Sashe 47
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuka ta fashe da shi tare da cewa,"Zan ije aikin ba zan iya jurewa ba."
"Ki yi haƙuri mu je ofis ɗina na duba kuskuren da kika yi." Ta faɗi tare da kama hannunta suka nufi ofishin.
Zama Hajar ta yi tana dubawa."Wannan aikin ai bama na ki bane, sannan ban ga abin da kika yi ba?" Ta yi tambayar tana ɗaga files ɗin.
"So yake kawai ya wulaƙanta ni, har yanzu ya kasa manta abin da na yi masa."
"Wannan ba hujja bace, ya kamata ya dauki ƙaddara a matsayin sa na musulmi."
"Zan gaya wa Marwana zan aje aikin kawai."
"Wannan ba shi ne mafita ba. Ki kaiwa Muhsin files ɗin kawai zan yi mishi magana."
"To," Ta amsa tare da fita ofis ɗin.
Muhsin yana zaune hankalinsa kan desktop da yake aiki a ciki. Jin buɗe ƙofar ya ɗago idanunsa yana kallonta wanda zai shigo, bayan ya ba da izinnin shigowa.
Ganin Nasreen ce dai ya biya da kallo cikin tausaya, domin abin da Damir ya yi sam bai mishi daɗi ba. Miƙa masa takaddun ta yi ya karɓa sannan ta fita.
Tana komawa ofis ta fashe da kuka. Tana jin Ingawa yana bugawa, amma ta ƙi buɗe masa. Kiranta ya yi tana ganin kiran har ya gaji ya daina kiran.
Da ta tashi aikin tana zaune ta tura wa Marwana tsaƙon ta ke aikin. Marwana na kicin ta ga tsakon. Cikin damuwa ta fito motarta zuwa gidan.
"Mai ya faru za ki aje aikin?" Ta yi mata tambayar ba tare da bari sun amsa sallamar.
Mama ta kalle ta cikin mamaki ta ce,"Ake aiki kuma? Mai ya faru saboda ba ni da labari."
"Nima yanzu ta yi mini text wataƙila aure za ta yi, saboda soyayya take yi Mama. Kila mijin da za ta aura baya so."
"Auren babu laifi, amma aikin yana da amfani " Mama ta ce tana kallonta.
Dariyar takaici ta yi sai hawaye."Ya Damir ba ya son ganina kora da hali yake mini, saboda in kika ga yadda ya tozarta ni sai kin tausaya mini, kuma wallahi na yi aikin da ya sanya ni daidai."
Ranta ya bace sosai musamman da ta ke hawaye."Don Allah kar hakan ya sanya ki aje aikin, zan yi wa Momi magana daga ya bazai ƙara faruwa ba." Ta furta tare da share mata hawaye.
"Ki bari na bar aikin kawai, saboda yanada gaskiya. Bai kamata ace yana ganina, bayan na wargaza masa farincikinshi, kuma bana son na ƙara baƙi jini a girinsa, domin in har kika gaya mata ta yi masa faɗa zai ƙara tsanata."
"Zan yi mata magana ta yi masa faɗa, kuma in sha Allahu ba zai ƙara ba."
Ta jima tana bata baki sannan ta yi mata sallama ta tafi. A lokacin da ta koma Hajiya tana sallah a ɗakinta. Saboda ba ta sallah Zama ta yi tana tunanin yadda za ta ɓullo ma lamarin.
Jin motarsa ta miƙe don ta shiga ciki ta sanar da Hajiya, amma sai ta ga Hajiyar ta fito daga dakinta.
Damir yana shigowa ya harari Marwana"Hajiya zan sallami yarinyar da Marwana ta kawo, saboda ba zan iya biyan kuɗi ba ta aiki ba." Ya ce cikin zafi yana kallonta.
Muhsin haushinsa yake ji, tun abin da ya faru don haka ya fara hawa sama ba tare da ya tsaya ba.
"Momi kin ga wulaƙancin da Ya Damir ya yi mata? Ki gaya masa ya fita cikin rayuwarta ni na ɗauke ta aiki ba shi ba."
"Ke Marwana ki iya bakin ki yayanki ne. Ka kuma Damir babu ruwan ka da ita." Ta furta tana kallon su.
"To shikenan tunda kina nuna kina da share a kamfanin, zan rinƙa biyanta da kuɗinki ko da ace ba ta zuwa aikin." Ya ce fuu ya yi sama.
Momi za ta yi cikin takaici domin lamarinsa na damunta.
Tun daga ranar babu ruwanda da ita. Ta ci gaba da aikinta cikin kwanciyar hankali. Tsakaninta da Ingawa kuwa sai abin da ya karu, saboda tun ana ya da ƙanwa har aka fara soyayya. Ita kanta mamaki tayi yadda ta aminta da shi, domin a tunaninta ita da ta ƙara aminta da wani ɗa namiji ba, amma sai ga shi fara jin soyayyar Ingawa a xuciyarta. Ko dayake baza ta ga laifinsa ba, domin a dalinsa ta gane tana da ƙima da daraja. Kalaman da yake gayamata suke matuƙar tasiri a xuciyarta. Ya iya kwantar da kai ya samu zuciyar mace, sannan hannunsa a sake yake. Kullum hidima yake da rayuwarta da yaranta. Kayan wasan da ya siya musu har yawa ya yi musu. Sosai ta sake da shi in har ba aiki take yi ba, wuni suna online. A gurin aiki suke ɓoyewa, saboda babu wanda ya san suna soyayya.
