← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 92

Sashe 24

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki tashi ki je ki yi wanka Ahmad ya kai ki allura. Ya ce na gaya miki ki shirya ya fita ya shigo miki biredi, ki haɗa da wannan."

"Da ma ya barshi saboda ba wani cin biredi na ke yi ba." Ta ce tana ƙoƙarin saukowa daga gadon.

"Ko za ki fara yin wanka ne?" Mama ta yi mata tambaya tana kallon ta.

"Eh bari na yi wankan na fi jin ƙarfi." Ta ce tare da miƙewa.

Bayan ta sauke mata ruwan ta sanar mata da take ta yi wanka. Tana ƙoƙarin shiga cikin bayin, Baba ya fito daga cikin ɗaki yana miƙa da alama lokacin ya tashi.

"Ke Nasreen, lafiya na ganki a gidan nan?

"Farouk ya ce na dawo gida."

"Da ya ce ki dawo sai kuma kika dawo saboda ba ki da hankali?"

"So kake ta zauna ya kashe ta ko?" Mama da take gindin murhun ta yi masa tambayar a maimakon amsa.

Harara ya zabga mata yana kallon ta."Ok, ke kika ɗauke mata gindi kenan?"

"Cikin dare ya koro ta, kuma ba ta da lafiya sai na ce ta koma? Saboda rashin imanina?"

"Dole za ta koma don ba za ta zauna a cikin gidan nan ba."

"Nasreen, babu in da za ta Baba. Ka ji tsoron Allah ka tausaya rayuwar ta. Jiya tun safe muna asibiti da ita ba ta da lafiya, amma mutumin nan ya ƙi kaita kuma bai zo ba. Bayan ta dawo ya ba ta zaɓin ta zubar da ciki ko ta bar masa gidansa. Sam ba shi da imani. A matsayinka na uba, bai kamata ace ka barta ta ci gaba da zama da wannan mijin ba."

"Ok, na sanya ta kashe auren na zo na rinƙa kasata a tire ko? Mata nawa ne suke haƙuri a gidan aurensu? Ai yanzu duk macen da kaga tana gidan mijinta haƙuri ne ya zaunar da ita."

"Baba, ko me za ka ce Nasreen ba za ta koma ba, in har ba Faruk ne ya buƙaci haka ba."

"Sai ka zaunar da ita kana kallonta. Abincin da za ka bata ta ci ya isheka wahala." Ya furta tare da ɗaukar buta babu kunya ya yi ƙofar gida.

Inda Nasreen da take zubar hawaye ya ƙarasa."Ki shiga ki yi wanka babu in da za ki je, kuka in sha Allahu ba zan rasa abin da zan ba ki kici ba."

"To," Ta amsa cikin muryar kuka ta shige bayin.

"Baba matukar bai canza halinsa ba, Allah sai ya hukunta shi. Kina jinsa Mama, saboda abin da za ta ci yake don ta koma ta ci gaba da zaman wahala a gidansa? Abinci shi ne kawai damuwar bawa, da har zai ce ya koma don yana ba ta abinci?"

"Ku yi masa fatan shiriya amma yana buƙatar ya gane gaskiya."

"Allah ya shirye shi." Ya faɗa jin abin da ta ce.

Da ta fito ta canza kaya sai ta shafa mai. Zama ta yi ta tafka tagumi hawaye yana bin ƙuncinta.

Da ƙyar Ahmad ya rarrasheta sannan ta samu ta karya. Kwanciya ta yi kan gadon Mama cikin damuwa.

Farouk kuwa bayan fitarta hankalinsa kwance ya yi kwanciyarsa. Washegari da safe ko tunanin ta bai yi ba, ya shirya kansa ya wuce gurin aiki.

Kwana ɗaya biyu har sati suna tunanin zai zo, amma shiru ya kar malam ya ci shurwa. Ganin haka Baba ya wanke ƙafarsa ya je har gidansa.

Yana ta bugu da kwaɗa sallama. Tun da ya fito ya ji muryarsa, ya koma ya yi zai iyarsa yana kallo. Sai da ya tabbatar da ya gani sannan ya je ya buɗe gidan.

A lokacin har ya gaji ya jiya zai tafi." Da sassafe ba za a bari mutum ya huta ba, in har maula ya kawo mutum Gara ya juya, tun da babu uban da ya ba ni ajiya." Ya buɗe ƙofar yana faɗin haka.

"Au Ashe kai ne?" Ya yi masa tambayar cikin ɗauke fuska tare da haɗe hannunsa ya riƙe a cikinsa yana kallonsa.

"Na yi tunanin babu kowa a cikin gidan, saboda na kusan awa ina ƙwankwasawa?"

"Ina nan bacci na ke yi." Ya ba shi amsa fuskarsa babu fara'a.

"Ina kwana?" Ya yi masa gaisuwar a gajarce.

"Ai na ɗauka ba za ka gaishe ni ba, domin Faruku na san za ka aika."

Banza ya yi da shi yana kallonsa, don ba shi da abin da zai ce masa.

"Nasreen, da ka turi gida har sati ba ka zo ba, mene ne nufinsa?"

"Ba ta gaya maka abin da ta yi mini ba?" Ya yi amsa tambayarsa a maimakon ya ba shi amsa.

"Ta ce mini ba ka son haihuwa?"

"Eh, saboda ban shirya tara 'ya'ya ba na kasa ciyar da su." Ya ba shi amsa yana kallonsa.

Ya san cewa magana ya gaya masa, amma sai ya basar bai tare da ya ce masa komai ba, don ya san zai fadi abin da ya fi haka."

"Ba a haihuwa aka haife ka, ko daga sama ka faɗo?"

