Sashe 69
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana zaune tana karanta wasikar jaki, kiran Marwana ya shigo. Ɗagawa ta yi tare da yin shiru bayan ta yi mata sallah.
"Nasreen lafiyarki kuwa?"
"Ya Damir ne ya mayar da ni sakatariyar...." Kafin ta ƙarashe ta ji ta zabga uban ihu tana kabbara.
"Addu'a ta ta karɓu Nasreen Ya Damir sonki yake ɗawainiya da shi. Neman hanyar da zai kusanta kan shi dake yake yi."
"Hummh! Tunanin ki kenan, in har ya yi hakan ne don ya ƙuntata mini daidai na ke da shi."
"Bana tunanin haka, kin ga ya kira ki just to say thanks. Kuma ya zu ya dawo dake sakatariyarsa. Wallahi sonki yake yi tsabar girman kai ya hana shi furtawa, saboda har kama shi na yi yana tura hotonanki."
"Haka kika ce ya batun fitarmu?" Ta yi mata tambayar tana son kauda zancen.
"Dalilin da ya sanya na kira ki kenan. Ya Ahmad yake tambayata da ƙarfe nawa za mu je?"
"Shi ya Ahmad ɗin?" Ta yi mata tambayar cikin zallar mamaki tana zargin su.
Tuna katoɓarar da ta yi, sai ta daure ta ce,"Eh mene ne kike mamaki ko ba yayana bane, da zai kira ni ki yi mamaki?"
"Hmmm ki ci gaba da munafunci ku Allah zai tona asirinku."
"Tsakanina da shi girmamawa ne saboda kamar Ya Damir na ɗauke shi ba maganar soyayya."
"In ta yi wari maji." Ta ce tare da kashewa sai kuma ta yarda saboda da suka soyayya ba zai ɓoye mata ba.
Kan dole ta tattara ta koma ofishin ba don ta so ba.
Tun data dawo sai hankalinsa ya kwanta. A rana sai ya kai mata aiki sau nawa. So yake su shaƙu su rinƙa magana, amma har yanzu ya kasa samun hanyar da zai kusanta kanshi da ita, yayin da ita kuma ta kasa shaƙuwa da shi. In ya ji tana magana tana dariya sai ya ji kamar ya je ya yi ta kallonta.
Farouk kuwa, hankalinsa ya tashi sosai kamar zai yi hauka. Ya rasa hanyar da zai yi ya rinƙa ganinta, domin tun ranar da ya je kampanin ta sanya securities kar su kar bari ya zo ko ƙofar gurin.
Yana zaune cikin tsananin damuwa hawaye yana bin fuskarsa. Da sauri ya miƙe tsaye tare da yin murmushi mai kama da kuka, ganin ya samu sabuwar shawara.
Kai tsaye ya tuƙa mota sai makarantar su Raihann. Ofishin Principal ya je tare da yi masa bayani. Bai yi wani dogon bincike ba, domin shi ya sanya ta a makarantar.
Shiga cikin aijinsu ya yi ya ɗauko musu shi. Raihann na ganinsa sai hankalinta ya tashi sosai. Hannu ya sanya ya riƙe ta ganin kamar tana son kunyata shi. Musaddik kuwa har zai fara kuka.
Da sauri ya fita da su cikin makarantar kamar wanda ya yi sata. Sai da suka yi nisa, sannan ya faka motar tare da rungume su ya fashe da kuka.
Ba tare da sun damu da murnar da yake yi ba, sai suka sanya kuka Musaddik yana faɗin,"Anty Rai'an Ummm zan je."
Ƙara kamasu ya yi rungume su."Ku bar kuka ni ma mahaifinku ne. Kaicona da son kuɗi ya sanya na kasa jawo ku jikina. Ya furta ganin yadda suka tayar da hankalinsu.
