Sashe 79
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kusan awa biyu ya ɗauka yana bacci, har sai data leƙa sau biyu. Ganin har lokacin bacci yake yi, mai ƙarfi sai ta koma ta zauna bayan ta yi magariba.
A lokacin da ta idar, Marwana ta shigo cikin asibitin, da Muhsin riƙe da kulolin abinci. Kallon juna suka yi sai ta yi dariya ta ce,"Amarya."
Dariya suka ƙara yi sosai sannan ta zauna."I can't believe wai kin zama matar Ya Damir in simple way. Da ace Faruk ya san abin da zai faru kenan, in ya aikata wallahi ba zai yi ba."
"Sosai shi ya sa ake cewa mutum ya yi tunani kafin ya aikata abu. Ga shi ya yi sanadin aurenmu babu shiri."
"Haka ne wallahi, to ya batun amarci ina ba a asibiti za ku yi ba? Saboda yadda na ga yana wani kallonki, kar dai ki bada kai tun ba ki tare ba."
"Marwana, bana son rashin mutunci ni fa matar yayanki ne."
Dariya ta kwashe da shi sosai tana kallonta."To ni ma na kusa zama matar yayanki? Ko ba ji ance za a sanya mana rana sai a yi bikinmu da tarewarki ba."
"Na ji Allah ya sanya alkhari."
"Amin, amma ki bani amsar tambayar. Ina angon na ki yake."
"Yana can yana bacci, bawon Allah kanshi yake bani tsoro kamar ya ƙara tasawa."
"Karki damu zai warke, Faruk mugu ne sam ba shi da imani."
"Wallahi ai ya ga ƙarshen sa hauka."
Muhsin ne ya shiga sai ya fito.'Ya Damir ya tashi za ku iya shiga." Ya ce musu sannan ya koma ciki.
Ganbanta ne ya buga sosai, da ta tuna alƙawarin da ta yi masa. Sosai take jin kunyarsa, saboda ta iya zance a waya, amma a zahiri sai ta kasa.
Kanta a ƙasa ta yi sallama ta shigo. Ɓata fuska ya yi, domin ya ji haushi da Muhsin ya fara shigowa. Ya so ace ta cika masa alƙawarinsa.
Idanunsa na kanta, don haka ta ƙarasa cikin sanyin jiki ta zauna gefen Marwana."Sannu da jiki Ya Damir." Marwana ta ce tana kallonsa.
"Yauwa sis ina little Marwana?"
"Tana gida ganin ciwon da ka ji, ta yi ta kuka da tare za mu zo, amma sai ta fara zazzaɓi. Mommy ta bata magani bacci take yi na taho."
Murmushi ya yi, jin abin da ta ce tana kallon Nasreen, da ta yi shiru motsin kirki ta kasa.
"Anty Nasreen ga abinci, ki zuba wa Yaya. Hajiya ta ce ki lura sai ya ci sosai, saboda ba ya son cin abinci in ba shi da lafiya."
Harara ta zabga mata, don ta san da biyu ta kira ta da Anty kuma take maganar.
Kallonta ya yi, yana murmushi alamun ta ji abin da aka gaya mata.
Ɗauke kanta ta yi ba tare da ta amsa ba.
"Marwana zo mu je mu ba shi guri ya ci abinci."
Da sauri ya kalli Muhsin yana shi masa da albarka a zuciya, domin kamar ya san hakan yake so su yi.
Jin fita za su yi, sai ta takura tana kallonsu har suka fita. Tana jin Marwana ta ce,"Ki zuba masa abincin bari mu gaida marasa lafiya."
Ba tare da ta amsa ba ta, je inda aka aje kulolin ta ɗauki filet. Sannan ta zuba masa. Tun da suka fita ya bi ta da ido, amma ta ɗauke na ta, saboda kallon tuhuma da yake mata.