"Ba haihuwar ba ce ba ni da ra'ayi. Na gaya maka bana son na tsufa da wuri ne. Na yi mata maganar mu yi tsarin iyali, amma sai ta bijire mini. Ni kuma ba zan zauna ina ciyar da matar da ba ta mini biyayya."

"To yanxu mene ne nufinka?" Baba ya yi masa tambayar ganin yadda yake cika yana batsewa.

"Ba ta gaya maka ba? Na gaya mata sai dai ta zaɓa. Ko ta bi umurnina, ko kuma a biya bi abin da na kashe don ba zan yi asara ba."

Zare idanunsa ya yi jin abin da ya ce. Dariyar ya saki yana kallonsa."Ka san Allah, ko kana tsafi Faruku, ka ce na biya ka kuɗin da ka kashe, wallahi biyar ba za ka samu ba. Don haka tun wuri ka sasanta da matarka ku zauna lafiya."

"Kai dai za ka yi wa 'yarka faɗa ta zauna a ɗakinta in ba haka ba, duk abin da na kashe sai an biya ni, don babu abin da na mora a aurenmu. Haka kawai ka haifi yara ka kasa basu tarbiyrt da za su yi wa miji biyayya? Wallahi da na san haka take babu abin da zai sanya na ɓata kuɗinta na aureta."

Duk rashin mutuncin Baba sai ya tsaya kawai yana kallonsa yadda yake gasa masa magana.

Ƙasa ce masa komai ya yi, saboda ya san ya fi shi iskanci.

"Shikenan zan je na lallaɓata ta amince sai a xubda cikin, innya so kuka ƙara fahimtar juna sai ku haihu."

"Da dai yafi maka alkhairi kai da ita."

"Bari na wuce, in sha Allahu yau za ta dawo."

"Kar ta dawo in ta so. Ka ta za ta cuta ba ni ba." Ya ƙarashe maganar yana watsa hannunsa.

"Umhm! Farouk, haka za ka barni na tafi? Kasan da nisa tsakaninmu kuma wallahi a ƙasa na taho?"

Babu kunya ya watsa mishi harara yana faɗin,"Ban kira ka ba kuma ni ba ni da kuɗi a jikina. Kai kuma ba waya ce da kai ba."

"A dai duba ba a rasa ba."

Dudar dubu ya zaro ya miƙa masa cikin ɗauee fuska.

Da sauri ya karɓa yana washe baki.

Faruk kuwa tsaki ya yi tare da raka shi da kallon ƙaskanci.

Baba na komawa gida ya shiga, ɗakin Mama da take zaune da carbi a hannunta tana ja. Babu sallama ya ɗaga labulen yana faɗin,"Kin san Allah? Dole Nasreen ta koma gidanta, don ba zan yarda ta haifar mini ɗan wani a gidana ba."

"Haba Baban Ahmad! Yaron nan tun da ta zo ya ƙi zuwa, shi ne kuma kake son ta koma?"

"Eh, dole ta koma sannan ta bi umurnin mijinta, na gaya musu ai duk wacce na aurar ba za ta dawo ta yi mini zawarci ba."

"Nasreen ba za ta koma cikin gidanta ba, in har bai amince ta haifi cikinta ba." Ahmad ya furta haka.

"Amaduu! Wallahi ka kiyaye ni. Ka bar ganinka shirgege tsaf zan sanya maka tafi." Ya ce yana nuna sa da yatsa.

"Baba ka ji tsoron Allah. Ka da Nasreen ta mutu saboda baƙincikin da take fuskanta a gidan aurenta. In ban da don zuciya. Mijin da ba ya buƙatar haihuwa har kake so ta koma gidansa?"

"Ka fito kai tsaye ka zage ni. Dama na san ba ka ɗauke ni da daraja ba. A yanzu ma ba ku ƙi na gungure na faɗi na mutu ba."

Shiru kawai ya yi cikin ɓacin rai, ba tare da ya ce masa komai ba har na wani lokaci, sannan ya kalle sa ya ce,"Ba za ta koma gida...."

"Wai Nasreen 'yarka ce ko yata?" Ya yi masa tambayar cikin tsawa.

"Kai ka haife ta, amma ni ɗan'uwa ta ne. Dole na ƙwatar mata 'yancinta."

"To shikenan, mu zuba ni da kai shege ka fasa." Ya waiwaya inda take tana ta kuka.

"Ta shi ma za ki koma ɗakin mijinki." Ya ce mata cikin tsawa.

Miƙewa ta yi tare da ƙara sautin kuka ta tana haɗa kayanta.

"Babu inda za ki wallahi har sai A ya zo bikonki, kuma ya gane kuskurensa." Cewar Ahmad ya kama hannunta.

"Bari na fita na dawo, kar ta koma gidanta za ka ga abin da zan yi muku." Ya ce cikin fushi tare da fita fuu kamar kububuwa.

Kuka take yi sosai cikin damuwa. Ta san cewa in har ta koma gidan ba tare da ya zo ba, wulaƙancin da zai yi mata sai yafi wanda ta baro.

"Ki yi shiru ki share hawaye ki babu inda za ki." Cewar Ahmad.

Mama kuka take yi tana tausayinta sai dai babu abin da za ta iya yi.

Farouk kuwa ya yi tunanin za ta dawo. Don haka ya ƙi fita a ranar kwata-kwata, ya ƙudiri in har ta dawo maganganun da zai gasa mata. Maganin da ya bata ta ƙi sha ya ɗauko, tare da ije su a fili. Ya ƙosa ta dawo ya ba ta tasha. Tun da ta samu ciki hankalinsa yake tashe, don kar ta haihu ta ragwaɓe.

Shiru yana zuba ido har cikin dare ba ta dawo ba. Tun yana sa rai, har ya cire ganin kwana biyu ba ta dawo ba.
Chapter 24 · 0% Book details