Sashe 46
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zare idanunsa ya yi kamar zarrare. "Ina wayana kuɗin da yake account ɗina wayyo miliyoyina." Ya ce tare da zunduma ihu.
Murmushin takaici ta yi masa tare da miƙa masa wayar. "Tun da aka kawota asibiti ake ta cire maka kuɗi, a lokacin da Usman ya ɗauko ka, muka yi ƙoƙarin kulle account ɗin, amma ta zare komai naira dubu goma ta bar...."
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Na shiga uku wayyo kuɗina. Na rantse ba zan yarda ba, saboda ko lahira ta je sai na bita." Ya faɗa yana surutu kamar mahaukaci.
"Sai ka shirya ka je inda ka jajibo ta, in ka yi sa'a tana nan to." Cewar Anty Asiya.
Ihu sosai yake yi yana surutai daga ƙarshe miƙewa ya yi."Zan je inda take ba zan iya haƙuri na warke ba."
"Mu je na raka ka."
"Usman ya goya shi a motarsa har gidansu, amma babu kowa sai sauran masu haya gidan."
Wani bayerabe ya kalli Faruk da yake shirin hauka ya ce,"Reshiidaaa ba ta nan tun da ta yi aure bata ƙara...."
"Na shiga uku na lalace. Usman zan mutu wallahi account ɗina miliyoyin ne a ciki. Har da kuɗin da na karɓa na Alhaji Adamu kan maganar gidan da ya ɗora ni a kai. Usman hauka zan yi in har ta sace kuɗaɗen nan! Gara na mutu kan ta sace kuɗaɗen da na ki ci na ki kula da iyalina na tara su." Ya furta cikin razana yana zambarwa.
"Ya za ka yi da jarrabawa? Yakamata mu je inda aka ɗaura muku aure."
"Ta gaya mini babanta ba ta son shi, mahaifiyarta ta mutu. Wani ta samu ya ɗaura mana aure."
"Wannan dalilin ya sa ya ake son mutum ya auri mai asali, shikenan ka kai kaka baro."
"Wallahi kuwa, saboda gara na mutu da ace na rasa wannan kuɗin, domin ba zan iya daukar ƙaddararsu ba."
"To kashe kanka za ka yi?" Ya yi masa tambayar cikin jin haushin abin da ya ce.
"Ina ga hakan ne mafita mutuwa kawai yafi a gareni." Ya ce tare da zabura ya yi titi yana ihu. Ganin da gaske yake yi ya kwala ihu taimaka mishi suka sanya shi a mota.
Da ƙyar suka koma gida Anty Asiya na ganinsu hankalinta ya tashi. " Da gaske ta gudu da kuɗin ko?"
"Ba ta domin babu labarinta."
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un!Faruk ka jawa kanka asara. Kana zaman ka da matarka mai kirki, ka je ka auro yare ga shi nan ka jawa kanka."
"Anty Asiya ki taimake ni mutuwa zan yi babu kuɗin Faruk babu Faruk." Haka yake ta faɗi yana sumbatu marasa kan gado.
Hauka tuburan ya fara domin yana ganin ya yi rayuwa a haukan yafi masa da zama babu kuɗi. Sosai ya zama mahaukaci domin babu maganar da yake yi dai ihu yana faɗin,"Babu kuɗi babu Faruk."
Ganin ya zauce suka tattara suka kai shi asibitin mahaukata, saboda ko acan sai da aka sanya masa ankwa. Ihu yake yi yana kiran sunanta tare da kunduma mata ashar.
Nasreen
kamar yadda Marwana ta ce za ta zo ta shirya ta zo. Nasreen na zaune a falo ta yi sallama ta shigo. Cikin farinciki ta kamo hannunta suka zauna.
Suna ta hira har wani lokaci sannan aka kira sallar azahar suka ta shi duk yi. Bayan sun idar Mama ta gama dambu ta kawo musu. Sosai take cin dambu tana santi har ta gama.
