Sashe 5
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Allah ya kyauta Faruk ya yi mini tozarta."
"Ba ya nan."
"Kawai tafiya zan yi ba sai kin bani kudi ba, ke da kike buƙatar taimako Allah dai ya bayyana ya Ahmad."
"Amin," Ta ce sai hawaye suka zubo mata.
"Ya zamu yi? Sai haƙuri dana haka rayuwar take sai a yi ta ɗauke na gari. Da ace ana shawara wallahi Baba zan ce a ɗauke, saboda ba shi da amfani."
"Kar ka yi masa fatan hakan, duk lalacewarsa mahaifinmu ne, mu yi masa fatan ya shiryu ba."
"An gaya miki yana nadama ne? Har yau babu nadamar da ya fara."
"Allah ya shirya shi."
"Amin," Ya ce tare da yi mata sallama ya wuce.
Ɗaki ta koma ta fara danna wayar. Data ta siya ta shiga play store ta ɗauki facebook lite da gb Whatsapp. Bayan ta yi installing ɗin su, sannan ta buɗe. Da ta gama duba facebook ta shiga groups da take so, sai ta sauka a ta koma Whatsapp da tsaƙwanni suke ta shigowa daga group na su na makaranta. Maman Muwaddat ta yi wa sallama ta gaya mata ta canza wayar. Ganin ba ta a online sai ta fara duba tsaƙonnin da suke shigowa.
Bayan ta gama duba tsaƙon dai ta bi shawarar da zuciyarta take ba ta. Numbar Marwana ta ɗauki ta kwafe tare da saving a wayarta. Ta yi hakanne don ta rinƙa ganin status ɗinta, ta santa mayyar sanya status ne. Yawanci hotonta Damir sai na matarsa da kuma Little Marka da ƴaƴanta. Bayan ta sanya babu yadda za a yi mutun ya san ta kalli status ɗin mutum, sannan ta kashe wayar ta kwanta tana tunanin rayuwa.
Tana son ta san halin da suke ciki. Tana son ta san ko yanzu suna farinciki. Addu'a take musu kullum Allah ya dawo musu da farincikinsu.
Da ta yi isha'i ta yi gama abin da za ta yi ta kwanta. Wayar ta janyo ta kunna data. Ta daɗe a facebook wani zubin ta ga labarin dariya, wani zubin takaici har ta gaji ta sauka ta koma Whatsapp.
Tana duba status sai ta ga Marwana ta ɗora status. Da sauri ta fara dubawa jikinta har yana kyarma. Hoton farko ita da Little Marwana, sai kuma ta sanya hoton Marigayiya Batula da stickers na kuka da addu'a da ta rubuta da turanci. Ganin hoton ya sanya hawaye zuba daga ƙuncinta.
"Allah ya jiƙanki Batula ya sanya kina kyakkyawar matsayi." Ta ce tare da ƙara duba status na gaba.
Wani irin faɗuwar gaba ya same ta har sai da ta miƙe. Ganin hoton Damir Gabakiɗaya ya canza kamar ba shi ba. Duk da cewar ba sau biyu ta ganshi, amma fuskarsa da ya zauna a idanunta kamar an zama shi yana nan. Har yau tana tuna fuskar da take saukar da annuri, amma yanzu sai ta ga saɓanin haka. Ya ɗan yi duhu ga wata ƙasuma da ya tara. Yana sanye da jallabiya fara tar farin har yana kashe idanu. Inda aka ɗauki hoton zai tabbatar maka da ƙasa mai tsarki suka je. Wataƙila ummra suka je don Alllah ya kawo masa ɗauki. Ta ayyana hakan a ranta tana kallon hoton zuciyarta na bugawa. Hoton Gaba ta kalla duka family ɗinne suka ɗauka. Sai ta rintse idanunta tana jin ƙaunar waɗannan ahalin, duk da cewar sun tsaneta tana son su, kuma za ta ji gaba da musu addu'a. Kallon Marwana take yi cikin tsanannin ƙauna, tana share hawaye da ke gangarowa a fuskarta. Ta san cewa ba ta yi wa waɗannan ahalin adalci ba, kamar yadda rayuwa ba ta amarya adalci take raba ta da mutanen da suke ƙaunarta.
A ranar kasa bacci ta yi tana ta juye-juye tamkar wata maciya. Ganin bacci ya ƙauracewa idanunta, sai ta tashi ta yi alwala. Addu'a sosai ta yi goshinta na ƙasa. Tasha kuka tana kaiwa sarki ɗaya wanda ba shi da abokin tarayya a gurin bauta, da ya bayyana musu Ahmad in yana raye, sannan ta yi sallar istikhara kan sana'ar da za ta fara. Kwanciya ta yi kan daddumar bacci mai ƙarfi ya kwashe ta.
Saboda ruwan da aka yi cikin dare, sai bacci ya yi mata daɗi. Ba ta tashi ba sai kusan bakwai don ta makara. Da sauri ta yi alwala ta yi sallah sannan ta tashi Nasreen. Kicin ta nufa don ta ga abin da za a girka, sai ta ga ya ije musu taliya leda ɗaya da kayan miya. Ba ta ji wani abu ba, domin idan da sabo ta saba, za ta iya cewa yanzu ta samu ci gaba, tun da albarkacin auren da ya yi ba ya bari sai ya dawo ta yi girki.
Komawa ɗaki ta yi, ta ɗauki kudi don ta siya wa Raihan indomie ta dafa mata, domin kafin ta gama lokaci ya ƙure. Duk da saurin da ta yi, hakan bai hana yin lattin ba. Tana tsaye a falo tana gyara ma Raihan zaman hijabinta ya fito. Da alamu fita zai yi.