Kuka suke yi sosai ganin ya kai su gidansu. Hannun Raihan ya ja tare da ɗaukar Musaddik suka shiga ciki. A falo ya zaunar da su kan kujera.
Zama ya yi yana kallonsu, cikin dana-sani ganin yadda suka takure suna kuka. Kicin ya shiga ya ɗauko musu abinci ya kawo gabansu, amma babu wanda ya yi shiru sai kuka da suka ƙara fashewa da shi.
Ta sa su ya yi, yana kallon suna kuka shi ma yana jin kamar zai yi kukan.
A kwanakin Ahmad yake ɗauki su saboda yana zama gida, amma a ranar sun fita da ogansa kan wani business ɗin za su fara, har lokaci ya yi bai dawo ba. Ganin haka ya kira numbar mai mashin da wani lokacin yake ɗauku su.
Bayan ya je ya neme su, amma ba sa nan don haka ya kira wayar Ahmad. Mamaki ne ya kama shi domin sun yi waya da Nasreen har yake gaya mata, ba zai samu zuwa ba, amma ya tura mai mashin.
"Ok to na gode." Ya ce tare da kashe wayar ya fara neman layinta.
"Hello Ya Ahmad." Ta ce masa bayan ta amsa sallama.
"Yaran nan suka wajenki ne?" Tambayar da ya yi mata ya sanya ta miƙe a razane.
"A'a ba su dawo ba ne?"
"No, kin san ba ni a gida mai mashin ya ce a ɗauke su."
"To ko Mama ta tura Zainab."
"May be bari na kira ta."
"To," Ta ce masa xuciyarta na bugu.
Kasa jiran shi ta y,i ya kira ta sai ta kira shi a lokacin yana waya. Sai da ya gama sannan ya kira ta.
"Nasreen yaran nan fa ba su a gida, kuma na kira Principal yake gaya mini Faruk ya ɗauki y....."
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Saboda me zai ɗaukar mini yara? Don ya ƙuntata mini ko? Ni dama sai da na ji a jikina kamar haka za iya faruwa." Ta furta cikin muryar kuka.
"Please ki na su dole ya dawo da su ai."
"Wallahi kuwa domin ko kotu sai na kai shi. Sam ba zan iya ba shi yarana ba, ina son su tashi cikin tarbiyya." Ta ce sai kuma kuka.
"Ki natsu yanzu yanzu zan dawo gida." Ya ce mata tare da kashe wayar, bayan ya rarrasheta ganin yadda ta tayar da hankalinta.
Nasreen uwar son yara. Yana kashe wayar ta miƙe saboda ɓacin rai ji take kamar ta rufe Faruk da duka.
Ta fito za ta je gurin Damir da shi ma ya fito zai fita. Saura kaɗan su ci karo saboda ba ta ganin gabanta. Da sauri ya kai hannu zai riƙeta ganin ta yi taga-taga za ta faɗi, saboda takalminta mai tudu daya goce.
"Please take easy Nasreen." Ya furta cikin tsananin tashin hankali.
Ganin zai riƙe ta sai ta ja baya har ta gwammce ta faɗi, sai kuma Allah ya ba ta sa'a ta tsaya.
"Are you ok?" Ya tambaye ta cikin damuwa.
"Yes." Ta ce masa tana ƙoƙarin saita natsuwarta.
Kunya sosai yadda ya rikice ya ji, sai ya fara shafa kansa zai wuce, ba tare da ya iya ɗaga idanunsa ya kalle ta ba.
"Ya Damir." Ta kira sunanshi cikin rashin dubara.
Cak ya tsaya ba tare da ya juya ba. Ganin ya tsaya sai ta ce,"Ina son zan je gida. Please akwai abin da ya taso."
Da sauri ya juyo yana kallonta, ganin yadda take ba a cikin natsuwarta ba.
"Lafiya?" Ya tsinci kanshi da tambayarta.
Har ta buɗe baki za ta ce babu komai, sai kuma damuwar da take ciki, ta gwammace gaya masa, domin ya ƙyaleta ta tafi.
