Sashe 14
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lafiya lau Nasreen." Ya amsa yana murmushin saboda komai na ta ya yi masa.
"Amma zan iya aurar 'yar talaka? Dubi irin gidansu." Ya ce yana kallon gidan a wulaƙance.
"Please, Nasreen gani da ƙokon bata domin tun da na ganki na ga matar aure?"
"Gaskiya karatu zan yi kuma bayan haka sam ba ni da ninyar aure yanzu."
Da sauri ya yi mata wani banzan kallo da mamakin ƙarfin halinta. Ganin mutum mai aji da 'ya'yan banki kamarsa ya zo tana 'yar gidan talaka liƙis tana gaya kishi zabinta.
"Da dai kin duba lamarin saboda duka taimakon juna za mu yi, kuma gane da karatun ki zan ɗauki nauyin karatun." Ya ce cikin ƙosawa saboda shi mutum ne wanda bai iya roƙo ba.
"Na gaya maka zaɓina kuma ina fatan za ka je gaba ka nema. Allah ya ba ka wacce ta fini." Ta faɗi haka za ta juya.
Baba da ya dawo daga kasuwa. Yana tafe yana surutu tare da surfawa wasu yara da suke ball suka kusa buge shi zagi.
"Ka ga mini 'ya'yan Allah bani, yan banza marasa tarbiyya." Ya ce yana huci.
Turus! Ya tsaya daga nesa yana hango tsaleliyar motar dake dake a gaban gidansa.
Shafa idanunsa ya yi tare da sungulin kansa don ya gane ko mafari ne.
"Ikon Allah! Ko dai aljanu suka ije motar nan na ke ganin su a zahiri? Ni dai na san unguwannan ta matsiyata ne, sam babu wa da yake da arzikin mota. Daga keke sai mashin." Ya ce tare da fara tafiya cikin sauri.
Don Allah ayi mini haƙuri daga yau zan rinƙa posting page ɗaya, sai bayan sallah na ci gaba da biyu.🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
*_WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
*08144072423*
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 8
Shafa idanunsa ya yi, tare da tsungulin kansa don ya gane ko mafari ne."Ikon Allah! Ko dai aljanu suka ije motar nan na ke ganin su a zahiri? Ni dai na san unguwannan ta matsiyata ne, sam babu wa da yake da arzikin mota. Daga keke sai mashin." Ya ce tare da fara tafiya cikin sauri.
Shafa motar ya fara yi yana kallon ta yadda take sheƙi.
"Kai wasu dai wallahi duniya na maraba da zuwansu. Dubi mota sai kace yau aka ƙero ta?" Ya ce tare da ƙara shafata yana bin gefe-gefe.
Tsananin mamaki ya kama shi ganin Nasreen tsaye da kyakkyawar saurayi.
"Nasreen!" Ya ƙwala mata kira yana faɗin haka.
Jikinta ne ya kama rawa ganinsa. Ba tsoron ya ganta tana zance take yi ba, ta san cewa dole sai ya kwafsa.
"Ga Babana ya dawo bari na tafi. Ina maka fatan alkhairi." Ta ce tare da kama hanyar gida da sauri.
"Dawo don ubanki na ce. Ki dawo munafukai banza." Ya ce da sauri ganin za ta shige.
Ƙwalla suka cika mata idanu ganin toxarcin da yake mata.
"'Yar banza. Ni za ki wa alaye? Dama abin da kike zuwa kina yi ke nan a jami'a, kike fakewa da karatu kika hana yaron nan ya tara kuɗinsa."
"A'a Baba, wallahi yau ne kawai na taɓa tsayawa zance."
"Gaya wa banza wanda bai da wayo." Ya ce tare da ƙarasowa ya jingina da motar yana wa Faruk kallon sama da ƙasa.
Faruk shi ma kallonsu yake a wulaƙance. Ya sausauta kallon jin ta ce masa Baba.
"Mahaifinki ne?" Ya yi tambayar cikin rashin yarda.
"A'a kai ka haife ta. Ko don ka ganni baƙi?" Ya yi masa baƙa tare da tambayarsa.
"Allah ya ba ka haƙuri." Ya ce zai buɗe motarsa. Shawarar fasa auren ya yi ganin kalar mahaifinta.
"Dawo ɗan saurayi dawo mana." Ya ce tare da jawo masa riga.
"Don na dawo kuma sai ka tafi? Ba ni da matsala ai. Ka ganni sam ba ni da damuwa. Mai yake tafe da kai?"
"Gani ta na yi ina so zan aure ta, amma kuma na fasa saboda ta ce mini karatu..."
"Kara me? Kuma a gidan uban wa?" Ya katse shi yana faɗin haka.
"Karatu za ta yi don haka Allah ya ba ta sa'a." Ya furta zai shiga.
Da sauri ya riƙe hannunsa tare da rufe motar.
"Kana sonta ko?" Ya yi masa tambayar da ya kasa amsa masa.
"Wallahi na ba ka ita, ko yau za a ɗaura aure zan ba ka ita. Da ma tuntuni nake ta ma 'yar banzar yarinyar nan, maganar ta fito da miji, amma ta shafa ma idanunta toka, tare da yin kunnen uwar shegu da magana. Yanzu kuwa tun da Allah ya kashe ya ba ta mai ƙubbar susa. Ba zan bari ta yi sake ba. Kasan su mata ba hankali ne da su ba."
"A'a, tun da ba ta sona ba zan yi mata dole ba, ta yi karatunta Allah ya ba ta sa'a." Ya ce yana mamakin zagin da yake yi kamar ya fito daga zuriyar maguzawa.
