← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 92

Sashe 12

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka take yi sosai har Mama ta gama dafa mata ruwan wankan ta kuka mata bayi. Tana wanka tana kuka. Abin da take gudu kenan, wannan dalilin ya sanya ta jure duk wani tozarci, amma ga shi daga ƙarshe dai dole hakan ta faru. Bayan ta gama wankan ta shafa mai. Ta kwanta sakamakon zazzaɓi mai zafi da ya rufe ta.

Tunanin haɗuwarta da Faruk da zaman auren da suka yi take yi. Lokaci guda ta fashe da kuka tana jin babu wani namijin da za ta kuma yarda da shi. Ya kamata mu ji asalin su sannan auren soyayya ko ƙiyayya suka yi da rayuwar aurensu ta ƙare a haka.

WAIWAYE, ADON TAFIYA.

Bukar Nadamu. Shi ne sunan mahaifin Nasreen. Mutum ne mafaɗaci da ita faɗin magana da za ta ɓatawa mutum rai tun yana ƙuruciyarsa. Ya tashi cikin rayuwar talauci domin tun yana ƙarami, Allah ya yi wa mahaifinsa rasuwa. Mahaifiyarsa ta ije shi a gurin ƙanin mahafinsa ta ƙara aure.

A maimakon ya taimaki maraicinsa sai kawai ya ɗauki rayuwar nanaye.. Babu ruwan shi da zuwa islamiya ballantana boko da ba ta yi suna a ƙauye su ba.

Ƙanin mahaifinsa Bala ya so ko karatun Muhammadu ya yi don ya taimaki maraicinsa, amma sai ya shafawa idanunsa riƙa ya yi kunnen uwar shegu da duk wata barazana da yake masa.

A haka ya ta so rayuwa babu tsari, sai dai neman kuɗin da ya sanya a gaba babu dare babu rana.

Haka ya girma har ya isa aure. A wannan lokacin Allah ya buɗa masa, har ya gina gida kuma yana samu babu laifi.

Take ya fara neman aure inda ya samu Mariya ta kafe sai shi. Cikin ƙankanin lokaci aka tsayar da bikin har lokaci ya yi.

Bayan sun yi aure ta yi haihuwa biyu. Ya ƙara rakito wani auren. Sai dai matar ba su yi shekara biyu ba, suka rabu ta bar masa yaro ɗaya da suka haifa.

Ya fara zuwa birni sai likafa ta ci gaba, har ya sayi gida mai ɗauke da ciki huɗu sai turakarsa. Take ya ɗauki burin auren mata kala-kala ya sa ya wa ranshi. Kasancewarsa mai hange-hange.

Bayan sun tare ya ƙara auri wata matar ta yi haihuwa ɗaya suka rabu da cikin na biyu.

A ƙalla sai da ya auri mata biyar, suna rabuwa kuma ko wacce sai ta haifa masa. Wasu su rabu da cikin na biyu.

A unguwarsu ya ƙalla idanu ya ga Fatima. Tun da ya ganta ya kashe ya tsare tare da kashe mata mahaukacin kuɗi, amma san ba ta taɓa ɗaya idanunta ta kalle shi ba.

Fatima mahaifiyarta ta rasu tun tana ƙaramar. Tana zaune da mahaifinta da matarsa Mama Hajja. Tun da ta ga mahaukacin kuɗin da yake kashewa ta mace dole a ba shi ita.

Ta yi kuka ta yi kuka domin sam ba shi a cikin mazan da take so. Abin da yafi ɗaga mata hankali auri sakin da yake yi.

Tun da Mama Hajja ta na ce kan dole ta amince, don ta san babu makawa sai an yi. Cikin ƙankanin lokaci ka sanya ranar bikin.

Tun bayan da aka yi auren ta fara nadama, saboda mugayen halayensa da tuntuni tana da labarin wasu. Sam bai damu da ibada ba, kuma babu ruwanda da kula da tarbiyyar 'ya'yansa.

