Sashe 78
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 41
Kallonsa suka yi sai ta yi murmushi."Gida mana Damir. Ai ba kaza bace kawai da za a kamata a kaita gidanka, dole za a yi bikin, kuma an ɗaura iyayenta ba su sani ba, don haka dole gida za ta koma, kai ma kana buƙatar lokaci a gidanka za ka zauna, kuma tun da Batula ta mutu ka kauracewa gidan dole a gyara."
"Mommy sai ta zauna a ɗakina, in ma gidan ne, a yau zan iya oder na komai gobe a gyara." Dariya suka yi ganin rashin kunyarsa.
"No ka yi haƙuri so nake a yi biki sosai, sannan Marwana kamar ta samu wanda take so. In ya so sai a sanya bikin da nata a sanya wata ɗaya kawai, sai ki gaya masa ya turo."
Ɓata fuska ya yi yana kallon ta, domin yana jin ba zai iya wanna kunyar ya barta a gida har wata ɗaya ba tana matsayi matarsa.
"Mommy don Allah ina bukatar matata, na haƙura da duk wani shagalin da za a yi. Mu ai ba yara bane."
"Ka yi haƙuri kawai Damir dole ayi biki." Mommy ta ce masa tana mamakin zaƙewarsa.
Tura baki ya yi, kamar ƙaramin yaro ba tare da ya ce komai ba.
"Mommy wanda na samu Ya Ahmad ne Yayan Nasreen, kuma ya ce dama na gaya muku a yi maganar bikinmu. Dama ina jiran na ga Ya Damir da Nasreen sun haɗa kansu sai na gaya muku."
"Alhamdulillah Masha Allah! "Suka furta lokaci guda.
"Ka ga wani haɗin Allah! An zama jini ɗaya?" Mommy ta yi maganar cikin zallar mamaki.
Da sauri Ahmad ya ƙara tafiyarsa ya isa mota cikin jin kunya.
"Ahmad dawo da Nasreen ta yi jinyar mijinta. Kai kuma ka dawo na yi magada kai." Alhaji Sani ya ce.
Ji ya yi kamar zai gudu saboda kunya. Tsayawa ya yi yana sosai kansa.
"Nasreen je ki zan yi wa Mama bayani." Ya ce tare da shigewa cikin motar da yaran cikin jin kunya.
Dariya suka yi sosai Alhaji Sani ya ce,"Aiko kin samu miji mai kunya don har ya fiki."
Fuskarta Marwana ta rufe tana murmushi.
"Lamari ya yi kyau ga shi shi ma nagartaccen namiji. Kawai ya kawo kun sa rana, sai a sanya bikin wata ɗaya da kuma tarewar."
"Allah ya kaimu ya sa an ƙulla aikhairi." Ta furta cikin farin ciki.
Nasreen sao sunne kanta take yi, ganin yadda yake ta kallonta. Da sun haɗa idanu sai ya yi murmushi. Ji yake kamar ya haɗata da jikinsa, so yake ya rungumeta ya yi kissing ɗin ta, don tabbatar da cewar da gaske matarsa ce ta zama gonar sa.
Mota suka shiga sanan suka wuce asibitin, saboda hutun da yake buƙata. Nasreen aka bari sai Marwana da ta je ta kawo musu abinci. Kan dole ya kwanta ya rintse idanunsa, don dole kawai, domin hatta Nasreen waje aka koreta sai ya yi bacci na awa biyu, amma fa tun da ya shiga cikin ɗakin ya kasa bacci. Tana zaune tana karatun Alkur'ani, don ta samu natsuwa. Har yanzu ta kasa yarda cewar matar Damir ce ita.
Ganin kiransa sai ta zare ido."Ya Damir bacci ka ce ka yi."
"Please matata, ki shigo na yi abin da zai tabbatar da kin zama mallakina, har yanzu gani na ke kamar mafarki na ke yi."
Dariya ta yi tare da rintse idanunta."Da gaske na zama mallakinka ina jiran ka yi bacci in ka tashi sai na zo na yi wa kyakyawar fuskarka kiss ka tabbatar da haka."
Da sauri ya miƙe, ya tashi zaune yana mamakin da ma ta iya kalaman.
Komawa ya yi ya kwanta, yana sakin tsaddaden murmushi kamar tana gabansa. A hankali ya furta,"Please peck or deep?"
Kunya sosai ta ji, jin tambayar da ya yi mata, domin da agabansa ya yi tambayar ji za ta yi kamar za ta nitse. Ɗaurewa ta yi ta ce,"Your choice. Cikin sanyin murya ta furta.
Jin abin da ta ce sai ya shafa kansa cikin murmushi ya ce,"Oh my God!" Da wata irin murya ma kashe jiki
"Ashe ta iya kalamai? Kodayake she is educated, duk wannan kunyar zai tafi in har muka tare." Ya ce yana ayyana soyayyar da za su yi.
"Promise?" Ya tambayarta bayan ya ɗauki lokaci yana tunani.
"Yes promise if you sleep."
"Ok baby right now sleep bye." Ya furta tare da kashe wayar.
Ita ma murmushi ta yi, ta rungume wayar cikin tsananin frinciki.
Ga mamakinsa sai kawai ya rintse idanunsa, ya fara bacci sosai mai ƙarfi ya ɗauke shi.
Dariya ta yi ta cigaba da karatun.
Ahmad ciki farinciki ya ƙarasa gida. Mama da take cikin damuwa ta kira shi ya fi sau nawa. Na ƙarshe ya lura da kiran ya amsa yana faɗin,"Mama gani zan shigo da mota."
