Sashe 91
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Farouk, sai da ya ɗauki tsawon shekaru goma sha biyun, sannan ya samu ya haƙura da ita. Matarsa Maimuna ta haihu har sau biyar domin gwarne take yi, kuma ya kula da yaran, domin yanzu yana son yara. Ko su Raihann yana jin labarinsu ta gurin Anty Asiya da bata yin wata ba tare da ta zo ganinsu ba. Sannan ta hannunta yake musu ihsani, duk da Nasreen ta nuna ba sa buƙatar komai. Yana sonsu domin suna da numbarsa, amma cikin su babu mai kira, domin sam ba da ɗaukar sa a matsayin mahaifinsu. Damir suke kallo a matsayin ubansu.
Jin rasuwar baba, sai ya sanya Maimamuna da yaransa suka shirya su je gaisuwa. Sosai ya ji mutuwar Baba abin da ya faru tsakaninsu ya yi ta dawo masa, har kuka sai da ya yi. Godiya ya yi da ya shiryu kafin ya mutu.
A ranar sadakar uku suka je gaisuwa. A gurin maza ya zauna matarsa ta wuce ciki. Zama ta yi babu wanda ya santa. So take ta ga Nasreen da mijinta ya sha suɓutar kiran sunanta. Ya gaya mata har yau babu macen da ta kaita a duniya. Ta san cewa da zai yi mata ko rabin soyayyar da yake mata a yanzu ta yi sa'a. Tun tana jin haushin kiran sunan har ta haƙura domin ta san ba zai daina kira ba. A dalilin hirar da yake mata na Nasreen take saurarensa, tana taya shi jimammin rashinta, har ta samu matsuguni a zuciyarsa.
Damir a lokacin da ya yi sallama sai da ya ji wani iri. Tsawon shekaru bai sanya ya manta da shi ba. Kalonsa ya yi, ganin ya zube ya rame tamkar ba shi ba.
Gaisuwa ya yi cikin tausaya, sannan ya koma gefe ya zauna, yana satan kallon Damir da yake gefensa.
Farouk sai ya ji hankalinsa ya tashi, ya kalli kansa ya muzanta. Ganin yadda Damir ya dawo. Ya tabbata ko Damir ya mutu, Nasreen ba za ta iya auren sa ba, domin babu macen da za ta rabu da shi ta aure shi. Da sauri ya yi ƙoƙarin mayar da hawayen da suka taru gefen idanunsa.
Ganin yadda ya yi sanyi, Damirr ya miƙa masa hannu suka gaisa. Gaisuwa Faruk ya yi masa ya amsa.
Ahmad ne ya fito da kulolin abinci, Marwana na bayanshi suna magana. Wani irin bugawa zuciyarsa ta yi ganin Marwana. "Ashe auren ta ya yi sun zama dangin juna?" Sai ya ji wani irin hawaye. Ya kalli Marwana da yaransu biyu suka riƙe mata hannu, da alama abu suke tambayarta yadda suke magana.
Ahmad duk da rasuwar da aka yi masa, amma yana kallonta cikin tsananin soyayya.
Damir ya miƙe ya kalli Faruk da ya zauna ya yi shiru."Mu je ka yi musu gaisuwa." Ya ce tare da miƙewa.
Babu musu ya miƙe ya bishi ciki. Mamaki yake yi ganin kyawun gidan sun yi kuɗi. Ya ƙara tsorata da lamarin Ubangiji. Tabbas ya yarda bai kamata ace mutum ya yi ma wani gorin arziki ba. Yau ga su Nasreen, da ya raina yake ganin auren shi ne kawai mafita, Allah ya azurta su har sun fishi.
Kiran Nasreen da take zaune gefen Mama ta yi. Tun da matar Faruk ta shigo take bin ta da kallo. Yaran ta kalla cikin mamaki, ganin suna mata kama da Faruk, amma saboda halin da take ciki dai ba ta gasganta ba, kuma ta san babu yadda za a yi ya zo.