"Ina kwana?" Ta ce masa ba tare da ta kalli inda yake ba. Shi ma bai kalle ta ba, ballantana ya kalli 'yarsa ya sa ya kai ya fice. Sai ta miƙe tana kallonsa tare da mamakinsa. Inda ace uban ƙwarai ne yadda Raihan ta yi lattin. Jikinsa na rawa zai kaita. Ba za ta ce masa bai san darajar karatun ba, tun da da karatun yake cin abinci, yaran ne kawai ba ya so.
Bayan ta kai Raihan ta dawo kasancewar ya fita, sai kawai ta faɗa gyaran gidan sai da ta gama ta ɗora girkin. Tana zuba taliyar Rashida ta fito.
Ganin abin da take yi sai ta ƙarasa gurinta cikin ɓacin rai. Yunwa take ji sosai, saboda dankalin da aka yi ba ta ci sosai ba. Amaimakon ya yi mata daɗi ƙarnin ƙwan ya dame ta, sannan da dadddare shinkafa da mai da ya ji shi ma ba ta ci da yawa ba. Ita a rayuwarta tana don cimma mai daɗi, a lokacin tana gida duk inda za ta samu kuɗi ta ci abinci da kyau sai ta yi. Maza kuwa kullum cikin roƙon ayi mata take away take yi. Da zarar sun kira ta sun gaya mata za su zo. Buƙatar da za ta bijiro a kawo mata abinci. Ta saka a ranta a gidansa za ta ci abin da ta ga dama, amma sai ta ga saɓanin haka. Yanzu haka ma ganin taliya ake dafawa ya ƙara ƙular da ita za ta sauke fushinta kan Nasreen. Ko jiya sun kai kusan ƙarfe ɗaya tana masa magiyar ya canza cimar gidansa, amma ya shafawa idanunsa toka, ya yi kunnen uwar shegu da ita, domin da ga ƙarshe filo ya sanya ya toshe kunninsa. Da ya ga ba zai yi ba, sai ya ɗauko wayarsa ya sanya iyafis ya barta tana ta ɓaɓatu.
"Sai yanzu kika da damar girki?" Ta furta a gajarce tana kallonta.
Jin abin da ta ce ya sanya ta yi murmushi ta kalle ta."Akwai uban da na ke yi wa aiki?"
"Babu, amma shi wanda ya aure ki ya ga kin fi dacewar ki tsaya a matsayin kukunsa."
"Alhamdulillah tun da kin ce babu kin samu amsar tambayarki."
"Ke ni fa ba sa'arki bace, domin ko kalona kika yi kin san babu abin da za ki mora a jikina."Ta ƙarashe maganar tana juya makamakan mazaunanta.
Eh tabbas in har ta ce za ta yi faɗa da ita, san babu abin da za ta tsira, amma duk da hakan sai ba ta karaya ba." Ni ba ni da lokacin ki saboda ban dawo don na rinƙa faɗa ba."
Tsaki ta ji jin abin da ta ce,"Wallahi zan yi maganin ki da ke har mijinki."
"Allah kawai ke da wannan ikon." Ta ba ta amsa tare da ɗaukar ruwa tana wanke albasa.
Tsaki ta yi ta juya ta fita. A falo ta zauna ta kunna kallo. Ƙara ta ƙure sosai kuma waka ake yi. Nasreen ba ta kula ta ba. Ta gama abincin sannan ta ibi nata ta fito zata shiga ɗakinta.
Rashida da take tsaye tana rawa tana juya mazaunanta ganinta ya sanya ta ƙara ƙaimi. Kallo ɗaya ta yi mata ta ɗauke kanta, domin abin dariya ya bata. In tana mata gwaɗashe da jikinta ba da shi, sam hakan ba zai dame ta ba, domin Allah ya halicce ta. Tana son kiɓa amma bata fatan ta yi irin nata da ya wuce misali.
Bayan ta karya sai ta hau Whatsap. Ganin Maman Muwaddat, ta tura mata hotunan hijaban da za ta ɗaura a status, ya sanya ɗora sannan ta shiga facebook ta yi posting.
Sauka ta yi sannan ta ɗauki littafan makarantarta tana dubawa. Tana ta karatun har zuwa karfe ɗaya. Bayan ta yi sallah ta miƙe don ta shirya ta ɗauko Raihan.
Tana tafiya wayar Mama ta shigo da sauri ta ɗauka. "hello mama,"
"Na'am kina lafiya?"
"Lafiya lau, ɗazu ka kira ba ki ɗaya ba?"
"Eh ina sallah da kuma na gama sai wayar ta mutu babu caji, ya zaman na ku?" Ta karashe maganar da tambaya.
"Lafiya lau Mama."
"To ki ci gaba da haƙuri Allah ya yi miki albarka."
"Amin," Ta amsa sannan ta kashe wayar. Rungume wayar ta yi tana jin ƙaunarta. Fatanta Ubangiji ya ba ta abin da za ta ɗauke ɗawainiyarsu, ta zame gurbin Ya Ahmad ko ta yi fiye da shi.
Kamar yadda ba ta yi tunanin zai dawo ɗakinta ba, haka ya faru domin har ta yi sati ɗaya a gidan bai leƙo inda take ba. Hakan bai dame ta domin tafi bukatar ya yi rayuwarsa ta yi nata. Ta ci gaba da harkanta cikin kwanciyar hankali.