Sashe 83
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Oh please stop crying ko kina so na yi?" Yadda ya yi maganar da ɓata fuska da ya yi, ya sanya ta saki dariya ba tare da shiri ba
"Kin ga yadda kika yi kyau? Gaskiya kuka da ɗaure fuska ba ya miki kyau."
Murmushi ta yi bata ce komai ba. Ganin sun yi shiru na wani lokaci sai ya yi ajiyar zuciya ya ce,"Wane fata kike yi wa aurenmu?"
Ganin ya yi maganar cikin rashin wasa sai ta daure ta ce,"Ina fatan mu kasance cikin farinciki, sannan mu gudanar da rayuwar aurenmu, cikin tsarin Musulunci da koyarwa ta Annabi Muhammad (A.W.S)"
A tare suka ƙarashe. Jin ta yi shiru ya ce,"In sha Allahu za mu yi rayuwarmu cikin tsarin Islama, sannan mu samu zuriya ɗayyiba. Fatana duk shekara ki yi wa Little Marwana ƙanni."
Zare idanunta ta yi ba tare da ta ce komai ba. Dariya ya yi sannan ya miƙe. Mu je mu yi alwala, sannan mu yi sallah. Mu roki Allah ya bamu zaman lafiya mai ɗorawa." Ya ƙarashe maganar tare da kama hannunta.
Wani iri ta ji haɗuwar hannunsu. Kasa cewa komai ta yi, tana jin kamar ta janye hannu. Duk da yanayin da ta shiga nasa ya fi nata, amma sai ya jure suka nufi bedroom ɗinsa a sama. Kallo ɗakin ta yi ganin yadda ɗakin ya tsaru. Damir rage baban rigarsa ya yi, sannan ya kalle ta ya yi murmushi ya wuce bayi.
Tana tsaye ya fito daga bayi bayan ya yi alwala. ""Ki shiga ki yi." Ya ce mata sannan ya wuce wandrop na sa ya ɗauki dadduma ya shinfiɗa musu.
Da ta shiga bayin, sai da ta ƙare masa kallo saboda ɗaukar hankalinta da ya yi. Bayan ta yi alwalar ta fito.
Mamaki sosai ta yi ganin ya ije mata hijabi. Tunani ta fara ko ɗauko mata ya yi. Ba tare da ce masa komai ba, ta tsaya a bayansa ya fara ja musu sallah
Nasreen hawaye ta ji yana zuba a ƙuncinta, jin yadda yake sallar cikin natsuwa yana jan aya. Ba ta ƙara farinciki ba, sai da ya ja sallar raka'a biyu, sannan ya dafa goshinta ya yi addu'ar da Annabi ya koyar da mu in mu yi sabon aure. Ya kuma shiga jero addu'a. Sai ta ji hawaye yana zuba mata, tuna ranar aurensu da Faruk kamar dole aka yi masa ya yi sallar. Yana gama sallamewa ya jawo kazarsa.
Ya daɗe yana mata addu'a, sannan ya sauke hannunsa yana kallonta. Sunkuyar da ka ta ta yi ƙasa ta yi, tana godiya ga Ubangiji da ya ba ta mijin da take so, mai addini da aiki da shi.
Damir kallonta yake yi sai ya rasa ta inda zai fara. Kunyarta ya yi yawa, kamar ba ta taɓa aure ba. Ya tabbata da wata matar ce ya aura a matsayin bazawara, abin da za ta yi mishi sai ya yi mamaki.
Gyaran murya ya yi, sai ta kalle shi a kunya ce tana hamma.
"Bacci? Bai kamata ki ji bacci a ranar yau ba."
Abin da ya ce da kallon da ya yi mata ta kasa cewa komai.
Janyo ledar da ya shigo da ita. Kayan ciye-ciye da kaji ne a ciki sai kuma naman balango, da kuma fannin drinks kala-kala.
Da kansa ya miƙe zuwa kicin, ya ɗauko musu filet da spoon sai ƙaramar wuƙa.
Yankan namar kazan ya yi, yana murmushi ya kai mata baki. Da sauri ta kauda fuskarta cikin jin kunya."Nasreen na fara gajiya da wannan kunyar ta ki, a haka za mu raya wanann daren?"
Kasa amsa masa tambayar ta yi."Na ƙoshi Mommy sai da ta tabbatar mun ci abinci da Marwana, sannan ta barmu muka tafi gidan Marwana."
"Amma tun yaushe kika ci? Kuma ko kin ci abinci dole na ciyar da ke a First night ɗinmu. Please ki ci ko babu yawa." Ya furta cikin sigar rarrashi
Ba ta karɓa ba sai ta kalle shi za ta yi magana. Ganin yadda ya ɓata ransa sai ta buɗe baki a kunya ce."Good girl." Ya ce tare saka mata naman kazar.
So take yi ta ɗan saki jikinta, amma sosai take jin kunyarsa, kuma shi yake ƙara sanya mata kunyar da irin kallon da yake mata. Har yau ta kasa sabawa da kallon da yake mata, domin ita kaɗai yake yi wa. In har zai yi magana da ita, sai ya canza kalar idanunsa.
Ganin ba za ta ci ba sai ya yi mata dole tasha drink. Kayan ya kwashe ya kai kicin ya sanya a frij.
Tana zaune ko motsin kirki ta kasa. Ganin ya nufi wandrop nasa, zai sanya kayan bacci cikinta ya ɗuri ruwa.
"Ya Damir, zan je na canza kayan bacci."
Juyowa ya yi ya watsa mata kallo, saboda ya fahimci guduwa za ta yi. Ganin yana ƙoƙarin cire rigarsa ta kauda idanunta, sai ya rage hasken ɗakin.
