Sashe 22
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na kaiki asibiti kin bani ijiyar kuɗin ne? Ai ba kya tausaya wa kanki, tun da na kawo miki mafita, amma kika kunnen uwar shegu da maganata tare da shafawa idanunki toka. Da ace kin sha maganin ai da duk hakan ba ta faru ba, muna nan muna cin amrcinmu."
Ta kasa ce masa komai sai kaƙarin amai take yi.
"Zubar da cikin nan za a yi, don ba za ki rinƙa mini ƙazanta a cikin gidana ba." Ya ce tare da komawa ya kwanta yana jin kamar ya shaƙeta.
"Ni kuma wallahi ba zan zubar ba, saboda ban sani ba, ko shi kadai ne rabona a duniya."
"To sai me? Mata nawa suke rayuwa ba tare da sun haihu ba?"
Ba ta tanka masa ba, ta koma ta zauna tana jin yadda cikinta ke juyawa.
Da sassafe ya fice gidan ba tare da ya kula da halin da take ciki ba.
Kwanciya ta yi domin ba za ta iya zuwa makaranta ba.
Fadila ta kira ta sanya mata attendance.
Tana kwance har zuwa sha biyu, sannan ta samu zazzabin ya sauka. Miƙewa ta yi don ta nemi abincin da za ta ci.
Shinkafa ta dafa da mai da yaji ta ci. Tana zaune tana kallo a falo ta ji alamun shigowar motarsu ya dawo.
Ya shigo babu sallama ya samu gefenta ya zauna."Sannu da dawowa."
Wata uwar harara ya jefa mata wanda ya ba ta dariya.
"Tashi ki kawo mini ruwa " Ya faɗa fuskarsa a ɗaure.
Miƙewa ta yi ta ibo masa ruwan."Saboda iskanci a tsaye za ki bani don ki tabbatar mini da ba a gidan tarbiya na auri ki ba?"
Ƙasa magana ta yi saboda miyau da ya taru a bakinta. Burinta ya karɓa ta je ta zubar.
Miƙewa cikin zafi wanda ya santa ta razana za ta matsa. Cikin rashin sama ruwan ya zube masa a jiki.
Mari masu kyau guda biyu ya wanka mata, wanda ya sanya ta haɗiye miyau babu shiri.
"Saboda kin raina ni za ki zuba mini ruwa a jiki? Wawiya mara tunani." Ya ce tare da ficewa daga gidan.
Nasreen da wani irin hajjiiya ya kamata. Daina gani ta yi na wuccin gadi. Ji ta yi ta faɗi ƙasa saboda rashin ƙarfin jikinta. Sai kawai ta fashe da kuka.
Miyau da ta haɗiye bisa dole ya hautsina kayan cikinta.
Wani irin amai ya turniƙota wanda ya sa ta ruga cikin bayi, amma ba ta ƙara ba ta shiga kwaro shi.
Tana kuka tana amai ji take yi gara mutuwa da auren.
Fadila da take ta sallama ta ji ba'a amsa mata ba, ya sa ta shigo har cikin falon. Ganin babu motarsu a cikin gidan. Jin kakarin amai ya sanya ta shiga cikin ɗakin a razane.
"Subuhanallahi! Nasreen jikin ne?"
Ganinta ya sanya ta miƙe tare da share bakinta ta faɗa jikinta tana kuka.
"Gaskiya Faruk ba shi da imani. Kina cikin wannan halin ya iya tsallake wa ya bar gidan nan?" Ta ce tana kallonta.
"Nasreen, lafiya mai ya samu fuskarki haka?"
Farouk ne." Ta faɗa cikin tsananin kuka.
"Kina nufin faruk ya mare ki?"
"Eh, saboda na zuba masa ruwa a jiki bisa kuskure."
"Ruwa wuta ne? Anya akwai ɗigon imani a zuciyarsa?"
Kuka take yi ba tare da ta ce komai ba.
"Gaskiya ba ki dace miji ba. Ga shi ciki ne dake zaman aurenki zai ɗore kuwa?"