Saboda yadda ta Marwana ta nuna ɓacin ranta, dun daga ranar ba ta ƙara bari ta zargi wani abu ba, ta ci gaba da soyayya da Ingawa hankalinta kwance batare data ƙara tunanin maganar da ta yi mata ba, domin ta san babu hanyar da zata iya jawo hankalin Damir gareta. Mutumin da inya ganta kamar ya ga kashi. Kullum tsanarta kara nunkuwa yake a zuciyarsa.
Ranar safiyar Laraba ya kasance birthday ɗinta. Ita har ta manta da ranar sai da safe ta ga tsaƙon Ingawa na wishing. Murmushi ta saki ta kara ta tsakon fiye da sau ɗaya, sannan ta ije ta yi wanka.
Saboda birthday ɗinta ta yi kwalliya mai kyau. Kuma ta yi wa su Zainab alƙawarin in ta dawo Marwana ta ce za su fita PG. Sosai suka yi murna suna jiran dawowarta.
Kallon kanta ta yi cikin mamaki ganin yadda ta canza. Idan aka gaya za ta yi kyau da ƙiba haka sai ta ƙaryata. Murmushi ta yi ganin yadda fuskarta ta kyau, domin ita kanta burge kanta ta ke yi.
Turare mai sanyin ƙamshi ta fesa, sannnan ta ɗauki jakarta ta fice bayan ya yi wa Mama sallama.
Saboda kyan da ta yi har yangan tafiya take yi, domin abayar ta yi mata kyau.
Da ta isa kampanin ta buɗe get ɗin, daidai lokacin da motar Ingawa ta sawo kai. Murmushi ta sakin masa tare ɗaga masa hannu.
Kallonta ya yi ganin yadda ta yi kyau. Ganin za ta shige da sauri ya kashe motar ya fito.
"Nasreen," Ya ƙwala mata kira ya tahowa inda take da sauri ya ƙaraso.
Matsawa ta yi can dan lungun da babu mutane sosai. Murmushi ta sakar masa. "kin ga yadda kika yi kyau kuwa? Anya yau zan iya aiki."
Kunya sosai ya ba ta, ganin yadda yake kallonta kamar zai cinye. Karka manta birthdayna ne."
"Ina zan manta da wannan ranar! Shi ya sa na siyo kyauta don na bada." Ya ce tare da ya hannunsa cikin aljihunsa ya zobe mai kyau.
"Happy birthday Nasreen kawo hannunki na zura miki." Yadda ya yi maganar da kashe ta da idanunsa, da ya yi suka sanya ta jin kunya sosai.
Da sauri ta zare idanunta, tare da kai hannu za ta karɓa a maimakon ya zura mata.
Ɓata fuska ya yi."Don Allah ki tsaya na sanya miki please." Ya yi maganar cikin shagaɓa.
Sai ta kasa cewa komai tana kallon shi. Mamaki take yi ji take kamar ba ita ba.
Daga bayan su Damir ne a gefensu yana ƙoƙarin kiran waya. Saboda tankin ruwa da ya ɗan kare shi ba su gan shi ba. Duk maganganun da suke yi a kunninsa. Wani irin bugawa zuciyarsa ta yi lokacin da ya juya zai shiga ciki, ganin ba samu wanda yake kira ba.
Nasreen ya gani ta miƙa hannunta Ingawa yana murmushi zai sanya mata zobe. Ji ya yi jiri ya ibeshi lokaci guda zuciyarsa ta buga. Kansa ya sara ta kamar zai fashe. Idanunsa suka yi ƙanana saboda tashin hankali. Tun ranar da Momi ta ce ya fita cikin rayuwarta. Ya ji haushi ko sunanta ba ya son ji, amma kuma abu ɗaya da bai gane ma zuciyarsa ba. Kullum sai ya tuna yana jin haushinta, musamman dai ya shiga yanayin dayake bukatarka matarsa wacce za ta kula da shi. A wannan yanayin Allah kaɗai ya san haushin ta da yake ji, domin shi ma namiji ne dayake buƙatar mace. Alƙawarin da ya yi wa Batula kawai yake mantar da shi wannan yanayin, sannan duk a cikin mata, har yau bai ga wacce zai iya mallaka mata jikinsa.
Ransa ne ya ɓace, idanunsa suka yi ja har ya ji jiri yana ibansa
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 25
Ransa ne ya ɓace, idanunsa suka yi ja har ya ji jiri yana ibansa. Mamakin hakan da ya ji ya yi, sai ya fara tafiya da sauri zai bar gurin, amma tamkar an riƙe shi a gurin ya tsaya. Yana gurin har ya kusa zura mata zoben.
Ga mamakinsa sai ya ji ya fara taku cikin ɓacin rai zuwa gurin. Gabakiɗaya hankalinsu na kan yatsunta da ya sha adon lalli zai zura mata.
"Na ɗauke ku aiki ina biyanku, kuna amfani da lokacina kuna shirmenku?"
Da sauri suka ɗago idanunsa suna kallon shi. Jikin Nasreen ya fara rawa har ta ji ƙasa ba za ta iya ɗaukar ta ba. Hawaye ya fara sauka a kuncinta.
Sun kasa ce masa komai har Ingawa, domin bai taɓa tunanin zai zo gurin ba. Ganin sun yi shiru sun kasa cewa komai, sai ya ci gaba da magana." Ina ganin ka mutumin kirki ashe mara kamun kai ne kai?"