Tana ƙudundune cikin hijabi kiran Damir ya shigo. Da ta ɗauka sai ya ce,"Hello baby ki fito za a yi miki ta'aziya."
"Ok," Ta ce ta fita domin a tunaninta 'yan'uwansa ko abokansa. Tana zuwa ya kama hannunta. "Har yanzu ba za ki daina kuka ba? Nasreen wanda ya mutu ya riga ya mutu."
Jikinsa ta faɗa tana kuka ta ce,"Na kasa yarda Baba ya tafi ya bar mu. Ina tuna rayuwar da muka yi da shi. Duk da bai sauke haƙƙinsa ba, ina jin zafin rashin sa saboda soyayyar da Allah yake sakawa tsakanin iyaye."
"Is ok, ki yi mishi addu'a. Ga wanda ya zo ta'aziya ku gaisa."Ya ce mata yana nuna mata Faruk.
Kallonsa ta yi cikin tsanani mamaki. Yanzu ta gasganta matarsa ce. "Ya Damir don me za ka kira ni don ya zo? Ko kana son ka tuna mini abin da suka yi mini da Baba?"
"Ko kaɗan Nasreen gaisuwa ya zo miki. Fuskarsa kawai kika kalla, za ki tabbatar da wanan ba Faruk ɗin da kika sani ba ne."
Farouk da ya rikice ganin yadda ta zama babban mace, irin masu ji da kyau da hutu. Ya buɗe baki cikin rawar murya ya ce,"Na san za ki faɗi haka don Allah ki yafe mini. Nasreen na cutar dake da Baba, amma gani na duƙa ina neman mana yafiya ni da shi. Ki yafe mana mun cutar da ke. Haƙiƙa rayuwa ta koya mini darasi. Kaicona da na kasance daga cikin WASU MAZAN da ba su ɗauki mace a bakin komai ba. Kaicona da na kasance azzalumi ga rayuwar mace na ɗauke ta a matsayin baiwa. Wacce na ke biyan buƙata ba tare da na fahimci darajar da Allah ya ba ta ba. Haƙiƙa na cuci kaina na kasance daga cikin WASU MAZAN masu cutar da mata. Rayuwa ta koya mini darasi. Rashin ki ya sanya na gane sakacin da na yi wa rayuwata. Na rabuwa da mace kamarki. Kaicona ina ma ace duniya za ta ƙara bani zaɓi mu dawo da rayuwar aurenmu baya. Da na zama bawa a gare ki. Na yi kuka na yi dana sanin rikon sakainar kashi da nayi miki da yarana, saboda haka babu shaƙuwa da ƙauna a tsakaninmu. Ina son su, amma ba sa son ganina a matsayin mahaifinsu." Ya ƙarashe maganar yana hawaye sai kuma ya duka ya ɗaga hannunsa.
"Don Allah ki yafe mini kar na mutu da haƙƙinki. Ki yafe mini cutarwar da na yi miki domin duniya ta koyar da ni." Sai ya fashe da kuka tuna haurinta a ciki da ya yi ta durƙushe tana kuka, amma bai kula ba.
Kasa cewa komai ta yi, sai ta fashe da kuka zata tafi. Damir ya riƙo hannunta. "Please ki yafe mishi ya yi nadama."
"Ya Damir ya cutar da ni." Ta ce tare da ƙara sakin kuka.
"Ki yafe mishi Allah ma muna masa haƙuri ya yafe mana."
"Don Allah ki yafe mini, wataƙila na samu farinciki a rayuwata, domin tun da na rabu dake na kasa samun sukuni." Ya furta mata cikin muryar kuka.
"Na yafe maka Allah ya yafe mana."
"Amin na gode." Ya ce tare da miƙewa.
"Damir kai ma ka yafe mini, na wulaƙanta ka da na yi. Sannan ka yafe mini na barin maka ɗawainiyar yaran da na haifa. Duk da ba ni da abin biyanka, amma a shirye na ke don na biya ka saboda ku fahimci ina sonsu."