"Ya ce na zubar da cikin ba ya son haihuwa, ni kuma ba zan iya kisa ba, kuma ina son na ga ɗan cikina." Ta ce mata cikin rawar murya.
Tsananin tausayinta ya kamata musamman yadda ta yi maganar."Sam ba shi da ɗigon imani a cikin zuciyarsa. Ki yi haƙuri ki yi addu'a Ubangiya ya kawo miki ɗauki."
Kamata ta yi ta kwantar da ita. Ganin yadda take rawar sanyi ya sanya ta lulluɓa mata bargo.
Fara gyara gidan ta yi ganin duk ya yi ƙura. Bayan ta gama gyara gidan ta dawo kusa da ita.
"Za ki iya cin wani abu na girka miki?"
"Wainar fulawa na ke so na ci tun jiya, amma na san ko na yi masa magana, ba zai siya mini fulawar ba, kuma kuɗin da Ya Ahmad ya bani sun kusa ƙare wa."
"To bari na fita na je bakin titi na sayi fulawar." Ta ce mata tare da miƙewa ta ɗauki mayafinta.
Tana tafe tana tunani tare da fargabar aure. Sosai halin Faruk ya tsorata ta, ganin yadda yake cutar da ita.
Gwangwani uku ta siya, sannan ta yi cefane da yajin da za ta daka mata.
Bayan ta dawo ta kwaɓa fulawar ta fara soyawa. A lokacin da ta kawo mata tana kwance. Taimaka mata ta yi ta mike sannan ta ije mata filet ɗin.
"Na gode Ubangiji ya biya ki." Ta furta hawaye na bin fuskarta.
Sai da ta cinye wainar tas! Sannan ta koma ta kwanta.
Fadila na wanke kayan da ta ɓata ta ji shigowar motarsa. A ranta ta ɗauki aniyar yi masa magana. Yana shigowa falon ta fito, daidai lokacin da ya fara kiran sunan Nasreen.
"Ba ta da lafiya ba za ta iya fitowa ba." Ta furta masa daidai lokacin da ta fito daga kicin ɗin.
Kallon banza ya watsa mata, ba tare da ya tanka mata na zai wuce.
"Faruk, ina son magana da kai." Ta furta masa haka.
Kamar ba zai juyo na sai kuma ya tsaya yana kallonta a wulaƙance."Nasreen, ba ta gaya miki ki daina zuwa gidan nan ba? Domin ina zargin harda sanya hannunki, gurin hure mata kunne ta daina yi mini biyayya."
"Ka ji tsoron Allah, ka daina cutar da rayuwarta. Nasreen, mata ce a gurinka ba baiwa ba, amma..."
"Ke dakata!" Ya katse ta da sauri yana faɗin haka.
"Har gidana za ki biyo ni kina gaya mini maganar banza? Matata ce ita, kuma ba ki isa ki gaya mini yadda zan zauna da ita ba. Don haka, kar ki ƙara kuskuren sanya bakinki a lamarin aurenmu."
Kalamansa su ka yi matuƙar ba ta mamaki."Faruk, ni...."
"Get out of my house!" Ya furta da ƙarfi cikin ɓacin rai.
"Gidan banza na ka, in sha Allahu ba zan ƙara shigowa."
"Ki shigo ki ga yadda zan karya ƙasusuwan jikinki." Ya furta mata yana kallonta.
Harararsa ta yi, tare da sakin tsaki ta shiga cikin ɗakin don ta ɗauko jakarta.
Nasreen kuka take yi cikin tashin hankali. Tun da ya shigo ta zauna kan gadon, duk da azababben ciwon kan dake damunta. Tsoron ta kar ya wulaƙanta Fadila, sai kuma ga shi bai shanye raɗa ba.
"Nasreen, ki yi haƙuri bisa jarrbawar da Allah ya yi miki, domin mijinki bai san darajar mace ba. Allah yana tare dake."
