← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 92

Sashe 44

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Komawa ta yi ta ci gaba da aikin tana hawaye. Da aka tashi kowa ya fara tafiya. Saboda kar su Hajar su nemeta, sai ta kulle ofis ɗin. Wayarta da suka kira bata daga ba, sun yi tunanin ta tafi don haka kowa ya tafi. Tana zaune har shidda maraice ya fara tana aiki. Hawaye take yi tana aiki.

Wayarta ta ɗauko ta kunna don ta sanya karatun Alkur'ani, saboda tsoron da ya fara kamata, ga shi gurin ya yi shiru. Tana buɗewa messages na Ingawa suka fara shigowa. Kafin ta buɗe dai kiransa ya shigo. Da sauri ta ta katse. Tana ƙoƙarin kashe wayar tsaƙo ya shigo.

"Nasreen, ki ɗauki wayata, saboda na san kina ciki baki fito ba, kuma wallahi kin ji na rantse ba zan tafi gida ba ina nan ina jiranki har sai kin gama aiki."

Zare idaunta ta yi kan dole ta kira shi."Hello," Ta ce cikin muryar kuka.

"Ban taɓa tunanin oga Damir mugu bane sai yau. Nasreen, akwai abin da yake tsananin ku? Don Allah mai kika yi mishi?"

Hawaye suka ƙara zubo mata"Babu komai don Allah ka tafi gida na kusa gamawa." Ta ce tare da kashe kiran.

Tsaki ya yi ya tura mata da cewar yana jira ta gama.

Ba ta gana aikin ba har sai da aka kira sallar magariba. Da sauri ta fito bakinta ɗauke da addu'a, domin tsoro take ji sosai.

Oga kale ko sir Samir wai ya haka ne😄😄😄😄
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.

*WASU MAZAN*

BOOK 2

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 23

Ba ta gama aikin ba har sai da aka kira sallahr magariba. Da sauri ta fito bakinta ɗauke da addu'a, domin tsoro take ji sosai.

Tana addu'ar Allah ya sa ya tafi, amma sai ta gan shi ya fito daga masallacin kampanin hannunsa ɗauke da carbi.

Ganin ta nufi waje da sauri ya fita ya shiga motar. Gabanta ya faka."Ki shigo na kaiki gida saboda na san cewa Mama hankalinta ya tashi."

Ba musu ta shiga domin ta gaji matuƙar gaske! Idanunta har wani zafi-zafi suke mata.

"Mai ke tsakaninki da shi? Tabbas kin san shi kuma akwai alaƙar da ya taba haɗaku?" Ya yi mata tambayar tare da waiwayo wa ya kalle ta.

"Tabbas mutumin kirki ne tun da har kai sai daka zargi na yi masa wani abu. Ba zan gaya maka ba, wataƙila ka tsane ni."

"Ba zan taɓa tsanarki ba saboda Allah ya sanya mini sonki."

"Ka yi hakuri bana fatan tuna abin da ya faru." Ta ce masa cikin hawaye. Ganin haka ya ja bakinsa ya yi shiru, yayin da zuciyarsa take ta tunani.

Da suka kofar gida sai ya kalle ta daidai lokacin da ta buɗe ƙofar."Na gode da kulawarka. Hakan ya tabbatar mini da na samu Yaya mai kaunata."

Murmushi ya yi yace,"Kin cancanci haka ki shiga gida ki yi wanka sannan sallah ki huta Please kin gaji."

"Na gode sai da safe."

"A gaida Yarana da Mama."

Ɗaga masa kanta ya yi sannan ta fice daga motar.

Tana ƙoƙarin shiga sai ga Baba ya fito."Nasreen lafiya kika daɗe haka?"

"Aiki ya tsare mu." Ta ce masa tare da shiga ciki.

Juyawa ya yi ya koma dama yana ta jiranta ta dawo ta ba shi kuɗi.

"Hankalina ya tashi sosai na kira wayarki a kashe, mai ya faru kika daɗe?" Mama ta yi mata tambayar ba tare da ta amsa salamar ba.

"Aiki ne Mama yau kowa sai lokacin da na tashi aka tashi." Ta yi mata ƙaryar haka.

"To hankalinsa ya kwanta shiga ki yi sallah ki huta."

"To,"Ta amsa tare da ɗaukar Musaddik tana shafa kan Raihann.

"Ki aje yaron nan ki je ki huta. Ke Raihan zo na sa ya muku tuwo ku ci, kamo hannu Musaddik ku bari ta huta." Mama ta ce tana janyo robar tuwon da ta gama. Sakin hannunta ta yi suka shiga ciki.

Tana shiga cikin ɗaki ta fashe da kuka takaicin abin da ya yi mata. Tana cikin kuka wayar Marwana ya shigo. Kamar ba za ta dauka ba, sai kuma ta share hawaye ta ta daga wayar da sallama.

"Nasreen kina lafiya?" Ta yi mata tambayar jin muryarta.

