Sashe 18
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ki tashi ki haɗa mana breakfast."
Jikinta na ɓari ta miƙe ganin yadda ya ci magani.
Kallon kayan take cike da maimakinsa. A yadda yake da wadata mai kamata ace ya fito wadannan kayan ba.
Sai ta yi masa uxuri, domin ba ta son ƙara sanya kanta cikin damuwa.
Haɗa komai ta yi ta kawo masa da yake zaune a falo yana kallo.
Jawo ta ya yi ta zauna kusa da shi.
"Mu karya." Ya ce mata wanda babu musu ta zauna a gefensa.
Cikin jin kunya take juya ruwan tea din, tana kallonsa da yake ta aika ma cikinsa, don har ya kusa cinye ƙwan.
Sai da ya ci abinci da sosai, sannan ya ture ya ci gaba da kallo, ba tare da ya kula ta ba da take ta juya cokali
Yunwa take ji sosai amma bakinta babu daɗi. Haka nan ta daure ta sha ruwan tea sannan ta cinye ɗan ragowar ƙwann ya rage mata.
Miƙewa ta yi ta kai kayan kicin tare da ƙara gyara gurin. Bacci take ji sosai domin da kyar take buɗe idanunta.Kama hanyar ɗaki ta yi tana hamma.
"Nasreen," Ya kira sunanta.
Dawowa ta yi ta zauna a can nesa da shi.
"Ina da wasu dokoki da zan kafa miki a gidan nan, wanda matuƙar kika kiyaye su, to ba za mu rinƙa samun matsala ba, amma kin ga in kika yi kunnen uwar shegu da su. Tsakanina da ke babu sausauci.
Jin kalamansa ya sanya ta yi shiru, ta kasa cewa komai, sai wasa take da yatsun hannayenta.
"Na farko ni mutum ne mai tsananin tsafta. Sam ba na son ƙazanta in kika zama mai tsafta, ba za ki samu matsala da ni ta wannan ba. Sannan na biyu kuma ba na son mutane, saboda yadda na kashe maƙudan kuɗi, ba zan bari ko wane banza ya shigo mini gida ya ɓata ba, saboda haka, sai ki kiyaye waɗanda za su shigo mini gida. Kayan abinci kuma gwada miki zan rinƙa yi, don ku amaren zamanin nan, sam ba ku san yadda kayan masarufi suka yi tashin Gwauron zabi ba. A takaice ba na son albazaranci. Sannan kin sanni bana son ƙawayenki su rinƙa zuwa gidan nan, ko Fadila ban lamunta ta rinƙa mini safa da marwa a cikin gidana ba."
Da sauri ta kalle shi jin abin da ya ce tana mamakinsa.
"Na ga kin ɗago da sauri, Fadila tare aka haife ku?"
Ba ta amsa ba sai ta ɗauke idanunta kawai. Ganin ba ta ce komai ba ya ɗaura da cewa.
"So na ke na huta in har ba gara aka kawo mini ba, kar ki sake ki buɗe wa kowa gida."
Jin abin da ya ce ya sanya ta daina mamakinsa don ya zarce tunaninta.
"Ki na jina kin yi shiru?"
"Zan kiyaye." Ta furta tare da fara tafiya.
Ɗaki ta shiga ta kwanta cikin damuwa. Baccin da take ji ta nema ta rasa..Kwanciya rub da ciki ta yi tana hawaye.
Tana kwance ta ji ya tura ƙofar ya shigo. Gabanta ne ya faɗi da sauri ta juyo tana kallon sa.
"Bacci ya kamata mu yi kin san ya kamata mu huta lokacin amarcinsu." Ya furta tare da kwanciya a gadon ya ja bargo ya rufe su.
Nasreen sai ta ji ta takura damuwa ta yi mata yawa. Ga tsanarsa ga takura ta da ya yi. Ji ta yi sam amarcin na su ba ya mata daɗi.
Ta ɗauka wasa yake mata kan maganar babu wanda zai shigo. Sai ta ga ashe da gaske yake. Haka aka rinƙa dukan ƙofar, amma ya hana ta ta je ta buɗe.
Wayarta da ke kan mirror ta yi ƙara alamun ana kira. Da sauri ta kai hannu za ta ɗauka.
Hannunsa ya sanya ya hana ta."Ƙila wadanda suke buga ƙofar ne suka kira. Kar ki ɗauki wayar, saboda babu wanda ya isa ya hana ni cin amarci. Jarabbabu kawai mutum da aure su da nacin zuwa ganin amarya."
"Zan duba ne watakila Anty Maryam ce, saboda ta ce in suka dawo kasuwa za su zo." Ta ce masa cikin rawar murya tana son yin kuka.
Ƙaramin tsaki ya ja yana kallonta." Ok, ki duba su ɗin ma ban yi maraba da zuwan su ba, don na san ba abin arziki za su kawo ba."
Ba ta ce masa komai ba ta duba wayar cikin damuwa."Su ne." Ta ce masa tana kallon sa.
Tsaki ya yi tare da sauka a kan gadon ya wuce ɗakinsa.
Ganin haka ya sanya ta sauko ta je ta buɗe musu.
Anty Maryam da Binta babbar ƴaƴansu su. Ganin su ya sanya ta faɗa jikinsu tare da saka kuka.
"To kuma mene abin kuka daga zuwanmu."
"Ba na jin daɗin zaman gidan ina son na koma gida."
