← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 92

Sashe 58

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Annur kuwa duk ya susuce domin sai ya ga kamar ta canza a ranar da ya ganta. Ganin yadda ta yi kyau sai ya ji kamar a ɗaura auren. Sun fahimci juna sosai tare da musayar numba. Nasreen ta ji ya kwanta mata sosai. Kasancewar haɗuwar farko ce ba su jima ba ya tafi.

Shiryen-shiryen komawa aiki take yi, da saboda Mama da ta takura mata. Duk wani shiri ta yi jira take Monday ya yi.

Farouk kuwa hauka tuburan ya yi saboda in ya tuna kuɗinsa, sai ya ji gara ya dawwama a cikin haukar. Sai dai nacewar da danginsa suka yi da magani Allah ya ba shi lafiya, domin a sanadin ciwon mahaifiyarsa sai da ta zo Nigeria. Tun da ya warke ba shi da aiki sai kuka ya ƙi cin abinci duk irin rarrashin da suke masa. Yana warkewa aka zo da motar 'yan sanda kan maganar kuɗin gidan da aka shi. Da ƙyar aka samu aka biya kuɗin don sai da aka sayar da gidansa da ya fara gini, sannan mahaifiyarsa ta cika sauran. Ya rage ba shi da wata ƙaddara da ga gidan da yake ciki sai kuma motarshi da aikin yi.

Duk lokacin da ya tuna, ya rasa maƙudan kuɗin da ya ɗauki tsawon shekaru yana tarawa ba tare da ya ci ba, sai ya ji kamar haukar za ta dawo sabo. Ganin dai an neme ta wa ƙaura da wambai, amma ba a samu ta ba, sai dangana, amma ba don ya haƙura ba.

Gabakiɗaya ya rame, ya fita hayyacinsa ko aiki sai da mahaifiyarsa ta yi masa da gaske ya fara zuwa.

Yana zaune a cikin ɗakinsa ya tasa ruwan Lipton yana kallo, wai yau shi ne zai sha ruwan bunu, saboda ba su yi albashi ba. Tun bayan da lamarin ya faru, da ƙyar yake iya kai abinci bakinsa, don shi ma an yi masa dole, da kuma yunwar da ta kusa kaishi lahira.

Kallon gidan ya yi cikin ƙuna yana tuna rayuwar da ya yi da Rashida. Rintse idanunsa ya yi cikin takaici ashe makashinsa ya rinƙa kiwatawa yana bata abinci. A ransa ji yake da ace zai ganta babu abin da zai hana bai kashe ta ba. Ya yi kuka har hawayen sun daina fitowa, musamman inya duba duk bankinsa ba shi da komai dai kuɗin albashi da yake jira, wannan lamari yana sanya duniyarsa ƙuntata.

Yana kwance kan dogon kujerar idanunsa rufe yana hawaye. Zuciyarsa ta tuno masa da Nasreen. Saboda tsananin razana har sai da ya miƙe, saboda yadda zuciyarsa ta buga da karfi. Tun bayan da suka rabu bai ƙara tunainta ko da na sakan ba, ballanatana ya tuna yaransa da suke gurinta.

Zaman da suka yi, abin da rinƙa dawo masa kamar yanzu yake faruwa. Rintse idanunsa ya yi cikin tsanannin tashin hankali yana tuna rayuwar da suka yi. Ga mamakinsa sai ya ji hawaye lokaci guda wani irin nadama ya fara shigarsa, tare da sonta mai tsananin. Sosai yake nadamar rayuwar da suke yi, musamman abubuwan da ya yi mata na ƙuntatawa."Ko yanzu tana ina?" Ya yi wa kasa tamabayar cikin tsananin tsoro. Ya san dai tana gidansu domin a yadda ta ke cewa ta tsani aure ba za ta yi aure da wuri ba. Ya dan har yanzu tana nan a cikin ƙangin talauci, saboda service ba zai canza rayuwar talaucin da suke ciki ba.