"Ai tun da kazo ɗan saurari babu tafiya. Karatun banza? Mutane nawa suka yi karatun babu aiki. Shi Ahmad shi na ke kallo shashasha da yake ɓata kuɗinsa gurin karatunta."
"Da ma ba kai kake biya mata ba?"
"An gaya maka jikin banza ne da ni? Da zan je na yi ƙwadigo banci ba na kaiwa Nasara? Yayanta da ya yanke kazar wahala yake biya. Yanzu kuwa tun da tarkota ya kama kurciya, na rantse ba ta da miji sai kai."
Nasreen kallon sa take yi tana hawaye, ganin toxarcin da yake ja mata. Da ma ta san tun da ya zo gurin sai ya yi abin da zai ja mata kunya. Tun ɗazu take alla-alla Faruk ya tafi."
"Baba, ka.."
"Rufe mini ba ki kafin na ci ubanki." Ya ce yana harararta.
"Ka kawo kuɗin sadakin yanzu ma sai a ɗaura."
"Sai ka ce wata bazawara?" Faruk ya yi masa tambayar cikin tsananin mamaki.
"A to mene ne, ko kanta farau? 'Yan mata nawa aka ɗaura ma aure da ga zuwa jin magana."
"To ni ma ina da magabatana saboda ba daga sama na faɗo ba, dole na je na sanar da iyayena." Ya ce yana masa kallon mamaki. A ransa kuwa ya sanya cewar shi da gidan har abada, saboda ko mutuwa zai yi saboda sonta ba zai dawo ba.
"Bari na kama kaina ban ga gidan aure ba." Ya ce yana ƙoƙarin shiga mota.
"Tafiya za ka yi ɗan saurayi?" Cewar Baba yana riƙe rigarsa.
"Lafiya mai ke faruwa a nan?" Ahmad da ya dawo daga gurin kanikanci, ya faɗa yana kallon Nasreen ganin tana kuka.
"Yauwa Amadu, zo ka ga wannan mara ƙashin arzikin, wai ba ta son wannan saurayin da ya zo neman aure ta."
Tamke fuska ya yi yana kallon Nasreen."Shi ga cikin gida."
"Baba kai ma ina son magana da kai." Ya ce ba tare da ya kalli Faruk da ya riƙe sitiyarin mota yana masa kallon ƙasƙanci ba.
Faruk kuwa raka shi da idanun ya yi cikin kallon ƙyama. Ganin yadda kayansa suka yi duƙu-duku.
"Tafiya za ka yi?" Cewar Baba yana kallon sa da ya shiga motar ya tada.
"Anya wannan yaron zai yi kyauta kuwa? Kai daga ganinsa marowaci ne.Ko 'yar fara ai ya miƙa mini."
"Da ma zance kike yi da maza ba karatu ba?" Cewar Ahmad cikin fushi yana kallonta ba tare da ya damu da kukan da take yi ba.
"Wallahi Yaya Ahmad ba na kula kowa." Ta ba shi amsa cikin muryar kuka tana share hawaye.
"To mai ya kawo shi ƙofar gidanmu?"
Gaya mishi yadda suka haɗu ta yi."Ki tsaya ki kula da karatun ki, kar ƙi kara yarda wani namiji ya biyo ki. Kina ganin abin kunyar da Baba ya yi miki."
"To," ta ce tana share hawaye.
Jikin Fadila ya yi sanyi sosai ta ji babu daɗi ganin lamarin da ya faru.
"Don Allah ki yi haƙuri duk ni na ja miki."
"Babu komai Fadila, domin na san shi ma ya kori kansa ba zai dawo ba" Ta ce tare da jan majina tana share hawaye.
Faruk kuwa, tsananin mamakin halin mahaifinta yake yi. Shi tun da yake a rayuwa bai taba ganin mahaifi irin sa ba. A ransa ya sanya shi da gidan har abada.
Amma me tun da ya koma gida ya rasa sukuninsa. Da ya rufe idanu ita yake hangowa. Ganin abin na son fin ƙarfinsa ya sa shi tsaida tunaninsa cak. Saboda takaici har marin ka sa ya yi, amma ya kasa mantawa da hoton fuskarta.
Kwana ɗaya biyu tun yana tunanin zai daina, sai ƙaramar magana ta zama babba. Ya rasa yarda zai yi. Numbar Fadila ya nema a cikin call da suka yi, saboda tun a hanya a ranar da ya bar ƙofar gidan ya goge.
Da ƙyar ya gane numbar da ta ƙare da sifili da biyu.
Kira har sau uku ya yi mata ba ta ɗauki ba, duk da cewar ta yi mamakin kiran shi. A tunaninta abin da Baba ya yi masa ba zai ƙara marmarin ko ganin numbarta ba.
Ganin ya ƙi daina kiran ya sa ta amsa tare da sallama a daƙile.
"Don Allah Fadila ki taimaka mini na ji muryar Nasreen?" Ya ce mata cikin damuwa.
Mamakin abin da ya faɗa ta yi take ta fahimci don Allah yake sonta.
"Nasreen ba ta sonka ba za ta saurare ka ba. Don Allah ka yi haƙuri kamar yada ta gaya maka. Bana son a sanadin ka mu samu matsala da ƙawata." Ta ƙarashe maganar tare da kashewa ba tare da ta ji mai zai ce ba.
Da fari ya yi nufin haƙura amma sai ya kasa. Cikin rashin kuzari ya ɗauki motarsa sai ƙofar gidansu.