Bayan ta zuba sai ta tsinci kanta da kasa juyawa. Ɗaurewa ta yi ta juyo cikin sanyinta. Kamar yadda ta zarga, yana kallonta idanunsa suna kanta.
Kan gadon ta ƙarasa ta miƙa masa abincin ba tare da ta lalle shi ba. Ganin ta tsaya bai karɓi abincin ba sai ta kauda idanunta.
Ita yake kallo ganin ta kalle shi dai ya tura mata kumatunsa."My promised, I need deep kiss baby." Ya ce yana tura mata leɓensa.
Saura ƙafan abincin ya zube, ganin haka da sauri ya sanya hannu ya tare abincin yana kallonta."Mene ne haka sai ka ce na aikata zunubi za ki razana haka?"
"Kusan haka ya Damir. Don Allah ka bari na gama fita shaukin mamakin mun yi aure."
"Yes, we are spouse from now on, kuma duk abin da ma'aurata suke yi ya kamata ki yi mini. Ko ba kyau tausayina ne duk a kanki a fasa mini kai?" Ya ƙarashe maganar, cikin zallar shagwaɓa wanda ya sanya ta juyo a birkice.
"Dama namiji na shagwaɓa ne?" Ta yi wa kanta tambayar kanta na ƙara ƙullewa. Tun da aka ɗaura auren ya ƙara canzawa. Tun ranar da ya fara nuna mata ƙauna yake canzawa, ashe haka yake da rigima da haka. Lamarin sai ya yi mata bambaraƙwai, wai namiji da suna Hajara.
Ganin ta shiga cikin duniyar tunani, sai ya langaɓe kansa yana kallon ta. Shi kansa mamaki sosai yake yi yadda ya saki da ita. Ada yana shakkarta, amma tun da aka ɗaura auren sai ya ji duk wani kunya da shakkarta ya fice, wataƙila don shi ne bos, shi ne zai fara bayar da ƙofar da za su zamo ɗaya.
"Nasreen," Ya kira sunan a can ƙasar maƙoshi.
Juyowa ta yi cikin kunya ta kalle shi."Please fulfill the promise kin san babu kyau saɓa alƙawari ko?"
Kallonsa ta yi wani iri, tana mamakin rashin ta idonsa. Ta yaya zai kalli idanunta, ya ce ta yi masa kis a ranar da aka ɗaura aurensu. Wataƙila kuma don ya ganta bazawara ce dama ance basu da kunya. Ta yi tunanin hakan.
Ko ya fahimci abin da take tunani ne sai ya ga zaƙewarsa. "Ok tun da baza ki yi mini ba feed me." Ya ce mata tare da gyara zama ya buɗe baki.
"Ba Bukar ba Habu." Ta ce a zuciyarta domin hakan ba za ta iya ba.
Ganin ta ƙi sai ya yi fushi, ya juya mata baya ya kwanta. Ba ta san lokacin da dariya ya kubce mata ba."Please Ya Damir stand up and eat, you are no like little Marwana."
"Am more than her. Nasreen a gurinki tamkar ita ko jariri na ke. Har Batula ta mutu in ina gari tare muke ciyar da junanmu, and kuma da ga yau tun na Allah ya ƙara bani ke zan ci gaba."
"Nan fa a asibiti what if wani ya zo ya gammu? And besides that, su Marwana suna waje zan ji kunya sosai su shigo su ganmu. Don Allah eat don't starve yourself."
"Dole ki cire kunya sosai. Ki tambayi ƙawarki Marwana ganin idanu ba ya sanya na kasa nuna ma matata soyayya."
"Akwai rashin sabo don Allah eat zan yi watarana."
Juyowa ya yi, ya tashi zaune tare da karɓar abincin."I don't believe your promise, but lemme eat am starving to dead."
"Good," Ta ce tare da ije mishi a gabanshi. Yana cin abincin idanunsa na kanta, so yake kawai ya gansu tare, ya matsu ya ga ranar ya tashi daga gwauro da runguma filo.