Dariya suka yi jin abin da ta ce."Allah Sarki! Kowa da haka ya fara dole ki jure." Cewar Binta tana kallon su.
"Ga shi in ji Mama, da ƙyar ta samu ta yi miki wannan siyayyyar, wannan kuma cincin da dibilan ne aka yi miki sai ki iba ki ce ya kai ma danginsa.."
"To,"
Ba ta ji daɗin kawo wa ba, don ta san wanda aka yi don shi ba yabawa zai yi ba.
Yana jin maganar su amma ya ƙi tasowa su gaisa.
"Kamar na ga motar mijin ki na nan?"
"Eh,"Ta furta cikin jin kunya.
"Amma shi ne ya ƙi zuwa mu gaisa?"
"Bacci ya ke yi." Ta tsinci kanta da yi musu wannan ƙaryar.
"Ko idanunsa biyu da wuya ya zo, saboda ya raina ƙurarmu. Nasreen, sai kin haƙuri da mijin da Allah ya ba ki, sannan ku dage da addu'a."
Kuka ta fashe musu da shi. Da ma mai shirin kuka ne aka jefe shi da kashin awaki.
Rarrashinta suka shiga yi sannan suka yi mata sallama suka tafi.
Yana jin sun fita ya buɗe ƙofar ɗakinsa ya fito.
Kallonsa ta yi cikin jin kunya lokacin da ya ƙara so daga da ita ya zauna.
"Abin da suka kawo kenan?"
Ta kasa ce masa komai wanda hakan ya sanya ya ja tsuka ya miƙe.
"Yunwa na ke ji ki je ki yi mana abinci. Allah ya sa kin iya saboda na ji ƙwan da kika dafa ya yi gishiri da yawa." Ba tare da ya kalleta ba yake faɗin haka, bayan ya ɗauki remote yana canza tasha.
Kicin ɗin ta shiga tana tunanin abin da za ta yi. Babu abin da za ta iya girkawa wanda ya wuce shinkafa da taliya, domin su kaɗai ne a cikin gidan.
Shinkafa da taliya ta haɗa ta yi jalop sannan ta shirya abincin a ciki kula ta kai masa. Ta yi tunanin zai yi ƙoƙarin, amma sai bai ce komai ba. Ya dai ci abincin fuskarsa babu yabo, babu fallasa.
Bayan ya gama cin abincin ya yi wanka ya fita daga gidan.
Sai a lokacin ta samu ta sake a cikin gidan. Ɗaki ta koma ta zauna tare da ɗaukar wayarta, tana duba waɗanda suka kirata.
Ganin numbar Fadila ya sanya ba ta ji ba daɗi ba. Tana ƙoƙarin kira sai ga kiranta ya shigo.
"Amarya ba kyau laifi."
Murmushin yaƙe ta yi mata kamar tana ganinta.
"Mun zo da sauran ƙawayenmu, amma mun yi bugun duniyar an, ba ku zo kin buɗe ba."
Ƙasa ce mata komai ta yi, domin ba ta san mai za ta ce mata ta yarda ba.
"Hala ba ku yi bacci ba jiya cin amarci ya hana?" Ta yi mata tambayar cikin zolaya.
Jin ta yi shiru ya sanya ta ce,"Gobe zan zo ni kaɗai tun da sun tafi. Ki aje mini dibilan da cincin."
"To, sai kin zo." Ta yi mata sallama tare da kashe wayar.
Farouk bai dawo gidan ba sai, bayan kiran sallar isha. A lokacin ta yi wanka, tana kwance kan doguwar kujera da wayarta tana karatu.
Jin ƙarar motarsu ya sanya zuciyarta bugawa, saboda tsoransa take yi sosai. Ji take yi kamar karya dawo gidan, don takurar da yake mata.
Jin yana magana da mutane maza a waje. Ta gane ba shi kaɗai bane. Da sauri ta tashi ta shiga cikin ɗauki, ta sanya hijabinta.
Ya shigo da kaya niki-niƙi a hannunsa ga kuma sauran abokan nan su ma ɗauke da kayan. Mamakin soyayyar da ya yi ta yi, ɗin ba ta yi tunanin zai siya komai ba. A maimakon ta ga ya zuba a store, sai ta ga ya shirya cikin ɗakinta da su.
"Sannun ku da zuwa." Ta ce tana tsaye.
"Amarya ba kyau laifi." Suka haɗa baki gurin faɗin haka.
Murmushin ta yi sannan ta gaishe su cincin da dibaln ta kawo musu.
Farouk ya ibo musu drinks ya kawo musu.
Ɗaki ta wuce takwanta tana jin suna hira har ƙarfe goma da rabi, sannan suka yi musu sallama suka tafi.
_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 10
Ɗaki ta wuce takwanta, tana jin suna hira har ƙarfe goma da rabi, sannan suka yi musu sallama suka tafi.
Tafiyarsu ya sanya ta ji babu daɗi. Ta so ace su yi zamansu har gari ya waye.
Tana kwance ya shigo cikin ɗakin bayan ya gama kulle ƙofar gidan. Kallon ta ya yi, tare da zama gefen ganin ya ja tsuka.
"Yanzu abin da kika yi wayewa ce, a matsayin ki na mace 'yar boko?"
"Tana son ta tambaye sa abin da ta yi, amma kuma ta kasa, tun da ba ta san laifin da ta yi masa ba."