Nasreen da take zabar musu material, da za su siya su ɗinka ta kalli Marwana da hankalinta yakan wayarta ta ce,"Kin ga wannan yadin yana da kyau?"
Karɓar wayar ta yi tana kallo."Yana da kyau in har ya yi miki ai ya mini, amma mu canza colour ɗin."
"Ok, bari ki ga wannan." Ta ce tare da karɓa ta nuna mata.
Wayar ya ƙara karɓa tana kallo."Yauwa ya yi sosai kuwa." Ta ce tana ci gaba da kallon yadin.
Wayar da ke hannunta na Nasreen ta fara ƙara alamun ana kira. Miƙa mata wayar ta yi tana faɗin,"Ana kiran ki."
Da sauri ta karɓa, ganin Ingawa ne sai ta ije ba da ta ɗauka ba. Bayan kiran ya katse ya ƙara shigowa.
Marwana da ta bita idanu ta yi, ganin yadda ta tsargu dai ta ce,"Ki ɗauka mana ba kiran ki ake yi ba?"
"Eh zan kira ɗaga baya." Ta furta hakan cikin tsarguwa.
"Ok, na manta a yi mantuwa tsaƙon Raihann da Little Marwana ta ba ta bari na ɗauko."
"To,"Ta ce mata daidai lokacin da aka ƙara kiran
Da ta fita sai ta tsaya a hanya ta kuma dawo. So take ta gane soyayya take yi. Ganin ta fita kai hannu ta amsa kiran."Yayana."Ta furta cikin sanyin murya.
Jin alamun shigowar yasa ya ta ce,"Zan kira ka." Ta kashe da sauri ganin ta shigo.
"Nasreen har akwai abin da za ki ɓoye mini, ko kina waya da Faruk..."
"Ban yi tunanin za ki zarge ni da aikata hakan ba."
"Abin ne da mamaki, ganin kin kasa ɗaukar wayar a gabana, wannan dalilin ya sanya na fita, don na tabbbatar da haka, saboda bana tunanin za ki iya ɓoye mini abu."
Ganin yadda ta harzuƙa, sai ta kamata suka zauna."Yi haƙuri kunyar amsawa na ke yi a gaban ki, saboda nasan za ki yi mamakin, har na manta wahalar dana sha a gidan Faruk na faɗa soyayya."
"Soyayya kike yi?" Ta zare idanunta tana tambayarta.
"Shi ne dai yake sona Ingawa ne a gurin aki, amma na gaya masa ya yi haƙuri don ba zan ƙara aure ba, sai ya roƙe ni kan na amince mu zama ya da ƙanwa, saboda mutuncinsa ya sa na amince."
Hankalinta ne ya tashi sosai, har sai da Nasreen ta yi mamaki.
"Za ki yi aure amma ba shi ba, saboda akwai wanda na ke son ki aura, kuma ba ke ganin akwai alkhairi a auren."
Kallo ta yi cikin rashin fahimta."
"So na ke ki auri Ya Damir..."
"Amma ba ki da hankali ko? Kin san yada ya tsane ni kuwa. Kin san abin da ya yi mini yau? Ki cire wannan mentality a ranki, saboda babu ta yadda za a yi hakan ya faru."
"Babu abin da ba zai iya faru ba, in har Allah ya ƙaddara. Addu'a na ke yi kuma Allah ya ga nufinka. Ya Damir yana cikin damuwa muna buƙatar ya dawo da rayuwarsa ya samu mata.
"Please Marwana stop hallucinating, it will never happen. Ya Damir ya tsane ni, babu wacce ya tsana kamar ni. Gaskiya ba ni da courage da har zan iya tunkararsa na sanya soyayyata a zuciyarsa, kin san yadda na ke matuƙar tsoronsa? Na rantse miki a gurin aiki ko sunan shi aka faɗa sai gabana ya faɗi.
"Gwada za ki yi in sha Allahu za mu dace."
