Sashe 3
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai tsaye ɗakin Nasreen ya shiga, yana mamakin halinta mai ladabi kunama. Ya tura ɗakin ya shiga, amma sai ya ji ta kulle."Ke Nasreen buɗe mini ƙofar nan, kuma ki zo ki buɗe mini get."
"Wallahi ba zan buɗe ba, domin raba kwanakin aiki za a yi. In har na ga matar da kake kira ta mai biyayya da komai tana yi zan yi, saboda yanzu tun da ka samu matar ƙwarai zan koyi komai daga gare ta." Ta furta masa da ƙarfi yadda zai ji.
Haushi ya sanya shi kaɗa kansa ya fice daga gidan. Tunanin dukan da zai yi mata in ya dawo yake yi.
Tana kwance har aka kira sallah. Ta yi sallah ta ɗauki Alqur'ani tana ƙarantawa. Addu'a sosai ta yi wa Ahmad tana roƙon Allah ya bayyana shi, sannan ta yi wa Batula. Tana addu'ar hawaye yana sauka daga ƙuncinta. Tana zaune har biyar da rabi ta yi. Kamar ba za ta yi girkin ba, sai kuma ta tashi ta shiga kicin don ta girka, tun da in bata yi ba ta san ba za ta ci ba.
Tana girki tana sauraren karatun Alkur'ani. Bayan ta gama ta fito da ta shiga cikin ɗakinta. Rashida ta gani zaune a falo da wasu 'yan iskan ƙananan kaya tana kallo. Kallon banza ta yi mata kafin ta mayar da idanunta ta rama. Abincinta ta sanya a kula ta shige cikin ɗakinta.
Kamar yadda ba ta sanya a ranta ba zai shigo ɗakinta haka ta ya faru. Bai shigo gidan ba sai da aka yi Isha, saboda ya san ba zata buɗe ba, da kanshi ya buɗe get ya shigo. Babu kowa a falon sai Rashida da take zaune cikin wasu arnan kaya. Ta yanke shawarar ta yi mishi kissa da lalama ta ga ko za ta samun kansa. In har ya fujire to za ta fito masa da ainihin kalarta.
Ganin ya shigo, ya sa ta miƙe da sauri kamar wata ƙaramar yarinya ta faɗa jikinsa. Ture ta ya yi ya zauna yana harararta."An gaya miki ni sakarkarun maxan nan ne, da za ki gaya mini magana , sai ki dawo ki rarrashe ni?" Ya tambaye ta fuskar a ɗaure.
Ganin ya gwasile ta da kuma tambayar da ya yi mata, sai ta koma ta zauna jikinta a saɓule."Gaskiya na gaya maka Faruk da ga ƙinta sai ɓata."
"To ki riƙe gaskiyar ta ki bana so, saboda wallahi in har kika ce za ki yi mini shishshigi, a lamarina zan gurza miki rashin mutunci."
"Allah ya ba ka sa'a. Ni ma ba kanwar kasa bace." Ta gyara zama tana faɗin haka a ranta, amma a fili kallonsa kawai ta yi ta tura baki.
Ganin ba ta ce komai ba ya saki tsuka."Tashi ki ɗauko mini abinci ko sai na roƙa za a bani?"
"Na ga ba ni na girka ba? Sai ka kira wacce ta girka ta ɗauki maka, na fahimci girkin nawa ne ba ka so, shi ya sa daga dawowarta ka ce ta karɓa." Ta ba shi amsa ba tare da ta motsa ba.
"Ashe kin san kwaɓa kike mini kin san ba ki iya girki ba. Wannan dahuwar cikin shigen ne bana so, sannan ki cika yaji kamar na wasu mayu."
"Sai ka ci gaba da ba ta tun da ta iya."
Ganin ba za ta tashi ba, sai ya saki tsaki ya miƙe. Har ya nufi ɗakinta sai kuma ya fasa. Kicin ya shige ya ɗauko kular abincin.
