← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 92

Sashe 77

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi ba zan daina ba domin matukar ina raye sai na mayar da matata. Nasreen tawa ce babu uban da ya isa ya aureta. Kutu zan kai a ƙwatar mini matata."

Ya ƙarashe maganar yana kumfar baki kamar zarrare, sai kuma ya juya ya ce,"Nasreen ki taimaka na ci albarkacin yarana mu koma da aure mu, wallahi na yi nadama zan riƙe ki da kyau."

Kallon sa ta yi cikin hawaye ta ce,"Ka riga ka yi sake na yi kuka na riƙe ka, alokacin don na zauna a gidan auren kar na yi zawarci. Na sha yi maka kuka don mu zauna lafiya, don kawai mu zauna mu rungumi yaranmu. Ba zan aure ka ba, Ya Damir na ke so shi zan aura, domin ina da yaƙinin zai ba ni kulawar da na kasa samu a gurinka."

"Karya kike Nasreen so kike ki aure shi saboda abin duniya, wannan dalilin ya sa kika rinƙa cin amanata, don haka ba zan taɓa barin ki aure shi ba."

"Haka kace?" Ta yi masa tambayar cikin tsananin mamaki.

"Eh ba zan taɓa barin ya aure ki ba."

Kallon Damir ya yi da ya tsaya yana kallon da cikin mamaki."Ya Damir kana sona?" Ta yi masa tambayar cikin murya da ƙarfi.

"Ina sonki Nasreen a shirye na ke na kashe ko nawa don na aureki, saboda haukar da yake yi ya tabbatar mini da macen ƙwarai ce ke, za ki cike gurbin matata da na rasa. Ni kuma na yi alkawarin zan mayar dake zinariya a cikin mata."

"Alhamdulillah!" Ta ce tare da murmushi hawayen da yake bin fuskarta. Ta kalli Ahmad ta ci gaba da cewa,"Ya Ahmad ka zama waliyin aurena, kuma a nan nake so ka ɗaura mana aure ka zama waliyina. Ina son ya ƙaryata kansa da ya sha gaya mini na babu namijin da zai iya aurena, saboda ba ni da tarbiyya."

Ahmad kallon ta ya yi, sai ya kalli Damir da ya cika da mamakin abin da ta furta. Sosai magantarta ya bawa kowa mamaki.

"Damir ka shirya aurenta?"

Wani murmushin ya kubce masa ya ce,"Eh na shirya kuma a shirye na ke na ba da sadaki mai tsada koda ya kai darajar raina ne. Ga Baba Sani ya karɓa mini aurenta."

"Shikenan a bada sadaki naira dubu talatin, domin mu yi koyi da abin da Annabi ya faɗa don aurenku ya yi daraja."

"Alhamdulillah na gode Ya Ahmad zan bayar da sadakin, amma darajarta ya wuce haka. Na bayar da mota kuma ko tsinke bana buƙata na kayan ɗaki da kayanta, da kuma kujerar maka."

"Alhamdulillah!" Ɗakin ya ɗauki kabbara ban da Faruk da yan uwansa.

"Wayyo Allah! Na shiga uku! Don Allah kar ku ɗaura auren wallahi ina son matata. Zan kashe kaina da su in har aka ɗaura auren. Nasreen haka za ki yi mini? Saboda ba ni da kuɗi sai ki guje ni? Marwana na tsane ki domin kece ki kik canza matata kika nuna mata kuɗi." Ya ƙarashe maganar yana ihu tamkar zautacce, sai kuma ya kama hannun Asiya da Isma'il.

"Kuna gani matata za ta auri wani? Wallahi auren ake ɗaurawa ga shi can za a ɗaura. Shi kenan na mutu a bani yarana don ba zan yarda ba." Ya furta sai kuma ya saki dariya yana kallonsu.