"To alhamdulillah." Ta ce tana kallon Baba da yake ta bata baki.
Yana shigowa suka yi kansa."Ya aka ƙare?" Suka haɗa baki gurin faɗin haka.
Kwashe abin da ya faru ya yi ya gaya musu. Sun cika da mamaki sosai."Yanxu da gaske an ɗaura auren?" Baba ya tambaya cikin mamaki.
"An ɗaura tana asibiti jinyarsa, saboda Faruk ya ji masa ciwo sosai kuma ya zubar da jini."
"Amma kana ganin ka ba ni haƙƙina na mahaifinta Ahmad? Tun da ka yi kuɗi ka mayar da ni bolar zuba shara? Duk abin da za kayi ba za ka shawarce ni ba, idan ba ni da matsayin da za a nemi shawarar sai a gaya mini ko ta waya ne, tun da yanzu ka zama uban gidan haihuwar maka yaran kawai na yi."
Mamakin abin da ya ce ya kama su sosai. Ahmad saboda takaici ya rasa abin da zai gaya masa, sai ya zauna yana tunanin abin da zai faɗa ya baƙanta masa.
Mama cikin zafi ta taso mishi tana faɗin,"Akan wane dalili zai nemi shawararka? Bayan haihuwar yaran ka yi ka bar mishi wahala? Ko don an ƙyale ka, an zuba maka idanu ka haifa ka bar mishi su, yana musu ɗawainiya shi ne za ka samu bakin magana?"
"Haƙƙina ne Nasreen ni na haife ta."
"Ba a kan haƙƙinka kake magana ba, abin da za ka samu kake jin takaicin ba a kira ba, saboda yaran kamar jari kake yi da su. In kana wannan maganar cewa haƙƙin ka, ya kamata ka yi magana haƙƙinka da ya kwashi yaran ya sanya su a makaranta, amma babu abin da ka ce sai wannan ka san da haƙƙinka?"
"Eh mana Ahmad duk mai ya yi wa 'yan'uwansa, ya zamar mishi dole a matsayinsa na babba, sannan in da ya shawarce ni zan yarda ya sanya sadaki naira dubu talatin kamar ya siyar da kaza? Ai darajarta ya wuce haka. Kamata ya yi, a sanya musu miliyan ko rani tun da suna da kuɗi."
"Darajar auren muke nema Allah ya albarkanci aurensu, kai da ka sanya wa zuciyarka son abin duniya sai ka je ka yi ta yi. Har yanzu za ka yi nadama ba Baban Ahmad? Ina ƙara jaddada maka rabuwarmu, domin zama da kai ba yi da amfani."
"Auren zobe mu ka yi, in har kika mun rabu na mutu ne, amma wallahi sai dai ki yi abin da za ki yi ba zan sake ki ba."
Dole ka sake ni bari a gama bikin Nasreen."
Shiru ya yi, ya zauna ganin yadda take gasa masa magana. Har sai da ya yi dana sanin maganar da ya yi.
Tun da suke sa'insar Ahmad bai tanka musu ba, sai da suka yi shiru sannan ya kalle shi cikin takaici ya ce,"Mama ki sha kurumunki ana gama bikin Nasreen zan kai shi kotu. Sam ba zai shiryu ba, don haka dole ku rabu da shi, tun kafin ya kuma je ya ƙara zubar mata da mutunci yana roƙon su kuɗi, tun da ga shi nan ya raina sadakin da aka abayar."
"Allah ya ba shi sa'a, wallahi in har ya aikata haka sai ya yi dana sani, domin sai na yi mishi abin da bai taɓa tunani ba. Tozarci da rashin ƙima da ya ja mata a gurin Faruk ya isa. Wannan karon in har ya aikata ba daidai ba, na rantse a ranar sai ya ba ni takaddar saki."
Ganin yadda ta harzuƙa, sai ya kalle ta cikin sanyi ya ce,"Ba zan aikata hakan ba saboda Nasreen tana bani duk abin da na roƙa. Don Allah ki daina gaya mini za mu ramu."
"Dole na gaya maka, saboda ba ka cancanci rayuwa da ni ba." Ta furta masa tana watsa masa mugun kallo.
Shiru ya yi, don ta bar maganar kuma cikin sa'a sai ta yi shiru. Nisa wa ya yi ya kalle ta ya ce,
"Amma Faruk ɗan tasha ne mara hankali kawai. Ai shi da Nasreen yarda ya bar nonon uwarshi ya barta. Allah ya bata wanda ya fishi. Ni kaina na yi dana sanin aura masa ita da na yi. Kalƙo mai kafar biri."
Banza suka yi da shi sai Mama ta nisa ta ce,"To shikenan Allah mun gode maka tun da abun ya zo da sauƙi. Shi kuma ya ga ƙarshen sa. Sai abin da ya faru ya zama izna ga WASU MAZAN da suke wulaƙanta mace, suna ganin zaman gindansu cikin ukuba shi ne kawai mafita."
"Amin Mama, da kuma WASU MAZAN da suke haihuwar yara ba tare da sun kula da rayuwarsu ba, su barshi kara zube su zama annoba a cikin al'umma, bayan sun san ranar gobe kiyama, Allah sai ya tambaye su amanar da ya ba su."
Mama ce kawai ta ce,"Amin," Baba kuwa sai ya muskuta, ba tare da ya ce komai ba, domin ya san magana ya gwaɓa masa.
Ganin Ahmad ya shige ciki, sai ta miƙe ta shige ɗakinta, aka bar shi yana ta kallo.