← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 92

Sashe 49

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni fa ban ga abin faɗa ba, saboda Ya Damir sau nawa kake riƙe hannun Anty Batula ka sanya mata zobe a ranar birthday ɗin ta, yau ne ranar birthday ɗinta, wanda zai aure tane ya bata gift."

Ba ta gama magana ba ta ji saukar mari."Saboda iskanci a gabana za ta rinƙa soyayyar."

Dafe kuncinta ta yi ta sanya kuka."To Ya Damir mai na yi za ka mare ni?"

"Saboda ke kika kawo ta duk lokacin da ta baƙanta mini a kanki zan huce." Ya ce tare da wuce wa ciki yana huci ganin kallon da suke masa.

Ya fita suka kalli juna."Alhamdulillah!" Momi ta ce tare da zama tana murmushi.

"Wallahi Momi kishi yake nunawa kishi ne zalla a idanunsa."

"Maganarki takusa zama gaskiya."

Sosai suke murna Momi kamar za ta yi tsalle. Marwana sai tsalle take tana jin dadi, ba tare da ta damu da marin da ta sha ba.

Da gudu ta haye sama tana faɗin."Ina zuwa."

Wayarta ta ɗauka jikinta na rawa ta kira Nasreen. Nasreen na zaune tana gyara fuskarta. Ganin kiran sai haushi yakamata, saboda duk it ta ja mata.

Ɗaukar wayar ta yi tare da sallama."Hello Marwana, dama ina shi...."

"Nasreen akwai abin da za ki iya ɓoye mini?"

Tambayar da ta yi mata ya sanya gabanta faɗin."Lafiya mai na aikata?"Ta yi mata tambayar cikin sanyi.

"Ya Damir mana kin sa na sha mari a banza saboda kishin ya ganki da wani."

"Kishi ya Damir ne yake kishina?" Ta yi mata tambayar cikin zallar mamaki.

"Eh, ya ce ya ganki da Ingawa yana sanya miki zobe."

"Au haka ya faɗa wayyo Allah na haɗu da terere." Ta furta a ranta sai kuma ta godewa Allah da tsanar da yake mata bai sanya shi yin mata sharri ba.

"Sai kuma ya ce miki kishina yake? Marwana kina wani irin tunani, saboda da kin san abin da ya yi mana za ki gane abin da yake nufi. Saboda ya taramu cewa yayi kar wanda ya kara soyayya har ma'auratan gurin."

Dariya ta kwashe da shi cikin jin daɗi."Ikon Allah haka ya ce?"

"Hmmmmh! Ni fa wannan aikin watarana sai dai na aiko mini da resignation letter, saboda bazan jure wulaƙanci ba."

"Wallahi Ya Damir kishi ya sanya shi faɗin haka, kuma watarana za ki gane hakan."

"Ki ci gaba da yarda da zuciyarki tana ɗora ki kan keken ɓera, kin san babu yadda za a yi haka ya faru."

"Sai mun haɗu za mu yi magana." Ta ce tare da kashe waya ganin ta ƙi fahimtarta.

Da yamma Ingawa ya zo saboda ya kasa barin dare ya yi. Baba na zaune ta zo ta wuce zuwa motarsa. Kallonta ya yi yana faɗin,"Oh ashe dai jinin masu kuɗi a jininki yake dubi yadda kika samu daƙwale yana ba ni kuɗi ko ban tambaya ba."

Motar ta shiga ta zauna tare da gaishe shi.Kura mata idanu ya yi na wani lokaci, sannan ya yi ajiyar zuciya.

Shiru suka yi zuwa wani lokaci sannan ya katse shirun ta hanyar cewa,"Ki gaya mini abin da yake tsakaninku, saboda a fara zargin kishinki...."

Kallon da ta yi masa ya katse abin da yake faɗi yana kallonta.

"Ni ka ga kishina a idanunsa, kasan mai ya haɗamu kuwa? Ya Damir ba shi da maƙiya kamata." Labarin abin daya faru a tsakaninsu ta yi. Ta share hawaye tana faɗin,"Wannan dalilin ya sa ya gane ki baya ƙaunar ganina, tun lokacin da abin ya faru ya riƙo ni, na yi nesa da shi, amma da suka dawo Marwana ta sanya rigimar sai ya bani aiki."

Shiru ya yi cikin tsanannin tausayi yana kallonta. "Haka kika sha wuya Nasreen? Tabbas ban ga laifin ki na kin amincewa da wani namiji ba. Farouk azzalumi ne ya cuce ki. Haka WASU MAZAN suke ɗaukar mace ba a bakin komai ba, bayan sun manta Allah shi ya sanya mu yi aure, kuma ranar gobe kiyama sai ya yi alƙalanci a tsakanin. Duk wanda ya cuci wani sai Allah ya saka masa. WASU MAZAN suna aure ne don kawai sha'awa ba sa ɗaukarsa a matsayin bauta."

WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.

*WASU MAZAN*

BOOK 2

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 26

Shiru ya yi cikin tsanannin tausayi yana kallonta. "Haka kika sha wuya Nasreen? Tabbas ban ga laifin ki na kin amincewa da wani namiji ba. Farouk azzalumi ne ya cuce ki. Haka WASU MAZAN suke ɗaukar mace ba a bakin komai ba, bayan sun manta Allah shi ya sanya mu yi aure, kuma ranar gobe kiyama sai ya yi alƙalanci a tsakani. Duk wanda ya cuci wani sai Allah ya saka masa. WASU MAZAN suna aure ne don kawai sha'awa ba sa ɗaukarsa a matsayin bauta. Wannan dalilin ya sanya auren Hausa Fulani yake mutuwa. Suka ɓata mata da shaye-shayen magungunan mata, da kuma supplements don su jawo hankalin mazaje garesu, waɗanda suke jawo musu cutar kansa da wasu cututtukan. Allah sai ya saka miki domin Faruk ya zalince ki."

