← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 92

Sashe 82

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana saura kwana huɗu, aka kira mai lalli ta zo ta yi wa amare. Sun sha kyau iya kyau domin mai lallin ta iya sosai. Events kuwa tun ana saura kwana uku aka fara, duk da Nasreen ba ta so, ita da agonta, amma sun yi dole.

Amare ana ya gyara da shirin biki Allah ya ba da zaman lafiya.

Wasu mazan na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What

*WASU MAZAN*

BOOK 2

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 43

Damir sai zumuɗi yake yi sosai yake farinciki. Jin sa yake kamar bai taɓa aure ba, musamman yadda ya ga amaryarsa ta dawo. Ta yi kyau ta cika tamkar wata a cikin taurari. Annur ya same shi a ranar walima, yana dariya domin tafiya ya yi. Damir ganinsa ya ɗaure fuska.

"Haka za ka yi mini Damir? Daga tafiya sai ka lallaɓe ka aure mini wacce nake so?"

"Da ma ba gurin ka bane shishshigi ka yi." Ya ce masa yana harararsa.

Dariya ya yi yana faɗin,"To kuma mene ma jin haushi bayan ka cinye wasan?"

"Dama Nasreen tawa ce haɗin Allah ne ni da ita." Ya furta masa yana kallon sa.

"Haka ne domin saura kaɗan a kashe ni saboda kishi, duk da cewar har ga Allah a lokacin da na ganta sonta nake yi, amma bayan Marwana ta gaya mini komai, sai na ga kai kafin cancanta ka aure ta, don haka a rinƙa kunnaka har ka furta mata soyayya. Yanzu ina girman kai da aji?"

"Babu duk na manta ina da su, domin a gabanta kamar ƙaramin yaro na ke dawowa, sai na yi abin na yi ta mamakin kaina."

Dariya suka kwashe da shi sai ya kalle shi ya ce,"Ya kamata kayi mini kyauta gaskiya, domin ƙila sai wani ya ɗauke ta za ka farga."

"Kar ka damu, ɗanmu na farko sunanka zan sanya masa."

Jin abin da ya ce sai suka ƙara kwashe da dariya.

"Wato har an fara maganar yaro tun kafin a tare? Na san cewa Allah kaɗai zai ƙwace ta, a gurin wannan gwauron, saboda Damir duk a cikinmu yana son matarsa, kuma yana girmama aure da mata." Cewar Ibrahim yana dariya.

"Mata ai abin kula ne domin su ne tushen kowa. Shi ya sa na ke mamakin WASU MAZAN da suke wulaƙanta su." Cewar Annur. Dariya suka yi, suka ci gaba da tsokanarsa har suka tafi gurin walimar.

Ranar Juma'a aka ɗaura auren Marwana da Ahmad. Dubban mutane manya da masu kuɗi sun sheda, sannan aka ƙara gabatar da auren su Damir da aka ɗaura babu shiri.

Su Maman Muwaddat da Fadila, an sha biki duk da tana jego, duk sai da ta halacci events ɗin. Sosai ta yi farin ciki ganin yadda Damir yake nan-nan da ita, domin ko a gurin events ɗin tamkar zai mayar da ita cikinsa. Kunyar da ya ba ta kuwa yafi a ƙirga. Idanunsa na kanta duk inda ta juya.

Sun kasace cikin tsanannin farinciki sosai waɗannan ahalin, musamman ma'auratan. Damir da Ahmad ba ki har kunne suna karɓar baƙi cikin farinciki.

Nasreen tana zaune a cikin ɗakinta cikin lulluɓi. Kuka take yi sosai dangin Mama da ita suna mata nasiha. Sosai take yin kuka duk da ta sa halin Damir, amma sai zuciyarta take mata tunanin in har ya canza fa? Ji ta yi tsoro ya kamata har ta ji auren ya fita a ranta. Tunanin wane irin zama za su yi ya fi ɗaga mata hankali. Wani shashi na zuciyarta ya kore wannan tunanin, tare da ba ta shawarar ta yi tunanin zaman lafiya da zuriya mai ɗorawa. Sai kuma ta tuna ta rabu da yaranta kenan, dole su zauna a gidan Mama. Tausayinsu ya kamata. Ta rungume su tana kuka sosai, ganin su ma suna kukan za su bita. Zainab ta ɗauke su ta fita ɗakin da su. Rarrashinta suka yi suna bata baki har ta yi shiru.

Sosai suka yi mata nasiha, sannan aka sakata a mota sai gidan su Damir, wanda daga nan za a kaita gidanta.

Mommy rungume ta ta yi cikin tsanannin farinciki. Sosai take masa murnar samun mata kamarta, musamman da tun da suka fara soyayya ta canza shi ya dawo kamar da. Ya koma cikin farinciki da annashuwa.

Da ƙyar aka ɓamɓare amarya Marwana aka sanya ta a cikin mota, wacce take ihu tana kiran Mommy ganin da gaske za ta bar gidan.

A motar ita da Nasreen ce da a kayi shawarar ta rakata, don sai da ta shiga cikin motar sannan ta natsu ta yi shiru. A cikin motar hannunsu rungume da juna sai hawaye suke yi.

Da aka shiga Nasreen ta ji daɗin yadda danginta suke yabon gidan.

Dirama bai tashi ba sai da Nasreen ta mike za su tafi. Sai kawai ta saka kuka ta rungume ta ka cewar babu inda za su tafi.

"Nasreen don Allah kar ki tafi." Ta ce tare da ƙara riƙe ta saboda tsoron Ahmad ta fara ji.