Yana fitowa ta saki tsaki ta shige cikin ɗakinta. Kallonta cikin mamaki yake yi ganin yadda ta canza lokaci guda.
Sai da ya kammala abin da yake yi, sannan ya ɗauki wayarsa ya shige cikin ɗakinsa.
"Yana ƙoƙarin kulle ƙofa sai ga shi ta shigo da kayan bacci a jikinta."
"Ki koma inda kika fito ba hushi kika yi ba?" Ya ce mata cikin tsawa tare da nuna mata hanya.
"Ai dama na san ka kitsa abu a zuciyarka. Wato so kake ka kwana da matarka ko?"
"Wa Allah ya kyauta ga yar duma-duma mai zan yi da jiki duk ƙashi, amma ki sani ba zan ɗauki iskanci ba, saboda ba a yi macen da za ta juya ni ba."
"Sai ni Faruk ka jira lokacin da zan juya ka tamkar waina a cikin tanda." Ta ce a ranta amma a fili kallonsa ta yi sai kuma ta shiga cikin jikinsa.
"Haba my love ka san ba zan iya fushi da kai ba." Ta ƙarashe maganar cikin kissa tana son haɗa bakinsu.
Ganin tana son nasara a kansa sai ya tureta ya zauna a bakin gado. Biyo shi ta yi ta faɗa jikin shi."Wallahi in har kika ce za ki rinƙa tambayata kuɗi, kina shiga lamarina za mu sa ƙafar wando ɗaya dake, saboda ina ba ki abinci dama aure ba ci da sha bane."
Jin abin da ya ce sai ya ba ta mamaki, amma da yake sulhu take nema. Ƙara rungumeshi kawai ta yi tana mishi salo. Ba tare da ya ja aji ba, ya ba da kai bori ya hau.
A lokacin da Nasreen ta ji uhunsu hankalinta ya tashi sosai. Saboda takaicin rayuwar dabbobin da suka ɗauki kuka ta fashe da shi. Tunani ta fara ya za ta yi ranar da Raihan ta girma ta fahimci abin da suke yi. Da sake wallahi ba za ta saɓu ba, an yi sadaka da bazawara." Ta furta tana share hawaye. Bata kwanta bacci ba, har sai da suka dawo hayyacinsa Sannan ta samu ta rintsa.
Faruk kuwa har da biyu ya yi don ta ji su. Babu irin yadda bai yi ba, don su rinƙa haka, amma ta kawo masa ƙauli da ba'adi, yanzu kuwa tun da ya samu sai ya more abinsa.
Kasancewar sun sha love, ba su tashi ba har aka kira sallah aka sallame. Nasreen tun kiran sallar farko ta tashi ta yi sallah. Bayan ta gama addu'ointa ta ninke daddumar. Raihan ta tayar a lokacin shidda har da rabi. Ta yi sallah, sannan ta yi mata wanka ta shiga kicin don ta shirya abin kari.
Tana shiga taga dankalin hausa ya siyo sai ƙwai guda biyu. Tsaki ta saki, ta fara fere ɗankalin. Bayan ta soya ta ibi na ta sannan ta sanyawa Raihan a kula da ruwa.
Ɗakinta ta fara gyarawa, sannan farko tun da ba datti ya yi ba, cikin ne da yake yana buƙatar goge-goge ta barshi sai ta dawo kai ta makaranta. Bayan ta karya sai ta fice zuwa kaita.
Biskit da bobo ta tsaya ta siya mata sannan ta kai ta makaranta. Da ta dawo ba ta shiga cikin gidan ba. Gidan Maman Muwaddat ta shiga. Da sallama ta shiga cikin gidan.
Maman Muwaddat da take falonta, tana kaye-kayen kwanonin da suka yi breakfast. Cikin sauri ta ƙaraso ƙofar falon jin muryarta.
"Nasreen," Ta kira sunanta tare da kama hannunta suka shiga ciki.