Tashi ya yi yana zagaye falon yayin da zuciyarsa take ba shi shawarar ya je ya samu Baba kawai ya lallaɓo shi da kuɗi ya dawo da ita, domin a yanzu ya fahimci Nasreen ita ne kawai da za ta iya jure halinsa.

Kamar an tsiƙare shi, ya miƙe domin a zuciyarsa ya yi na'am da shawarar da ta ba shi. Ya san Nasreen tana da haƙuri, duk da cewar ta fara canzawa kafin su rabu, amma in ya bawa Baba kuɗi ya kuma roƙe ta, saboda talauci da su Raihann Baba na yi mata dole za ta dawo, don haka bai yi kasa a gwiwa ba, ya shiga ciki tare da fesa wanka, duk da ya rame, amma yana nan a Faruk dinsa ɗan kwalisa da isa.

Sai da ya gama wanka ya shiga motarsa zuwa biko, amma sai ya tayar da motar ta ƙi tashi. Tunawa ya yi da mai ya ƙare ya sanya shi sakin tsuka cikin takaici. Ga shi ba shi da ko sisi, domin ko abincin da zai ci kafin ƙarshen wata sai ya ranta. Kan dole ya kashe motar ya fito ya bar zuwa bikon sai an yi albashi.

A ranar da ta kasance Monday za ta je aiki. Tun safe ta tashi ta sanya musu ruwan wanka. Wanka ta yi bayan ta gama azkar ɗin ta. A yanzu suna da mai aikin da take share-share a gidan.

Zama ta yi ta bata lokacinta gurin gyara jikinta, amma ba ta yi heavy make up ba sai ta yi light. Bayan ta ta ma ta ɗauki abayarta sabuwa ta sanya sannan ta yi rolling gyalen abayar. Sabuwar wayarta ta ɗauka da key ɗin motarta ta fice.

A falo ta samu Baba da ya zauna a gaban tibi yana kallo kamar zai shige ciki. Gaishe shi ta yi sannan ta wuce ɗakin Mama. Tana zaune da carbi a hannunta.

"Ina kwana Mama?"

"Lafiya lau kin shirya?"

"Eh, zan wuce."

"Shikenan sai kin dawo Allah ya yi miki albarka. Don Allah ki haƙuri da halin Damir, ki rinƙa kauda idanunki kin ga mahaifiyar sa da kanta ta zo ta bada haƙuri."

"Mama, babu ruwan da shi amma wallahi ba zan ɗauki rashin mutunci da ba, saboda na lura in har ba cire tsoronsa na ke yi na nuna masa ba ya tsorata ni ba zai barni na zauna lafiya ba."

"Don Allah kar ki yi masa rashin kunya duk abin da yake yi, ganin sanadin taimakon ki hakan ya faru."

"Amma ban yi masa dole ya taimake ni ba, sai yanzu nake takaicin jininsa da yake yawo a jikina, saboda sam ba shi da tausayi da tafiya."

Mamakin abin da ta ce ta yi kafin ta yi magana ta fice tana cewa,"Mama, na tafi kafin na yi latti jarabbaben ya samu abin mini rashin mutunci." Kasa amsawa ta yi ganin kodayaushe gogewa take tana rage tsoro.

Ɗakin Ahmad ta shiga yana kwance da waya a hannunsa."Yayana na shirya zan wuce." Ta shi ya yi ya zauna yana kallonta.

"Kin ga yadda kika yi kyau? Sai kin dawo kar ki sake wani ta raina mini ke."

Dariya ta yi ta ce,Babu shi yanzu a duniyar nan tun da ina da kai."

"Drive safe sis." Amsawa ta yi sannan ta fice.