Wani irin rayuwa ake yi a gidan mara tsari da kan gado.

Bayan ya aureta ta yi burin ta bar gidan, amma haƙarta ba ta cimma ruwa ba. Sai ta haƙura ta daina zubar cikin da take samu. Cikin ikon Allah ta ƙara samun wani cikin. Wata tara ta haifi yaro namiji aka sanya masa suna Ahmad.

Bayan ta haife shi, ya ƙara auren wata jarabbabiyar mata bazawara. Sai dai, ba su dade ba ya sake ta, saboda ita kanshi ta hayyace shi. Kasancewar a lokacin da ɗan kuɗinsa ya ƙara neman aure. Bazawara mai haihuwa uku. Tunda ta zo gidan ta shiga jera masa 'ya'ya kwanuka har sai da ta yi shidda. A lokacin ko da ya yi ninyar sakinta babu wanda zai kula masa da 'ya'yan da ta tara masa.

A lokacin Ahmad ya girma har an yi masa kanni guda uku. Rayuwa ta fara tafiya girma ya zo masa. Ga shi ya tara 'ya'ya da yawa.

Shi kansa a wannan lokacin arzikin nasa ba kamar da ba. Kasancewar yadda komai ya canza. Ga shi Allah ya jarrabce sa sana'ar ɗan kunnin da yake yi ba kamar da ba, saboda nauyi sun yi masa yawa. Don watarana jarin da zai saro sai ya gagara.

Tun da ga wannan lokacin ya sakin musu komai, duk da cewar ko da can ba ɗawainiyarsu ya ɗauke ba, domin sau ɗaya ake girkin tuwo da daddaren, sai kuma safiya a dama koko. Da rana kuwa, kowa ta sa ta fishshe shi. Abin sai ya lalace don wani lokacin tuwon ma gagara yake yi.

Abin takaici a haka ya je ya tattara 'yan kuɗaɗen da yake juyawa ya ƙari aure. Tun daga wannan lokacin lamarin ya ƙara rikicewar sosai, domin wasu wannan suke yi wasu kuma tsurfau.

Fatima ta ƙara haihuwar yara biyu suka zama biyar, Yayarsu Mariya sai Ahmad da Musa, da Nasreen sai kuma Zainab.

Ta yi iya matuƙar ƙoƙarin ta ta ba su tarbiyya, kuma ta ci sa a yaran sun taso daban.

Gidan kullum cikin fada da zage-zage suke yi, amma ban da 'ya'yanta. Karatu kuwa bai damu da ya sanya kowa ba. Makaranta ce ta firamari duk wanda ya ga dama ya je. Islamiya kuwa da dole sai an bayar da kuɗi, in har ya daure ya yi maka rijistar ba zai ƙara kula ka ba da maganar kuɗin makaranta.

Daga baya ma, ɗan kayan makaranta da islamiyar da yake sanyawa duk sai daina. Banu ruwanda sai dai ya haifa ya barwa uwa, domin ai kai yanayin da abinci sai ayi wata bai ba da ba.

Rayuwa ta miƙa yara sun girma kuma sun taso. Gidan ya cika da yara sosai marasa tarbiyya, sai waɗanda Allah ya tsallakar.
Ya aurar da mata sosai duk wanda ya zo babu bincike zai aura musu, domin burinsa duk ya aurar da su ya daina ganinsu.

Ahmad yaro mai hankali da tunani. Tun da ya girma ya fahimci irin mahaifin da suka samu. Ya yi ma kansa karatun ta natsu. Daga ƙarshe haƙura da makarantar ya yi. Aikin garaji ya fara zuwa, in ya dawo ya yi sallar magariba sai ya tsaya, karatun da ake koya wa a masallaci kafin kiran isha'i.

Yana matuƙar ƙoƙarin ganin ya biya wa ƙanninsa bukatu. Tuni ya ije makaranta don su yi, musamman Nasreen da ya ga tana da hazaka da don makarantar.

