← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 92

Sashe 81

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana zaune a falo, suna ta shawarar bikin sai ga kiransa. Murmushi ta yi ganin ya sauko. Ba ta yi tunanin yana Kofar gida ba. Da sallama ta ɗauki wayar.

"Ina ƙofar gidanku." Ya ce tare da kashe wayar bayan ya amsa sallama.

"Innalillahi! Wai dama haka mutumin nan yake da rigima?" Ta yi wa kanta tambayar cikin mamaki.

Dogon hijabi har ƙasa ta sanya sannan ta gayawa Mama."Amma da gida kuka shigo sai ku tsaya a waje?" Ahmad ya ce .

"Gaskiya ki je ki ce masa ya shigo." Mama ta ƙarashe maganar tana kallonta.

"Ok tom." Ta ce sannan ta fita.

Tana hanya ta ga text ɗinsa ta taho masa da yaransa. Murmushi ta yi sai ta koma gidan ta taho da su.

Da sallama ta ƙarasa, tana shaƙar turarensa da ya kashe mata jiki. Amsawa ya yi, yana basar da ita, hankalinsa na kan yaran kamar su ya zo gani.

"Ina wuni?"

"Lafiya mai kika yi wa Musaddik ya ƙi magana."

"Rigima kawai yake ji shi da Raihan ne." Ta ce masa tare da zama bayan motarsa hakan ya ƙular da shi.

"Ok, kira Zainab ta shiga da su ga tsarabarsu."

"Tom Allah ya ƙara buɗi." Ta ce tare da kiranta.

Ba ta ɗauki lokaci ba, ta fito da sallama ta kwashi yaran bayan ta gaishe shi.

Sun yi shiru yana kallonta."Abin da kika yi kin kyauta?"

"Ya Damir mai na yi? Ina da hidima sosai a kaina kuma har tafiya zan yi."

"Ba matsala za mu je tare sai mu kama hotel."

Dariya tayi kawai jin abin da ya ce."Mu bar ofis sai bayan bikinmu."

"Maganar ya wuce ga shi ban ji haushi ba na zo."

"Ina maka barka da zuwa my Hearthrop."

Kalmar da ta gaya masa, ya ɗan sanyaya ransa har ya murmusa.

"Please ki dawo gaba." Ya ce mata yana nuna mata kujerar mai zaman banza.

Babu musu ta dawo gaban ta zauna tana kallon shi.

"Mai kike shiryawa? Ina son ki gama tsarinki na sani."

"Babu don ko wani taro ba xan yi ba bayan ɗaurin aure."

"Dole za a yi karki manta ba mu kaɗai bane."

"Haka ne sai dai don su."

"Na yi magana da masu furniture da kuma kalar fenti. Za su tura mini komai da na ke so na zaɓa, saboda so na ke a canza komi na gidan. Zan tura miki sai ki duba wanda ya yi miki."

"Ka zaɓa duk abin da ya yi maka ina son shi."

"No gidanki ne kece Ya kamata ki zaɓi komai. Maganar lefe Mommy ta ce akwai wacce take zuwa Dubai za ta haɗo."

Kanta ne ya faɗi jin abin da ya ce sai ta murmusa ta ce,"Shikenan, zan zaɓa Allah ya ƙara buɗi."

"Amin kuma duk abin da kike so, na hidimar biki ki gaya mini. Nawa zan bayar gyaran jiki?"

Hannu ta sanya ta rufe fuskarta cikin jin kunya."Ko nawa ne"

"Don Allah stop behaving kamar ba ki san rayuwar aure ba, mun san yadda zaman aure yake. Ki cire kunya mu tsara rayuwarmu."

"To," Ta ce ba tare da ta faɗa masa kuɗin ba.

"Zan tura miki kuɗi sai ki fara in sun yi kaɗan ki sanar mini."

"To," Ta ƙara cewa.

"Ba ki gaya mini kina da ciwon magana ba?"