"Faruk ne ya je makaranta ya ɗauke su Raihan." Ta ƙarashe maganar tare da zubowar hawaye a fuskarta. Tsoronta kar ya gudu da yaran.
Jin ta ambaci Faruk ya sanya kishi ya lulluɓe shi, amma abin daya yi da kuma yadda hankalinta ya tashi sai ya kauda batun kishi.
"Ok, sai kin dawo." Ya ce mata ba tare da ya juyo ba.
Kafin ya gama maganar har ta juya cikin sassarfa. Ganin yadda ta tashi hankalinta sai ya kasa komawa ciki ya fito zuwa ƙasa.
Tana ƙoƙarin tayar da motarta cikin damuwa ya ƙaraso. Ba ta lura da shi ba har sai da ya kira sunanta, ya tsaya saitin da take. "kashe motar." Ya ce mata ba tare daya haɗa idanu da ita ba.
Har za ta yi musu, sai ta fasa tana jin kamar ta yi mishi kuka. Ga mamaki sai ta ga ya ce,"Lemme drive you a halin da kike ciki ba za ki iya tuƙi ba."
"I can dri..." Maganar ta katse mata, sakamakon idanunsa da ya watsa mata. Kasa magana ta yi, sai ta fito kawai, saboda yadda idanunsa suka kashe mata jiki.
Motarsa ya nufa, bata da mafita ta bishi domin buƙatar ta kawai ta ƙwato yaranta a hannunsa.
Gaba ya shiga ta zauna a mai zaman baza. Cikin gwanancewa ya fara tuƙin suka bar harabar kampanin.
Fitarsu ya janyo cece-kuce a cikin ma'aikatan, wanda ɗaga hankalin Ingawa har ya kasa jurewa. Kiran waya ya shiga yi, amma ba ta ɗaga ba, daga bisani sai ta kashe wayar. Hakan ya saya shi cikin damuwa ƙwarai, yana ta safa da marwa a ofishinsa, tare da tunanin dalilin da yasa ya suka fita a tare.
A mota tuƙi yake yi da sauri, ganin yadda ta tayar da hankalinta, domin har hawaye ya ga tana sharewa. Ganin haka sai ya tsaya da motar ya jingina yana kallonta."Please ki bar kuka yaran naki ne dole za su dawo gareki." Yadda yayi maganar da taushin murya, ya sanya ta share hawayen tana kallon gefe sai kuma ta fashe da kuka.
Kukanta ya sanya zuciyarsa bugu sosai, da wani tsananin tausayinta ya fitar masa. Yana matuƙar tausayin macen mai saurin kuka, domin kukan shi ne hanyar da zai nuna tana cikin damuwa, sosai yake ɗaukar hawayen da matuƙar daraja, kuma zuciyarsa tana sarewa duk lokacin da ya ga mace na kuka don wani damuwa.
Tsoro ne ya kamata yadda ya koma lokaci guda. "Na daina." Ta ce masa kamar wata ƙaramar yarinya, tare da sanya gefen gyalenta ta share hawayen.
"Good!" Ya ce sannan suka fara tafiya.
Tana mushi kwatance ya kaita har kofar gida."Go and take your kids they are your belongings and you need to take care of them."
"Thank you for you concerned." Ya ce masa tare da fara tafiya zuwa cikin gida.
Yana gurin har ta buɗe ƙofar ta shiga sannan ya yi murmushi yana kallonta.Murmushi ya yi ganin yadda ta rikice yasan cewa in har ya aure ta ta haifa masa yara, za su samu kulawa sosai, ganin tana matuƙar son yara.
Jan motar ya yi cikin farinciki ya koma kampanin. Da ya koma sai ya tsinci kansa da kasa yin aiki yana son ya ji ko ta karɓo su, amma sai ya daure zuwa anjima sannan ya kira.