"Please Baby stop calling me Ya Damir. Daga yau ina son ki canza mini suna ga sunaye masu daɗi na ƙauna." Ya ce baya ya cire rigar, ya rage da ga shi sai singeleti da dogon wandon shaddar.
Yana ƙoƙarin cire agogonsa ya nufo inda inda take. Ganin haka sai ta yi kamar za ta ruga.
Kamar ya sani ya sanya hannunsa ya riƙo ta yana dariya. Ita ma dariya abin ya ba ta, saboda yadda ta zabura kamar ta ga wani zaki.
Kunyarsa sosai ta ji da ya haɗata da jikinsa. Jikinta ya fara rawa har sai da ya gane."Nasreen kin cika kunya don Allah ki saki da ni. I don't bite. Wannan abin ƙaramar yarinya ya kamata ta yi haka, amma ke kamata ya yi ki nuna mini soyayya kuma ki yi pampering ɗina."
"Don Allah, ka bar ni na canza kaya bacci sun yi mini nauyi." Ta ce cikin rawar murya ganin yana ƙoƙarin haɗa fuskarsu.
"Ok," Ya ce tare da kama hannunta ya ƙarasa dayan wadrop ya buɗe."Kin ga waɗannan kayan Nasreen, ni na siyo da na je Dubai, saboda ina son matata na ganta da ƙananan kaya. Lokacin Batula ta saba in har ba fita za ta yi ba, ƙananan kaya ne a jikinta kodayaushe. Haka kuma nake so ki zama, ga kuma kayan bacci nan suma duk na ƙaro miki."
Wani irin azzabben kunya ya lulluɓeta, ganin ya ɗauko doguwar riga ya bata. Kallonsa ta yi, yayin da ya ɗaga mata gira alamun ta saka.
Rigar ba ta da maraba da babu. Tana da kyau sosai, amma irin transparent ɗin nan ne."
Girgiza masa kanta ta yi, sa kawai ta fara hawaye ƙila ya fahimci tsananin kunyarsa da take ji, tun da ta gama fahimtar ba yi da shi. Ashe dama haka yake.
Ganin hawayen, sai ya ɗauko mata riga da wando purple masu kyau. Karɓa ta yi ba tare da ta ce mishi komai ba ta wuce bayi.
Zama ya yi kan gadon bai ce mata komai ba, saboda yasan dama ba za ta iya canzawa a gabansa ba. Har ya zauna sai kuma ya miƙe ya canza kayan shi zuwa na bacci.
Nasreen da ta sanya kayan, sai ta tsinci kanta da kasa fitowa. Ita kam ta ƙosa gari ya waye. Ko daren amarcinta da Faruk ba ta ji kunya haka ba.
Wayarsa ya janyo yana duba pictures na bikin, amma har ya gaji da dubawa ba ta fito ba. Ije wayar ya yi, ya nufi bayin domin ya fara tunanin kwana za ta yi.
Yana ƙoƙarin ƙwankwasawa ta fito kamar mara gaskiya."Da a bayin za ki kwana?" Ya yi mata tambayar cikin mamaki.
Ba ta amsa mishi ba, sai ta ƙarasa tsakiyar ɗakin ta tsaya. Damir ya lura in har ya biye mata sai dai su ji kiran sallar asuba. Don haka ya jawota ya haɗata da jikinsa. Ajiyar zuciya suka saki a tare, lokaci guda kuma suka sauke numfashi.
"Wannan ɗan kunnen, ya yi miki girma Please baby ki kiyaye, saboda ba son kina wahalar mini da kanki."
Murmushi ta yi cikin farinciki, ba ta ce masa komai ba, har ya cire ɗan kunnen ya ije kan mirror. Fuskarsa ya kai a dogon wuyanta, yana saukar mata da numfashin da yake sanya mata kasala.
"Nasreen kin ga ikon Allah ko? Ubangiji dama tun farko ya riga ya san zamu yi aure, shi ya sa ya haɗa ki da Marwana. Nasreen yau kin zama matata, bayan tsawon lokacin da na ɗauka ina dakon sonki. Ina sonki kuma na yi miki alƙawarin kulawa da rayuwaki har da yaranki. A shirye na ke na zama ubansu, in har kin amince za su dawo gidan nan."
Da sauri ta kalle shi cikin mamaki."Yes na zama mahaifinsu tun da kin zama matata. Zan haɗa su da Little Marwana na riƙe."
"Na gode Ya Damir, ba ni da abin da zan ce maka da 'yar uwarka." Ta furta tare da sakin kuka.
Sai a lokacin ya tuna da Marwana, ya san tana can tana yi wa Ahmad shagaɓa, domin yau Allah kawai zai shawo masa kanta.
"Is ok, kin cancanci haka domin kin sha wahala. Zan kula da rayuwarki yadda babu wata mace da za ta fiki." Ya ƙarashe maganar tare da rungumeta yana sauke numfashi.
Duk da tana jin kunyarsa, amma albishirin da ya yi mata, sai ta ji ta kasa janye kanta daga gare shi. Ganin haka ya ƙara matseta sosai. A hankali ya haɗa fuskarsu yana ƙoƙarin ɗauke mata hawayen da harshensa. Ganin haka ta kauda fuskarta cikin wani yanayi.
Janyota ya yi suka faɗa gadon ya yi mata rumfa. Damir Gabakiɗaya ɗaya ya birkice, mata domin ƙamshin turarenta ya fara aiki. Tun tana ƙoƙarin turesa har ta gaza don ya canza mata, saboda bai san tana yi ba.