"Ni? Ina magana sosai."

"Na ga yanzu kin fara ai, kuma gara ki sake sani, saboda ni da iyalina bazan zauna mu yi zaman kurame ba. Sosai na ke sakewa da su."

"To," Ta ƙara ce masa. Ganin haka ya matso daga kujerarsa zuwa inda take. "Bari na fara ƙoƙarin cire wannan kunyar, tun kafin daren amarcinmu ki hanamu shan amarci."

A tunani ta ya matso ne, don haka fit ta fice daga cikin motar. Bayan takaici dariya ma ta ba shi."Ni zan tafi kafin ki sanya mini hawan jini, da wannan kunyar taki. Duk wayon amarya sai an sha manta."

"Sai da safe." Ta ce tare da wucewa da sauri.

Dariya sosai ya yi, sannan ya tayar da motar cikin takaici. Shi da ya zo ya rage zafi, amma ko hannunta bai samu damar riƙewa ba."Wannan kunyar ya yi yawa dole ki daina" ya ce yana girgiza kansa

Da ta shiga cikin gida sosai take yi wa kanta dariya. Tana kwance tana tunaninsa, sai ga alert na kuɗi har sai da ta razana. Da ta kira shi kin ɗagawa ya yi kamar ya san abin da za ta yi. Juyawa ya yi tare da ɗora wayar a ƙirjinta. Tana mamakin mijin da Allah ya yi mata tagomashi da shi.

Washegari da safe, tana zaune tana lissafin inda za ta fara hidimar bikin. Marwana ta kira ta."Hello Marwana?" Ta ce bayan ta ganka wayar a kunninta.

"Nasreen ina maganar da na yi miki? Ki shirya muje." Ta ce mata cikin sigar rarrashi.

"Ni fa babu inda za ni, zan dai gyara kaina, amma ba zan yi ɗinki ba na cutar da kaina. Kan namiji na je na kashe kaina."

"Wallahi ba kashe kai bane. In har na san za ki cutu ba zan gaya miki ba. Ki kauda batun Ya Damir ɗan'uwane, kin san na zaɓe ki na ƙyamar shi ko? So nake ki kankaro ma kanki mutunci sosai. Hatta magunguna na siya miki supplements na gyaran jiki wanda basa cutarwa. Ni ma ina sha kin ga ba cutar da kaina ba."

"Ni fa tsoro na ke ji, saboda an ce yana kawo kansa. Bana son na cutar da lafiyata."

"Tabbas yana kawowa, amma akwai masu kyau waɗanda za su ƙara miki lafiya da kyau. Ya kamata ki kankaro ma kanki mutunci a gurinsa. Yadda yake rawar jiki ya ƙisa ki gyara kanki. Ko ɗazu sai da ya gama wa Momi magiyar a rage bikin."

Murmushi ta yi ta ce,"Yaushe za mu je?"

"Yauwa jibi ki shirya."

Ajiyar zuciya ta yi, ta kashe wayar bayan ta ce,"Allah ya kaimu." Duk da tana tsoro amma, ita kanta tana son ta samu daraja da ƙima a gurinsa.

Da ta shawarci Mama, ta amince ta bata goyon baya, domin yanzu ya zama ruwan dare. Ko haihuwa mata suka yi suna zuwa a yi musu ɗinki. Ballantana ita da za ta yi sabon aure. Ita kanta sai ta ji za ta jure zafin, don ta samu daraja a gurinsu.

Shawara suka yanke, sai Damir ya yi tafiya sannan za ta yi, tun da sun ji ɗan zumuɗin yana maganar zai tafi jibi. Don haka dai suka bari sai ya tafi, saboda ba sa son ya sani, in babu kuma yana nan dole ya gane.

A yadda ake kururuta abin, da ba ta ji zafin kamar haka ba, wataƙila kuma don asibitin da suka je ƙwararre ne. Baya sun dawo duk ta bi sharaɗin da likitar ta gaya mata.