Anty Asiya kama shi ta yi, tana hawaye sosai take yin kuka domin ta sha gaya masa ranar nan, amma ya ƙi ji ya yi kunnen uwar shegu. Yau ga shi Nasreen ta wuce da ajinsa, ta samu ingarmar namiji wanda ta san zata ji daɗi a gidansa, shi kuma babu mata babu kuɗin da ya kasa wadata iyalinsa, sannan ya koma haukarsa, domin yadda yake ihu yana zambarwa, ya tabbatar mata da ya koma gidan jiya.

Wani tsaddaden murmushi ya saki ganin an ɗaura auren. Ya saci kallon ta cikin farinciki, daidai lokacin da Alhaji Sani ya kalle shi."Alhamdulillah an ɗaura sai fatan zaman lafiya."

Sai kawai ya yi dariyar farinciki, sai ya mata da ciwon daya ji ganin Nasreen ta zama matarsa, duk cewar har lokacin bai gama yarda ba.

"Ikon Allah ni da nake neman hanyar da zan kusanta kaina da ita, sai ga shi Allah ya sauƙaƙa mini ta zama matata a lokaci guda." Ya furta cikin zallar mamaki yana kallon ta da take share hawaye

Marwana kuwa rungumeta ta yi cikin farinciki."An ɗaura kin zama matar Ya Damir Anty Nasreen." Kuka ta fashe da shi ta ƙara rungumeta domin ita kanta auren ya zamar mata bazata.

Shi kuwa ya kasa cewa komai, sai kallonta yake yi yana ta mamaki sosai.

"Allah ya sanya alkhairi." Mommy ta ce cikin farin ciki.

"Amin," suka haɗa baki gurin faɗin haka.

Kallon Faruk suka yi, da aka riƙe shi yana zambarwa sai ya kashe su, kuma a ba shi yaranshi. Hawaye ya wanke mata fuska domin abin tausayi ne, duk da tsanar shi da ta yi, sai da ta ji tausayinsa musamman da yake uban 'ya'yanta.

Suna tsaye aka wuce da shi yin ihu yana faɗin,"Nasreen haka ka zaki yi mini? Kin auri wani kin manta da ni uban 'ya'yanki. Wayyo na mutu na lalace Allah ka ɗauki raina huta."

"Anyi Asiya ta tsaya tana kallon ta ta tsare hawaye."Nasreen ina miki fatan zaman lafiya a gidan aurenki. Kin cancanci samun miji kamarsa, haƙiƙa haƙurin da kika yi Allah ya saka miki. Allah ya baku zaman lafiya. Farouk kamar ya koma hauka irin lokacin da Rashida ta sace masa ƙaddararsa. Farouk duk abin da ya faru da shi ya cancanta. Faruk ya cutar dake ya wulanƙanta rayuwarki, amma kuma Allah ya saka miki duba ga irin mijin da ya baki, kuma abin da ya faru da shi ya kamata saboda ya zama iska ga WASU MAZAN da suke wulaƙanta matansu suke ɗaukar su ba'a bakin komai ba. Rayuwarsa ta ishi ya zama ina izna ga WASU MAZAM masu dukan mata da musu horon yunwa. Mace mutum ce tana da daraja domin ita ce tushen kowa. Uwa ce kuma mata ce tabbas ta cancanci a mutunta. Don Allah ki yafe wa Faruk domin ya samu ya rage haƙƙin ki ɗaya ɗauka. Ki yafe mishi wataƙila Ubangiji ya ba shi lafiya, ya samu ya canza rayuwar sa." Ta ƙarashe maganar cikin kuka.

Hawaye ta share ta ce,"Allah ya ba shi lafiya ba komai na yafe masa."

"Amin mun gode. Sannan zan rinƙa zuwa in duba su Raihann." Ɗaga mata kanta tayi sannan ta wuce.