"Babu komai na bar shi da Allah." Ta ce tana kallonsa.

Shiru ya yi yana tunanin Damir ya cancanta ya aureta, kamar yadda ya hango kishinta. Haƙiƙa in dai haka ya faru shi ne ya dace ya aureta, to kuma shi da ya kamu da sonta ya zai yi? Domin sam bazai iya haƙuri da ita ba, zai ci gaba da ƙoƙarinsa idan Damir girman kansa da izza ya hana shi fahimtar yana so ta sai ya aure ta."

Ire-iren tunanin da yake yi, har suka hana hirar tasu ba ta yi armashi ba, saboda jikinsa ya yi sanyi sosai.

Nasreen data ta fahimci haka dai ta yi shiru tana kallonsa. Sallama ya yi matata tafi gida zuciyarsa cunkushe da tunani.

Da daddare kasa bacci Damir ya yi, duk yadda ya so ya kwanta abin ya ci tura. Da ya kwanta sai ya rinƙa tuna abin da ya faru. Ganinta yake a matsayin mai son kanta. Wannan dalilin ya sa yake jin haushinta sosai.

Da ƙyar ya samu bacci ya kwashe shi. Da safe sai ya tashi ba ya jin damuwar sosai, sai dai mugun haushinta da yake ji.

A ranar an ta shi da ruwa sosai domin tun safe ake ruwa, kasancewar watan ogus ne.

Da ruwan ya lafa ta samu ta je gurin aiki. Tana isa aka tsuge da ruwa. Haka aka wuni ana ruwa har lokacin tashi ya yi, Amma ruwa wa ake zubawa tamkar da bakin ƙwarya.

A tunaninta sai ruwan ya tsaya za a tafi, ashe duk masu abin hawa sun tafi. Dama a ranar Ingawa bai zo ba, saboda zazzaɓin da ya tashi da shi.

Ganin ruwan ya lafa, sai ta sauko ƙasa taga duk sun watse. Fita ta yi daga get ɗin ta fara tafiya tare da kunna lemarta.

Tana cikin tafiya Damir ya zo zai wuce ta. Ba tare da ta lura da shi ba ta ci gaba da tafiya.

Tun daya fara tafiya ya hango ta tana tafe da sauri. Gajeren tsaki ya ja yayin da zuciyarsa ke kimtsa masa ya rage mata hanya. A maimakon ya bi abin da take kimtsa masa, sai ya rage gudun motar. Yana bin bayanta a hankali har sai da suka zo gurin da ruwa ya taru. Da sauri ya ƙarasa gurin, ya watsa mata ruwa sannan ya wuce yana murmushin mugunta.

Nasreen da ba ta san da haka ba, ji ta yi ruwa ya wanke mata fuska har kayanta. Saboda rashin sanin faruwar hakan sai kawai ta firgita, ashe kwalbati ne kusa da ita ta faɗa.

Ƙara ta saki tana kiran sunan Allah! saboda hannunta da ya amsa ƙas! Sannan ta ji ciwo a hannun da gwiyar ƙafarta.

Da ta yi ƙoƙarin ta tashi dai ta kasa kawai sai ta saka kuka. A zuciyarta ta sanya ko mai Marwana za ta yi mata, ba zata ƙara zuwa aikin ba.

Wani irin haushi da takaici ya kamata, har ta ji daga yau babu sauran ragowa a tsakaninsu.

Ganin ta kasa tashi ya sanya ta tsaya kawai tana hawaye. Wani mai mashin ya zo wucewa ya ganta a cikin kwalbatin. Shi ya taimaka mata sannan ta miƙe ta hau mashin ɗin.

Asibiti ya kaita jin tana ta kuka da hannunta. Ko da suka je aka sanar mata da ta yi tsaguwar kashi. Rintse idanunta ta yi tana jin tsananin zafin yana shiga ƙwaƙwalwarta. Kallon hannun ta yi yadda ya fara kumbura.

"Za mu yi miki ɗauri bayan mun gama goge ciwon da kika ji."

Kanta ta ɗaga tare da rintse idanunta saboda yadda hannun yake mata zafi.

"Ni zan wuce ki kira gidanku sai ki gaya musu."Ɗan achabar ya furta yana kallonta.

"Na gode Allah ya saka da aikhairi, amma don Allah ka bani wayarka na kira gidanmu, saboda wayata ta lalace."

"Ok," Mai mashin ɗin ya ce tare da miƙa mata wayarsa mai botira.

Mama tana zaune cikin damuwa tana kallon wayarta. "Wai har yanzu wayar Anty Nasreen ba ta shiga?"Zainab ta yi mata tambayar ganin yadda ta damu.

"Tun ɗazu na ke gwada layin, amma baturiya take magana. Ko za ki kira Musa ki Yusuf su dubo ta."

"To ki kira Anty Marwana ƙila suna tare, ko ta san inda take."

"Kuma haka ne bari na kira ta." Ta ce tare da danna numbarta.

Bayan sun gaisa sai ta ce,"Marwana Nasreen ko kuma tare, saboda tun da ta ke aiki ba ta dawo ba, kuma ina ta kiranta baya shiga."

"Ba ta zo ba kuma mun yi waya da ita gab da za ta tashi. Ko dai ruwa ya sanya ta fake a wani gurin?"
Chapter 49 · 0% Book details