can go." Ya ce mata fuskarsa ɗauke da murmushin da ba ya son ta gani.
Cikin mamaki ta fita tana tunanin canjin da ya yi.
Hankalinta kwance ta ke aikin ta har ta gama. Ko da ta gama zama ta yi, tana huwatawa har lokacin tashi ya yi.
Wayyo Damir an ije girman kai da izza za a fara nuna wa Nasreen soyayya. Na matsu na ga wannan soyayya. Ko zai iya ko kuma girma kai zai hana shi?
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 35
Hankalinta kwance ta ke aikin ta har ta gama. Ko da ta gama zama ta yi tana hutawa har lokacin tashi ya yi. Ta kwashi tarkacenta za ta fice. Tana ƙoƙarin sauka ƙasa suka haɗe da P.A ɗinsa.
Turus tayi sai kuma ta shafa kai."Na manta na sanar miki ban gama ba, saboda aikin da na ke yi ya riƙe ni. Ki gaya masa gobe xan yi." Ta ƙarashe maganar, tana sauka ba tare da ta tsaya ta ji abin da za ta ce mata ba.
Kallonta ta yi, yadda ta daina tsoronsa su kuma ta juya zuwa ofis ɗinsa."Sir, ta ce aiki ya riƙe ta gobe za ta yi."
Da sauri ya juyo yana kallonta jin abin da ta ce. "Ok go." Abin da ya iya cewa kenan sai ya zauna yana mamakinta. Damuwa ce ta kama shi, domin tun safe yake son ganinta. Ko da ya ce gurin lunch kamar a ofis ta yi nata.
Da sauri ya kwashi tarkacensa ya fice don ya ganta, amma yana zuwa motarta na ficewa. Ji ya yi jikinsa ya yi sanyi sosai. Wani irin sonta ya ƙara mamaye shi. Cikin kasala ya shiga cikin motarsa ya tafi.
Nasreen tun ranar da Faruk ya zo, ta shiga damuwa saboda tana tsoron kar ya ɗauke yaranta. A dalilin wannan tunanin ta shawarci Ahmad ta canza musu makaranta, amma sai ya hanata ya ƙarfafa ta da cewar ba zai aikata ba tun da ba shi da wacce za ta riƙe masa. Abin da ya ce mata ya ɗan kwantar da hankalinta tamkar ta yi baƙo ya mutu.
Washegari da safe, ta yi wanka sannan ta sha kwalliya cikin shiga ta alfarma ta wuce ofis. Tana shiga jakarta ta ake kan tebur ta kama aikinsa. Zuwa ƙarfe sha biyu ta gama yunwa take ji sosai, saboda bata karya ba ta taho, domin da safe ta ji ba ta son cin komai, saboda da dadddare cikinta ya so ya ɓace.
Sai data gama aikin sannan ta ɗauka ta nufi ofishinsa. Ba ta ji tsoro ko faɗuwar gaba ba, har sai da ta kama murfin ƙofar za ta murɗa, sai kawai ta ji gabanta ya faɗi yana kuma harbawa da sauri.
Da sauri ta saki ƙofar tana ƙaranto addu'a, sannan ta samu ƙarin gwiyar shiga. Yana zaune da waya a gabansa. Aiki yake yi amma duk bayan minti sai ya kalli wayar, tare da tunanin wani lokaci za ta yi aikin ta kawo. Ganin har sha biyu ta yi dai ya fara tunanin, ko ta yi masa rainin da zai ba ta aiki ta ƙi yi. Zuciyarsa ta sare a lokacin da ya kuma ƙara tunanin ko ba ta son ganinsa ne. Yana ƙoƙarin ɗaukar waya ya kira p.a ɗinsa ya ji an murɗa ƙofar. Idanun ya zura a ransa yana addu'ar ita ce. Cikin sama addu'arsa, ta karɓu ganin ta shigo da siririyar sallama a bakinta.
Ɗago idanunsa ya yi, yana kallon ta yayin da ya ji matsanancin faɗuwar gaba. Yayin da yake kallonta, amma tun da ta kalle shi sau ɗaya ba takara ba domin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri kuma bisa rashin ƙa'ida.
Ƙarasawa ta yi, har gaban teburinsa cikin yanayi na ta ƙura ganin yadda ya zuba mata idanunsa kamar zai haɗiyeta.
"Ina kwana?" Ta yi masa tambayar tare da ije aikin a gabansa.
Files ɗin ya kalla, sannan ya ɗora shanyayyun idanunsa a kanta yana ƙoƙarin saita natsuwarsa ya amsa gaisuwar. "Lafiya lau." Iya abin da ya yi nasarar furta wa kenan, saboda yadda harshen da suke harɗewa, tamkar wanda yaron da yake koyon magana kuma ya nace sai ya yi.
Da sauri a ɗago ta kalle shi, jin karo na farko ya amsa maganarta cikin sanyi. Saurin mayar da idanunta tayi, yadda ya kashe ta da mayun idanunsa.Ganin ya yi shiru sai ta juya za ta tafi da ƙyar ya saita ɗan natsuwarsa ya ce,"Nasreeeeen." Ya ja sunan tare da yi masa gunna yana kallonta.
Tsayawa ta yi cak! Zuciyarta na bugu domin yadda ya kira sunan ta ji shi har cikin zuciyarta. Kasa juyowa ta yi har na 'yan daƙiƙa, sannan ta yi nasarar sakin murfin ƙofar da ta kama za ta fito ta juyo tare satan kallonsa.
Zuciyarsu ta buga a tare karan farko da ya ji yana son ya ji ta a jikinsa, domin wani irin shaukin ta da madarar ƙaunarta ya ƙara kama shi, saboda kallon da ta watsa masa, wanda ya sanya ya ji ta tamkar ya je gareta.