"Lafiya lau gajiya ce."

"Na ga Ya Damir y shigo cikin ɓacin rai. Ya Muhsin ya gaya mini abin da ya faru, so dai suka bar ki a kampanin. Mai ya faru?"

"Jin tambaya ya sa ta fashe da kuka."Wallahi ban san abin da na yi masa ba. Ina ganin aje aikin nan zan yi..."

"No, kar ku yi tunanin haka Nasreen. Aiki shi ne gatanki, kuma a tunanina zaman da kika yi da Faruk kin daina wa namiji kuka. Ya Damir mutum ne mai sanyi, in har za ki daure wallahi ba zai ja da fadanku ba zai sauko."

"Hmmmm! Haka kika ce saboda dan'uwanki ne."

"Zan shigo za mu yi maganar gobe. Ko ce Mama ta yi mini dambu gobe."

"In sha Allahu sai kin zo." Ta ce tare da kashe wayar.

Bayan ta yi sallah ta huta, tana zaune tana takaicin abin da ya faru. Kiran Ingawa ya shigo wayarta. Da sauri ta katse tunaninta ta ɗauka. Hira sosai sukayi har sai da katin ya ƙare. Sosai ta sake da shi ganin mutuncinsa, kuma kalaman da yake gaya mata yana sanya tana jin daɗi, har take gane ashe ita na tana daga cikin mata masu daraja da da namiji zai rinka gaya mata kalamai masu dadi. Duk da cewar suna ya da ƙanwa ne, amma maganganunsu duk na soyayya ne. Burinsa ta amince da shi akwai ya yi wuf da ita. Da suka gama wayar kwanciya ta yi xuciyarta cike da tunaninsa.

Faruk

Faruk zamansu da Rashida ya yi daɗi tun da yaran suka koma gurin Nasreen ba. Bai yi tunanin zuwa ba kamar yadda ba ta kira shi a game da yaran. Hankalinsa ya kwanta dai ya ci gaba da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali, domin ya shanye mangaron ya yarda ƙwallon ya huta da ƙuda. Hankalinsa kwance, yake shan soyayya da Rashida yana jin ya huta da maular Baba.

Rashida kuwa hankalinta ya kwanta, ta kara ƙiba ta zama ƙatuwa da kyar ake juyi. Kullum cikin yi masa asiri take yi tana ba shi yana sha. Da wannan ta samu ta shanye jikin saura kan ta mallake sa. Abinci kuwa saboda yadda ta samu kansa komai yan siyen mata, rayuwa ta canza komai ta ga dama shi take yi. Miji da gida ya zama nata. Soyayya suke ci sosai kamar za su lashe kansu, saboda duk abin da ya ce ta yi masa babu shakka ko kunya. A gadon ma, yadda yake so haka take masa harma da abin da bai bukata ba. Hankalinsa ya kwanta ya samu macen da yake so.

A yanzu komai na sa ta san sirrinsa, duk wani abun da ya mallaka sai ya gaya masa. Hatta ATM dinsa da ake ɓoyewa yanzu duk ta sani domin ya canza daga maƙoƙo ya zama mai sakin hannu. Kayan ɗaki komai ya canza mata. Hatta kayan kallo su da ya canza mata. An sanya su solar ya siya mata waya mai kyau.

Da ta sanya masa naci, har mota ya daure ya siya sai ya gyara mata nasa.

Da fari ana zaman lafiya sosai tana cin duniya da tsinke, amma ganin ta samu kansa sai kawai ta bawa 'yan'uwanta ƙafa su rinƙa zuwa maza da mata. Nan fa ya buga tsalle ya ce bai yarda ba, saboda rashin son mutane a jininsa yake. Ga kuma rowar abin da zai ba su ciki. Rigima sosai suka yi da ƙyar ta samu ta shawo kansa ya amince. Daga baya sai ta ɗauƙo ƙanwarta Maimuna ta sanya ta a makaranta za ta ƙaranci English language.

Ya nuna ɓacin ransa sosai, musamman da ba ta yi shawara da shi ba har korar ta yi yi, amma ta dawo ita tursasawar Rashida kan dole ya barta ta zauna.

Babu yadda zai yi haka ya ƙyaleta ta zauna. Aci wannan a dafa wannan. Ɗakin Nasreen aka ba ta da komai da komai. Hatta kaya ta ya ce ta ɗauka, wanda bata so ta yi kyauta da shi. Rayuwa ake yi mai daɗi sosai domin ya saki ya canza. Ta mai da shi irin janitalau komai dai abin da ta ce masa.

Danginsa sun yi matuƙar mamakin haka, sanin wane ne Faruk, amma ko da suka shigo dan su tsawatar rashin mutunci ta sanya ya yi musu, sannan ya ja musu iyaka da shi. Sai suka zuba idanu suna tausayin ranar da zai yi nadama.
Chapter 44 · 0% Book details