"Ban yi don ka biya ni ba, saboda na yi don Allah da farincikin rayuwata matata Nasreen."
Rintse idanunsa ya yi, jin sunan da ya kira ta da shi.
Damir waya ya fito, ya kira yaran duka da kuma Ahmad har da Marwana. Suna fitowa suka ganshi sai suka yi tsaki za su koma.
Ita da Damir suka yi ta ba su baki, sanan suka haƙura. Yaran kuwa da suka zo gaishe sa suka yi.
Farouk sai ya rungume Musaddik da Raihan yana kuka."Don Allah ku yafe mini don Allah."
Sororo suka yi suna kallonsa, duk da sun san Damir ba shi ne mahaifinsu ba.
"Oya go to you Daddy Raihan and Musaddik forgive him." Cewar Damir yana kallon su.
"Mun yafe mishi." Suka haɗa baki gurin faɗin haka.
"Allah ya yafe mana duka." Cewar Damir.
"Matata tana ciki da ƙannin Raihan, tare muka zo gaisuwa." Ya furta yana share hawaye.
Marwana ta shiga ta yi kiranta. Da ta ƙaraso cikin natsuwa ta yi musu gaisuwa.
"Maimunatu ga Nasreen Maman su Musaddik ga su nan." Ya ce ya a kallonta. Kallon kallo suka yi wa juna.
Maimunatu sai da ta tsorata, ganin irin matar da ya aura ya saki. Tabbas ya yi saken da yake cewa. Irin waɗannan matan ya wulaƙanta. Tabbas dole ya kasa mantawa da ita.
"Ki yafe wa Baban Namir, yana kuka sosai yana gaya mini cutarwar da ya yi miki. A dalilin ki ya fita daga cikin WASU MAZAN da suke cutar da mace ya zama na gari. Yana kyautata mini, duk saboda rashin ki da ya yi. Haƙiƙa Ni ma na ga saken da ya yi. Mace irin ki ba abun wulaƙanta wa bace, amma rabon ki auri wani ne."
"Na yafe mishi ba komai." Nasreen ta ce tana share hawaye.
Ciki suka shiga suka yi wa Mama gaisuwa, sannan ya tafi yana cizon yatsa.
An yi bakwai na Baba, sannan kowa ya watse ana masa addu'a. Tun da aka yi rasuwar suka dawo gida sai Nasreen ta kasa komawa yadda take. Hankalin Damir tashi, domin hatta yaran suna ƙorafi. Sai dai ta shige ɗaki ta yi ta kuka tana tuna rayuwarsu.
Ganin tana son cutar da kanta, sai ya shiga cikin ɗakin ya ce,"Yaushe kika fara daina bin umurnina? Nasreen kukan ki zai dawo da shi ne? Baba ya mutu kamar yadda ke ma za ki mutu. Ki yi mishi addu'a a halin yanzu bin da yake buƙata kenan."
Ganin yadda ya fusata sai ta faɗa jikinsa."Ina jin tausayin Baba, ina jin babu daɗi yadda ya yi rayuwa da iyalansa."
"Baba ya tuba kuma Allah zai yafe masa."
"Allah ya gafarta masa." Ta ce tana share hawaye.
"Amin, "Ya amsa tare da haɗa bakinsu. Bayan sun yi bacci sun tashi.
"Za mu fita duka da yara ki shirya."
"To,"Ta ce sannan ta yi hanyar bayi.
Wanka suka yi duka suka ɗau gayu. Ita ce kawai ta shafa mai kawai, ta sanya kwalli. Duk da yar gayu ce amma ina babu wannan.
A mota shi yake tuƙa su suna hira don su ɗauke mata hankali, amma murmushi kawai take yi in suka sako a zancen.
Ganin sun je gurin shaƙatawa sai ta yi mamaki."Yes mu shiga so na ke yi anan ki manta komai. Kuma ki yi mini alƙawarin za ki rinƙa tuna baba ne ta hanyar masa addu'a."