Duk maganar da suke yi idanun Damir yana kanta. Har yanzu ya kasa yarda ta zama mallakar sa zai iya komai da ita na aure. Tsawon lokacin da ya ɗauka babu mata ya kasa yarda cewar yanzu ya tashi a matsayin gwauro mai rungumar filo. Daga yanzu cikin jikinta su rinƙa kwana ba zai lulluɓa da bargo ba. Shi kam sai ya ce gwamma da hakan ya faru, domin Faruk ya yi mishi hanyar da ya mallake ta cikin sauƙi.

Nasreen ɗauke idanunta ya yi ta ƙarasa gurin Ahmad da yake ta kallota. Sai a yau ya ƙara kallon Damir sosai yake murna ganin irin mijin da ta samu. Ta ko ina ya kai ya kai matsayin da duk wacce ta same shi su ta yi ta godiya ga Ubangijinta. Ga kyau ga kuɗi ga jiki na maza sannan ga ilmi both Islamically and academically. Kai gaskiya mahaƙurci mawadaci. Da ya duba halin da ta shiga. Farouk ya ɗaga hannu a gaban Baba da shi ya kai wa Nasreen duka babu kunya. Ta yi kuka ta yi kuka har wani lokcin ya yi saɓon tunanin kamar Allah ya manta da rayuwarta. Ya tuna ranar da ta kira shi da tsohon cikin Musaddik ya hana ta abinci sannan ya duke ta, bayan ya sanya wankinsa da guga. Nasreen ta ga jarrabawar aure, amma kuma Allah ya saka mata.

"Yanzu sai mu koma asibiti, sai Muhsin ya zauna da shi ko?" Mommy ta ce tana kallonsa.

Zare idanunsa ya yi, jin ta faɗi Muhsin zai zauna da shi. Ya kalli Nasreen da take jin kamar ta ce za ta bi shi zuwa, asibitin amma tana jin kunya. Gurin Ahmad ta tsaya tana kallon ƙasa.

"Ok, bari mu wuce gida in sha Allahu za mu zo anjima da su Mama." Cewar Ahmad yana kallon su, sa kuma ya kalli Marwana da take ta farinciki tana tunani itama yaushe za a yi nasu, domin ta so ace tare za a yi bikin, amma kuma sai ga yadda auren na su ya kasance.

Damir kuwa kallo ya bi su da shi, so yake ya ga inda matarsa za ta wuce. A tunaninsa tun da an ɗaura ta zama nasa shikenan gida za su wuce, musamman da ya ce ba ya son komai, amma sai ya ga ta bi bayan Ahmad za su shiga mota, duk da cewar tana son ta yi jinyarsa.

Gyaran murya ya yi, duk suka kalle shi."Mommy ina matata za ta tafi?" Ya yi tambayar ba tare da ya ji kunya ba.

Kallonsa suka yi sai ta yi murmushi."Gida mana Damir. Ai ba kaza bace kawai da za a kamata a kaita gidanka, dole za a yi bikin, kuma an ɗaura iyayenta ba su sani ba, don haka dole gida za ta koma kai ma kana buƙatar lokaci a gidanka za ka zauna, kuma tun da Batula ta mutu ka kauracewa gidan dole a gyara."

"Mommy sai ta zauna a ɗakina, in ma gidan ne a yau zan iya oder na komai gobe a gyara." Dariya suka yi ganin rashin kunyarsa.

*AN ƊAURA AN ƊAURA TA ZAMA MATAR DAMIR💃💃💃💃💃💃💃💃 SU DAMIR BABU KUNYA WAI MATATA😁😁😁😁😁 WATO AN DAINA ZAMAN GWARANCI DUK WACCE BA TA FITO AN SHA RUWAN COMMENTS DA MURNAR BIKI BA KO ZAZZAƁI YA SAUKA BA ZAN JE ƊAUKO RAHOTON ANGO DA AMARYA BA*

Fans ina ba ku haƙuri domin yau da wuya a samu pages biyu, sakamakon zazzaɓi da na ke fama da shi.

Wasu maxan na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
Chapter 77 · 0% Book details