Yana ci yana kallon ta cikin ƙauna har ya kammala. Tana ƙoƙarin kwashe kular Marwana ta shigo da Muhsin.
"Ya Damir su Maman Nasreen da Ya Ahmad ne suka zo."
"Ok, su shigo." Bayan ya gyara zamansa.
Mama da Ahmad suka shigo tare da sallama. Damir cikin jin kunya ya ɗaga idanunsa yana kallon ta. Sun yi kama da Nasreen sosai, domin ita ta biyo. Duk da ya taɓa ganinta, amma bazai shedata ba, domin a wancan lokacin ba shi a cikin hayyacinsa. Sosai yake jin kunyarta da girmamata. Tuna mugayen kalaman da ya rinƙa faɗi a gabanta.
Itama cikin kunya irin ta surukai suka gaisa. Ahmad ya ba shi hannu suka yi sallama. Cikin dakewa kamar sun saba suke hira.
Sun ɗan jima kaɗan, sannan suka miƙe za su tafi. Nasreen ce ta miƙe ta ce,"Ni ma bin ku zan yi Mama, gobe da safe zan dawo."
Jin abin da ta ce, ya watsa mata idanunsa yana son yin magana, amma kunyar Mama ya hana shi cewa komai.
"Na yi tunanin anan sa ki kwana har na zo miki da kaya?"
"A'a Muhsin zai kwana da shi. Da safe zan dawo." Ta faɗa ba tare data kalle shi.
Kallon Muhsin ya yi sai yayi matsa ya ce,"Nan za ki kwana, asibitin mai kyau ne akwai gurin kwanciya kamar zai fi buƙatar ki."
"Eto, tun da Mama ta kawo miki kaya ki kwana mana." Cewar Ahmad yana kallonta.
Kamar za ta yi kuka, ta koma ta zauna ba don ta so ba. Dariya ce ta so ta kubce masa, amma sai ya daure ya kauda kansa. Bayan sun tafi, tana zaune shiru ba tare data kalle shi ba, sai ta ji ya yi gyaran murya ya ce,"Yanzu za ki iya tafiya ki bar mijinki a wannan halin?"
Kallon sa kawai ta yi, don ta san rigima yake ji."Kamar kwanan Ya Muhsin zai fi amfani."
"Na gaya miki haka? Na fi so ki zauna a gefenta in ta kallonki."
Ba ta ce masa komai ba, don haka ya ɗauki wayarsa, yana dannawa wani lokacin yana kallonta.
A haka suka zauna har na tsawon lokaci. Ganin tana hamma, sai ya nuna mata gadon da yake kwance tare da miƙa masa hannu ya ce,"Come and spleep baby."
Kallon sa yi a birkice, sai kuma ta miƙe ta ɗauki kayan baccinta yi hanyar bayi tana faɗin,"Zan kwanta a wancan gadon."
Bai ce mata komai ba, don shi ma tsokanarta ya yi. Brush ta yi sannan ta canza kaya ta fito ta kwanta. Ganin ta kwanta shi ma ya kwanta tare da sauke nauyyayyar ajiyar zuciya, yana mamakin yau yana kwance ɗaki ɗaya da ita.
Ba su jima ba bacci mai nauyi ya ɗauke su. Nasreen bata tashi ba, har sai da ya farka jin kiran sallah. Miƙewa ya yi, yana girgiza kansa da ya ji ya rage nauyin da ya yi masa.
A hankali ya isa gareta, yana murmushi ganin yadda ta dunƙule a cikin hijabi. Jin ya taɓa ta sauri ta miƙe."Ki tashi ki yi sallah." Ya ce tare da shinfiɗa sallaya.
Miƙa ta yi mai haɗe da salati, sannan ta nufi bayi. Bayan ta yi alwala ta fito. Lokacin da ta fito yana Sallah don haka. Ta jira ya gama. Ɗaukar sallayar ta yi, zuwa gadon da ta kwana ta shinfiɗa.