Nasreen yarinya kyakkyawar gaske mai hakuri. Wankan tarwaɗa ce ga hanci da gashi. Sannan ga ta doguwar sosai. Tana da hakuri saboda kusan yaran gidan babu wanda ya isa ya nuna musu ɗan yatsa. Ko ya taɓa su ya kwana lafiya, amma ita duk a unguwar koya ya sa ta da haƙurin gaske.

Ba ta da surutu ga saurin kuka. Duk lokacin da ka shiga gidansu za ka ganta tana zaune da littafi tana koyon Turanci, domin Allah ya yi ta da don ta ga tana turanci. Wannan dalilin ya sanya ta dage matuƙa gaske! Ganin haka ya sanya Ahmad duk ya fita sai ya fito mata littafin koyon Turanci da Novels.

Haƙarta kuwa ta cimma ruwa, domin ta iya turanci sosai, a lokacin tana aji shidda tana shirye-shiryen zana neco.

Ahmad ya biya mata duka za ta zana. Yana da burin ta yi karatu. Duk da dawainiyar ci da su da yake yi, amma hakan nan ya yi ƙutu-kutu ya biya mata duka, don zai iya gwammacewa su kwana da yunwa, amma ta yi karatu.

So yake ya cika burinsa na karatu a kanta, ganin yadda take da hazaƙa da saurin ɗaukar abu.

Cikin ikon Allah ta cinye jarrabawar har da jamb, da ya biya mata ta samu admission za ta karanta microbiology. A jami'ar Ahmadu Bello University Zariya.

Ahmad ya yi murna sosai, don haka ya dake ko da zai yi dako sai ya tara kuɗin da za ta yi karatun.

Ta fara karatunta cikin sa'a da nasara. Matsalarta ɗaya rashin kuɗi, duk da cewar yana ƙoƙarin, amma wani lokacin ta kan fita makarantar na ta karya ba, kuma sai dai ta taka ta je a ƙasa, duk da akwai tazara a tsakaninsu.

Ta kama kanta sam ba ta kula 'ya'yan masu hannu da shuni, domin ƙawarta ɗaya ce. Fadila wacce ita ma 'yar gidan Malam Shehu ne kamar ita.

Ta dage ba ta ji ba ta gani kullum cimin karatu take. A lokacin da result din su na first semester ya fito. Kowa a abin sai da ya cika da mamaki, domin babu wanda zai yi tunanin ita ce wacce ta fi ƙoƙarin a cikin abin, kasancewar wasu ba su santa ba.

Wasu suka cika da mamaki, musamman kallon da suke mata na yar talaka, don ko kayan da take sawa ba su da wani kyau sosai.

Suna cikin shirye-shiryen zana jarabawar su na second semester. Kwasam ta dawo makaranta, suka haɗu da Faruk da ya shigo cikin rayuwata babu zato babu tsammani.

A ranar an yi ruwan sama. Sun daɗe a makaranta, suna jiran ruwan da ake tsugawa, tamkar da bakin ƙwarya ya tsaya su tafi, amma kamar ana ƙarawa.

Hankalinsu ya tashi ita da Fadila, don ita Nasreen ko kuɗin mota da za ta koma gida babu.

Sun yi jugum-jugum har aka fara kifaye-kitlrayen sallah, sannan suka samu ruwan ya tsaya.

Fitowa suka yi zuwa bakin titi. A lokacin duhu ya yi. Ga shi duk keke napep ɗin da suka tsayar a cike.

Suna cikin wannan halin na tarabbbi, suka ga mota ash colour ta ja ta tsaya a gaban su.

Tsaki Fadila ta yi tare da jan hannunta a tana faɗin,"Ji wannan wawan mutumin, muna tsaye muna neman napep kuma ya tsaya mana a hanya."

Ba tare da ta ce komai ba, ta yi shiru saboda yunwar dake ƙwaƙwularta don ko da safe ruwan koko ta sha.

"Bayin Allah." Ta ji wata murya ta furta a cikin taushi.
Chapter 12 · 0% Book details