Da bismillah ta shiga motar ta tayar a hankali take tuƙi har ta isa get ɗin shiga kampanin. Wani abin mamaki duk tsoro da bugun zuciya babu. Hankalinta a kwance maigadi ya buɗe mata. Tana ƙoƙarin shiga motar Damir ta sanyo kai sai kuma Hajar da take bayansa.

Kallon motar ta yi, ba tare da ta ji komai ba ta shiga ciki. Ita ta fara yin parking sai shi ya wuce inda yake ije motarsa, Hajar ta yi parking kusa da ita.

A hankali ta buɗe motar ta ɗauki wayarta da jakarta. Hajar ce ta rugo da sauri ta rungumeta. "Nasreen jin ya kika yi ko kin je canza halittar ki ne?" Ta yi mata tamabayar cikin tsananin mamakin yadda ta koma.

Damir da yake ƙoƙarin rufe motarsa, yana jin ance Nasreen da sauri ya kalli gurin zuciyarsa na bugu. Cire idanunsa ya yi cikin mamaki yana tunanin ita ce ko gizo idanunsa suke masa, amma kuma sunanta da aka kira ya gaskata masa da ita ce. Mamaki sosai ya kama shi ganin yadda ta yi kyau ta canza kamar ba ita ba. Da sauri ya rufe kofar da ƙarfi har sai da suka waiwaiya suna kallonsa

"Kin ga ganinki ya mantar da ni Ya Damir ya shigo. Mu je mu gashe sa." Ta ƙarashe maganar tare da kama hannun ta da nufin su ƙarasa inda yake.

Zare hannunta ta yi, tare da nuna mata alamar ba za je ba. Hajar ta buɗe baki za ta yi magana, sai ta ga ya fara tafiya zai wuce, kuma dole ta inda suke zai biyo.

"Ina kwana Ya Damir." Suka haɗa baki a tare gurin faɗin haka.

Da sauri ya juyo, jin muryarta rangaɗaɗau babu alamun tsoro ko rawar muryar da take yi ada, saboda muryarta har ta fi na Hajar. Kasa amsawa ya yi, sai kawai ya yi motsi da bakinsa tare da ƙara saurin tafiyarsa. Hajar ta bishi da kallo ganin mood ɗinsa, ita kuwa ƙaramin tsaki taja tare da sakin yar dariya yadda zai ji tana yi wa Hajar magana. A ranta ta sanya bazata ƙara tsoron kowa ba, tun da ya Ahmad yana nan ko ya koreta ba ta da matsala.

Allah kaɗai ya san yadda ya ji a lokacin da ta saki dariyar. Mamakin maganar da ta yi masa ba tare da shakka ko rawar murya ba, da kuma yadda ta yi kyau ta canza kamar ba ita ba suka kama shi. A maimakon ya ƙarasa kujerar ya zauna, sai dai ya dawo kujerar da hannunsa saboda ba shi da ƙarfin da zai iya ƙarasawa inda kujerar take. Wani irin yanayi ya shiga idanunsa suke masa gizonta. Da sauri ya rintse idanun yana fatan kar su ƙara masa gizagonta.

Saman kansa ya shafa, yana jin ephoric feelings yana taso masa tun daga yatsun ƙafafunsa har zuwa kwanyarsa, amma saboda taurin kai da girman kansa sai ya ƙaryata haka. Hannunsa ya haɗa ya dunkule tare da fara zarya a ofis ɗinsa. Idanunsa ya rintse da suke ƙara muradin ganinta. Ƙoƙarin hana hakan yake yi, amma zuciyarsa na yi masa ingiza mai kantu da ya buɗe windonsa ya ganta. Ba tare da shiri ba ya aiwatar da muradin zuciyarsa. Da sauri ya saki saboda wani irin bugawa da zuciyarsa ta yi. Ta canza ta yi kyau. Da ya ga sabuwar mota, san sai yi tunanin ita ba, saboda yadda mai motar yake tunawa cikin natsuwa.
Chapter 58 · 0% Book details