"Nasreen, ashe Baba dai sai da ya tilasta miki kika dawo?"
"Ya zan yi? Baba sam ba ya yi wa rayuwata adalci."
"Gaskiya ba ya kyautawa."
"Ai na san cewa tun da ya Ahmad ya ɓace dole ya mayar da ni."
"Nima yana ɓacewa na sanya dawowarki a raina, amma sam kar ɓacewarsa ya zama karayar gwiwarki, saboda Nasreen ke ya kamata ki tashi ki ƙwaci 'yancin kanki. Ko da ace yana nan ya yi mishi hulɗin kuka rabu, in kika je wani gidan ba fata nake miki ka, kin san yanzu maza sai shiryar Allah. Akwai nagari amma da wasu sam ba su da kirki. In yana miki wulaƙanci shi ma hakuri za ki nuna Ahmad shi zai ƙwayar miki 'yanci? Bacewarsa kamar Allah ya ɗauke shi, don ki tashi ki zama jaruma ki fuskanci rayuwa. Jarrabawar rayuwa ba ta ƙare wa, domin Allah subhanahu wata'ala ya ce a cikin littafinsa mai tsarki,"Shin kun yi imani kuma kuna tunanin ba za mu jarrabce ku ba?" Da zarrar kin gama da wannan ƙaddara sai wata ta shigo. Matuƙar ba mutuwa kika yi ba, Ubangiji ba zai daina jarrabtarki ba, don haka ki tashi ki zama jaruma ki fuskanci ko wane irin ƙalubale. Nasreen haƙurin ki yana da yawa. Ban ce kar ki yi hakuri ba, amma ya kamata ki rage, saboda a yanzu rayuwa mutum mai hakuri ake takawa. Kina ganin halin da dangin mijina suka sanya ni. Da ina musu sanyi har cikin gidan nan ƙanwarsa take zuwa ta yi mini rashin kunya, amma tun da na rage hakuri na yi maganin ta, ga ba shi na zauna lafiya ba? Kamar haka za ki yi Nasreen a yanzu kar ki bari Faruk ya yi miki abin da ya saba. Kin ga ya yi aure wallahi in kika yi sakwa-sakwa har da amaryarsa za su haɗu su ci kashi a kanki."
Murmushi mai ciwo ta yi tana kallonta."Kin san wace ce Nasreen a yanzu? Kin san yadda zuciyata ta bushe? Tun da aka nemi Yayana wanda nake ganin shi ne tamkar ubana aka rasa. Wanda na ɗauka a matsayin haske a gare ni, amma y tafi ya bar ni. Zuciyata ta bushe bana jin tsoron kowa. Ji nake yi a yanzu ko a dokar daji zan iya rayuwa. Faruk ba ya gabana ba ce za yi masa rashin mutunci ba, saboda rayuwar aure ba rayuwar dabbobi bane da za mu rinƙa dabbaci, amma wallahi ba zan ƙara yarda ya wulakanta rayuwata ba. Ya fita a raina. Ba ni da yadda zan yi ne, bisa tursasawar Baba ya sanya na dawo gidan nan."
Kallonta ta yi cikin tsananin mamakin kalamanta. Hannunta ta kama ta riƙe tana fatan har cikin zuciyarsa maganganun suke fitowa."Da kyau Nasreen ina fatan hakan. Ki miƙe ki ƙwaci 'yancinki. Allah ya yi miki daraja ga ki mace kuma mutum, sannan ki kama sama'a kar ki ji tsoron hana ki da yake yi. Yanzu rayuwa ta canza komai ya koma social media in dai kina da waya androin za ki yi sana'arki ba tare da an sani ba. Kin ga tun da mahaifinmu ya rasu, aka raba mana gadon sai na sayi gida. Ragowar kuɗin dama akwai ƙanina Musa da yake ɗinka hijabi ko wane iri. Kuɗi na ba shi ya ɗinka mini da yawa. Daga ɗorawa a status na shiga groups da yawa, kin san ya kare?"