Ta ɓangaren Ahmad shi ma, waje ya ba da aka haɗo mata lefe, sosai yake shiri domin hatta sabon gidansa. Sai da akayi wasu gyare-gyare. So yake ya mayar da ita zinariya domin ta cancanta.

Ya rage biki saura sati ɗaya Damir ya dawo. Washegari aka kawo lefe naban mamaki. Nasreen kama bakinta ta yi cikin mamaki.

"Kai wannan kayan sun yi yawa kamar albazaranci ne." Mama ta furta tana kallon kayan, domin ta kasa ɗaga kayan, saboda tsabar yawansu.

"Gaskiya Ya Damir kamar bai san zafin kuɗinsa ba." Ta furta tare da ɗaukar makullin motar tana murmushi.

Haka mutane, suka rinƙa shigowa ganin lefen Nasreen, domin babu budurwar da aka taɓa ma irinsa.

Ɗaki ta shiga ta zauna, tana ƙoƙarin kiran layinsa sai kiransa ya shigo. Cikin murya mai taushi ta yi sallamar.

"Wannan muryar ta ki kar ta sanya yanzu na yi booking Hotel."

Cikin jin kunya ta rufe idanunta." Please Nasreen ba ki ƙosa ki tare ba?" Ya yi mata tambayar da muryar da ya tabbata mana da matsuwarsa.

"A'a da na so na ke na roƙe ka aka ƙara kwanaki..."

"Please stop jorking, in har ba so kike kiga rashin kunyata ba, don wallahi da dai Mama ta kauda idanunta ɗakin ki xan za dawo."

"Ya..."

"Don't say anything, ba kya tausayina? Tsawon lokacin da na ɗauka babu mata ai ya kamata ki tausaya mini. Ina fatan ranar amarcinmu za ki cire wannan kunyar, saboda so na ke ranar ta zama memorable, duk lokacin da muka tuna sai mu kasace cikin farinciki?"

Wayar ta cire tana kallon mumbarsa cikin mamaki. She was like dama haka yake? Saboda gabakiɗaya ya canza hatta muryar da yake mata magana da shi, mai sanya kasala da shiga wani yanayi ne. Shi ya sa tun da aka ɗaura auren ba ta son haɗuwa da shi. Those sexy eyes of him, suna sanya ta shiga cikin wani yanayin da bata son ya fahimta.

Tana wannan tunanin, ta ji ya kira sunanta da muryar da ya kashe mata jiki.

Sai da ta ja numfashi, sannan ta amsa can ƙasan maƙoshinta.

"Mai kika shirya wa ranar amarcinmu? I mean wane irin tarba za ki yi mini ina shigo, Are you going to hugg me or give me a hot kiss?"

Da sauri ta kashe wayar, ita kam yanzu ya daina ba ta mamaki sai dai al'ajabi. Kwanciya ta yi kan gado, domin ya saukar mata da kasalar da ko numfashi da ƙarfi take fisgo shi.

Damir kuwa, ganin ga kashe wayar sai ya yi dariya sosai."Yarinya za ki sake ne, don wataƙila ba ki san mijin da kika aura bane."

Tura mata da hotunan furnitures da aka kawo ya yi, sannan ya ɗauki fentin da aka canza. Tare da tura mata text ta duba duk abin da bai yi ba sai ta faɗa a gyara.

Murmushi ta yi, tana duba gidan cikin tsananin mamaki. Wai yau ita ce za ta zauna a irin wannan gida? Mai kama da al-jannnar duniya.

Bayan ta gama duba kayan, sannan ya fita zuwa falo, don ta je ta kira mai dilka ta ci gaba da mata.

Amarya Marwana ita ma, ɓangaren su ana ta shiri domin har an yi danki an shirya komai. Gida ya tsaru sai jiran amare kawai.
Chapter 81 · 0% Book details