Hannunta ta riƙe, amma sai ta fisge ta fice gidan cikin kuka, tana tausayin halin da ƙawarta take ciki.
"Zama kika yi kina gaya mata ina cutar dake ko?" Ya yi mata tambayar yana matsowa kusa da ita.
"A'a, wallahi ban gaya mata ba." Ta furta cikin muryar kuka tana matsawa.
"To, uban mai yasa ta tsareni tana gaya mini maganar banza?"
"Ka yi haƙuri ni ma ban sani ba, kuma zan yi mata magana."
"Kar ki yi mata Allah ya sa ta ƙara mini rainin wayo. Wallahi saina karya ƙafarta, sai na ga yadda za ta ƙara shigowa cikin gidana ta yi mini rashin kunya. Ki ma godewa Allah kin samu miji, ita fa ga shi nan babu mashinshini sai yawo a gidajen ƙawaye take yi."
Shiru ta yi ta kasa ce masa komai, domin ba ta da abin da za ta ce.
"Tashi ki dafa mini abinci." Ya furta tare da zama kan gadon.
Da sauri ta ɗago kanta tana kallonsa jin abin da ya ce, don ko makaho ya kalle ta ya san ba ta da lafiya, ballantana shi da idanunsa biyu suke ras!
"Ba ni da lafiya, ba zan iya ba."
Kallon da ya yi mata ya sa ta mike babu shiri, sai kuma jiri ya ibeta za ta faɗi.
"Ka tausaya mini ba zan iya tsayuwar ba."
"Kin san Allah ko suma kike sai kin yi mini abinci. Ai ban aike ki ba, in da kina jin maganata, da ba ki ɗaurawa kanki wahala ba."
Sau uku tana ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa, sai a na huɗu ta yi nasarar miƙewa.
"Kuma kika sake kika yi mini ƙazantar da kika tsira, wallahi sai kin raina kanki." Ya ce tare da fitowa ɗakin ya shige ɗauki sa.
Kicin ta nufa ta wanke kayan miyan, domin shinkafa da miya yake son ciki. Tana girkin tana kwanciya a ƙasa tayas ɗin, har ta samu ta gama, sannan ta sanya masa a kula ta kai masa.
Tana gamawa ta fito daki ta kwanta sai nishi take yi. Ba tare da ya damu da halin da take ciki ba, ya cika cikinsa sannan ya fice daga cikin gidan.
Nasreen tana kwance kan kujerar tana kuka. Ganin za ta mutu ta ɗauki wayarta ta kira Ahmad.
"Hello Ya Ahmad, ba ni da lafiya zan mutu." Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka tana nishi da ƙyar.
"Nasreen, da na ba ki da lafiya ne?" Ya yi mata tambayar cikin damuwa.
"Kwana biyu ina zazzaɓi kuma jikina babu ƙarfi."
"Ina Faruk ɗin, ya san ba ki da lafiya?" Ya yi mata tamabayar jin abin da ta ce.
"Eh, ya sani amma ya ce ba zai kai ni asibiti ba."
"Ok, gani nan zuwa gidan." Ya furta cikin ɓacin rai yana huci.
"Lafiya mai kuma ya same ta?" Mama ta dake gefensa tana cin dambu ta yi masa tambayar.
"Nasreen ba da lafiya kuma yaƙi kaita asibiti."
"Kai wannan yaro sam ba ya kyautata rayuwarsa. Ace tun da aka yi aure, matsalar yau daban ta gobe daban." Ta yi maganar cikin takaici.
"Bari na je na ga halin da take ciki."
"Don Allah Ahmad, karka kula shi ku raba abin faɗa."
"To Mama, zan je na kai ta kyamis, in kuma ya wuce kyamis sai mu je asibiti, amma in har ya yi mini hauka, ba zan lamunta ba, domin mutumin nan sam ba shi da hankali."
"Ka yi haƙuri ya ci darajar 'yar'uwarka."
Ba tare da ya ce mata komai ba ya fice daga cikin gidan.
Mashin ɗin da ya hau ya buga sai gidan.