"Hummmm!" Kawai ta ce mata, saboda maganar ta gundureta.
Jakarta ta ɗauka ganin yadda ta yi shiru."Ni zan wuce, amma ki yi tunanin abin da na gaya miki."
Ba tare da ta ce mata komai ba ta miƙe don ta raka ta. Har suka isa motar ta kasa magana, sai da taga za ta tayar da motar." Ki gaida Mommy."
"Za ta ji ina son ki je ki gaishe ta, saboda sai ƙorafin sai dai na je gidanku, amma ba kyau zuwa namu."
Gabanta ya faɗi don har yanzu tana jin nauyin Momi."Zan zo watarana."
"To shikenan, sai mun yi waya."
"Allah ya tsare hanya." Ta ce tare da juyawa ta shiga gida, bayan ta tayar da motar ta fara tafiya.
Da ta koma gida ita abin dariya ma ya bata. Gani take shirme irin na auta ya sanya Marwana ta yi wannan tunanin. Ta kwana tana tunanin ya za ayi har Damir ya sota?
Saboda tuna dokar da aka sanya a gurin aiki, tun asuba ta yi wanka ta shirya Raihann. Ƙarfe shidda ba ta yi ba ta fice daga gidan.
A lokacin da ta je wasu daga cikin ma'aitan da yawa sun iso. Saboda rashin mutunci bai zo ba har sai da goma ta yi. Ya shigo cikin taƙun taƙama ya wuce ofis ɗinsa. Burinsa ace ba ta yi aikin ba ya mata tijara, saboda jiya da tunani abin da ta yi masa ya kwana. Da ya buɗe idanunsa sai ya ga Ingawa a cikin ofis ɗinta.
Da ya shiga kai tsaye gurin files da ya iske masa ya duba. Ganin ta yi aikin da kyau sai ransa ya ɓace, amma duk da haka ya ɗauki alwashin sai ya tozartata.
P.A ɗin da ya tura ta je ta kira ta, amma sai kuma ya fito don ya je da kansa. Nasreen tun da ta ganta gabanta ya yi mummunar fadi. Jin yana kiranta hankalinta ya tashi, har hawaye suka taru a idanunta.
Cikin sanyin jiki ta miƙe xuciyarta na bugu. Da sauri ta ja ta tsaya ganin sa yana sakkowa zuwa ofishinta.
Neman inda za ta ɓoye ta fara, saboda yadda ya taho tamkar fusataccen zaki. Ta san wulakanci ya shirya mata, amma ba ta ga inda za ta ɓoye ba, domin ya riga ya ganta.
Tsayawa ta yi tana kallon sa har ya ƙaraso. Files ɗin ya watsa mata a fuska."Saboda ba ki da hankali, da ki yi mini abin da ba sanya ki ba? An gaya miki kuɗin banza na ke samu da zan ɗauki wacce ba ta iya aiki ba? Ko ki gyara ko kuma na sallame ki."
Yadda yake maganar ya ɗauki hankalin wasu daga cikin ma'aitan. Har ma waɗanda suke ciki sai dai suka leƙo. Takaddun suka zube daidai da gangarowar hawayenta.
Ta rintse idanunta tana jin tashin hankali da kunya. Ɗago idanunta ta yi tana kallon sa, ganin yadda ya cika ya batse.
"Ma za ki gyara in ba haka ba sai na kore ki." Ya ce tare da wucewa yana takun taƙama.
Duƙawa ta yi, ta fara kwashe takaddun hawaye yana bin kuncinta. Ji take yi za ta ake aikin saboda baza ta ɗauki wulanƙanci ba. Takaici da haushin tunanin da Marwana take yi ya kamata.
Hajar da ta fito za ta kai masa aikin da ta gama, ganin abin da ya faru sai ta tsaya tana kallon sa.
Da sauri ta ta ƙarasa ganin ya wuce."Am sorry Nasreen, gaskiya Yaya bai kyauta ba."