"Kar ki manta wanda zan barki da shi kamar ni ne. Ya Ahmad ne ɗan'uwana ne kuma yana da tausayi."

Share hawayenta ta yi jin ta karfafa ta, sai ta kalle ta ta raɗa mata a kunni."Don Allah ki bawa Ya Damir kula sosai, kar kunyarki ta sanya ki cutar mini da shi. Kin san ya daɗe babu aure, kuma ina fatan ba ki ba da kai bori ya hau ba, saboda yau ne za ki samar wa kanki mutunci a ɗakinsa, kuma zai yi ɗokin ranar, amma in har kin amince da shi kafin tarewar babu wani ɗoki a tsakaninku."

"Ba ki da kunya yayarki ce ni."

"Or na manta, amma kuma ni ma haka yayarki ce." Dariya suka yi sai suka rungume juna.

"Allah ya bamu zaman lafiya da mazajenmu. Mun zama 'yan'uwa jini ɗaya. Ina fatan zumuncin mu ya ɗore har abada."

"In sha Allahu Anty Nasreen."

"Ina fatan haka Anty Marwana." Sai kawai suka ƙara kwashewa da dariya a tare.

Ganin ta sake ta yi mata sallama, sai suka tafi a barta ita da ƙawayenta da za su sayi baki.

Nasreen daga gidan Marwana aka wuce da ita gidan Damir. Gida ne mai kyau sosai, domin yadda ta ga cikin gidan a hoto har yafi kyau a zahiri.

Sosai gidan ya burgeta don ko ina ya yi mata. Ko a tarihin rayuwata ba ta taɓa tunanin zata zauna a irin sa ba, ko lokacin da Faruk ya aure ta gidan shi, gani ta yi ya wuce da zamanta, amma sai ga shi yau Allah ya ba ta gidan da ya fi shi kyau. Tabbas ta yarda da cewar raba bawa da arzikinsa mutuwarsa.

Bayan kowa ya tafi ta ƙara duba cikin gidan. Sama ne kawai bata hau ba, domin kamar a kulle yake.

Tana zaune zuciyarta na bugawa tana ƙaranto addu'a. Sosai take jin tsoron gidan da mai gidan. Lamarin da ya faru tun farkon haɗuwarsu ya dawo mata. Hawaye sosai take yi tana addu'a.

Ɓangaren su ango kuwa, bayan dare ya yi sun tabbatar da amare sun isa ɗakinsu, sai aka kama shirin zuwa gida.

Damir bai buƙaci kowa ba acewarsa shi ba yaro bane. Shi kaɗai zai sayi bakin amaryarsa da yake jin kamar ya yi tsuntsuwa. A ransa shi kaɗai ya san zumuɗin da yake ji.

Dariya sosai suke mishi ganin har yafi Ahmad sabon shiga ɗoki. Shi da Ahmad tamkar abokai, suka zama domin sun ije sarakutan a gefe.

Siyyayya Damir ya yi, sannan ya tafi zuwa gidansa. Wani iri ya ji tuna rayuwar da suka yi da Batula, har sai da hawaye suka wanke masa fuska, amma sai ya gode wa Allah tun da Ubangiji yaba shi mace ta gari, kuma wacce a yanzu yake jin in har babu ita rayuwar sa sai a hankali.

Nasreen na zaune da carbi a hannunta tana ja, don har yanzu zuciyarta bugawa take yi da ƙarfi.

Bugun zuciyarta ya ƙaru, daidai da ji an buɗe get ya shigo da motarsa. A hankali ta yaye labulen windon tana kallonsa, daidai lokacin da ya fito suna gaisawa da maigadi.

Ƙoƙarin saita natsuwarta ta yi, jin alamun tafiya yana ƙoƙarin buɗe ƙofa. Bugun zuciyarta ya ƙaru, ganin ya buɗe kofar shigowa falo da sallama.

Cikin murya ƙasa-kasa ta amsa masa kanta na duƙe, saboda bata tunanin ya ji amsawar da ta yi.

Ya ɗan yi Jimm yana kallonta, zuciyarta cunkushe da ƙaunarta. Tsawon lokaci wata ɗaya da Mommy ta sanya yau ga shi ga matarsa a gida ɗaya. Daga shi sai ita, sai kuma iskan Ubangiji da yake kaɗawa, yana saukar musu da farinciki a wannan ranar.

A hankali ya ƙaraso ya zauna a gefenta. Ajiyar numfashi ta sauke jin ya kira sunanta. Sai ta rasa abin da za ta je masa.

Ganin ta yi shiru, sai ya ja gyalenta tare da duƙawa yana kallon fuskarta, murmushi ɗauke a fuskarsa.

"Sannu da shigowa." Ta ce masa kamar wacce aka yi wa dole

"Nasreen," Ya kira sunanta cikin shaƙaƙƙiyar murya, domin turarenta ya fara rikita shi.

Cikin jin kunya ta amsa da."Na'am," Ba tare da ta ɗaga idanunta ta kalle shi ba.

"Please look in to my eyes." Ya ce mata yana kallon fuskarta.

Jarumta ta yi, ta ɗaga idanunta don ta kalle shi, amma da sauri ta mayar da idanunta ƙasa, saboda abin da ta gani a idanunsa sun rikitata.

"Nasreen ina son ki. Wane irin tarba zan samu yau?"

Mamaki sosai ya kama shi lokaci da ya ga hawaye a fuskarta. Lokaci guda ya firgita ya fara tambayarta.

Tunawa ta yi ranar amarcinsa irin yada ya tafi.
Chapter 82 · 0% Book details