Sashe 93
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yusuf yayi murmushi yace, “in ba rik’e amana ba na zama butulu kuma munafuki, ya zamar min dole na kula da ita koda bana so, wannan ya zama kamar wajibi ne saboda mahimmacin da take dashi, amma ina da korafi Yaya.” Yaya Adam yace, “na me ya korafin?.”
“Har yanzu Ameena alfarmar Ammaha nake ci a wajan ta, tana zaune dani zaman hak’uri ne kawai amma badan tana so ba, bata yafe min ba ko nace babu soyayyar ta a zuciyar ta alfarma ce har yanzu. A taya ni rokon ta ta d’aure ta saka soyayyar ta ko yaya take baza tayi nasa sani ba.”
Yaya Adam ya murmushi ya kalli Ameena yace, “to Ameena kin ji.” Tayi murmushi tace, “Yaya ya kasa amincewa ne ko yaushe gani yake kamar har yanzu ban manta baya ba, ni kuma na manta amma tsarguwa ce dashi akan wannan lamarin.”
“Baki manta din ba ai har gobe kina tunawa.”
“Tunawa ya zama dole indai ba loosing memory zanyi ba ya kake so nayi?.”
“Sai ki manta din kawai, badan ciwo bane da nace dama kinyi losing memory din.” Al’ameen da yake kallon su yayi murmushi sosai ganin kawai soyayya ce take d’awainiya dasu yace, “ku bari ku koma gıda sai Kuyi wannan jayayyar, yanzu bamu Umma mu ganta.” Ameena ta mik’a masa Nayla ya karb’a yace, “ma sha Allah, yarinyar kuma kamar Umman ko Adam?.” Adam ya kalle ta yace, “da Ameena yake kama shiyasa kake gani kamar Umma. Allah ya raya ta.” Suka amsa da amin kafin Ameena tace, “Yaya Al’Ameen ina Fiddausi?.”
“Ya fita d’azu, amma ki kije ta maybe ta dawo.” Ameena ta tashi tace, “bara naje gidsn.”
Al’ameen yace, “kin manta da yarinyar.” Sai ta dawo tana dariya ta karb’i ta ga fita Zaytun tana wajan baban ta. Gidan ta shiga mai gadin yake fad’a mata ta fita kafin ta kai ga dawowa gida sai ga Fiddausi a mota an shigo gidan Ameena ta kalle tana murmushi a bayyane tace, “Fiddausi buri ya cika, Allah ya tabbatar zaki rayuwar da kike so amma sai kin sha wahala.” Fitowa tayi daga motar ta rungume Ameena tana kallon ta Ameena tace, “kina abinda kike so wallahi.” Fiddausi tayi dariya suka shiga ciki Ameena tana dariya itama haka suka zauna.
Fiddausi tace, “wallahi bani da damuwar komai a gidan nan Ameena, musamman yanzu da nake da ciki farin cikin da yake nunawa yana saka ni farin ciki nima. Ameena wani wato Allah yayi bazan yi rayuwar da nake so ba sai bayan na sha wahala a rayuwata. Sai bayan na gane banbancin abinda nake so da abinda ya kamata naso, shine ya kaini gidan Alhaji Bello kinga ai a nan nayi hankali daga baya in na tashi addu’a sai nace Allah na gari nake nema.” Ameena tayi murmushi tace, “sai Mun sha wahala dai, ni kaina ban d’auka zan samu rayuwar farin ciki a gidan Yusuf ba, sai gashi na samu farin cikin da ban yi tunanin samun sa ba wallahi.”
Fiddausi tace, “komawar ya zama miki alkhairi watakila da shi kika aure da baza ki samu farin ciki ba, da kika bawa Allah lamarin ki gashi yanzu komai ya zama tarihi.”
“Kamar ke, da kika yi nadamar da gaske kika tabbatar kinyi kuskure sai Allah bai sake baki ibrshim ba ya baki wani na daban Wanda yake da nagarta da komai kamar Ibrahim din ko nace yana fi ibrshim. Daman Allah ya rubuta Ibrahim da Ruky zai rayu dole ki bar gidan sa ta shigo, Ke kuma dole ki auri Bello ki san kinyi kuskure sannan sai ya baki jin dadin dan ki tabbatar da sai an had’a biyun ake samun kwanciyar hankali.”
Fiddausi tace, “bari kawai Ameena. Wanda bai yarda da Allah ba ai yana cikin wani hali, cikin lokaci kad’an ya bayyana mana abubuwa da yawa mun gani. Sai dai muce Alhamdulillah yayi mana ni’ima. Abu d’aya ke damuwa a wani lokacin shine Amir. Ina son yaron nan sosai amma sun yi min nisa yanzu.”
“Rukayya ta zama matar manya fa ina fad’a miki tayi kyau kin san fatar ta da d’aukar hutu wallahi baza ki gane ta ba.” Fiddausi tayi dariya tace, “ina son zuwa abujan wallahi to aikin ne ya dawo kano gabad’aya shiyasa zuwan yake wahala.”
“Ai rana zamu saka dukkan mu muje mu dawo a ranar dan jirgi mutum d’aya ma ta biya mu ne.” Fiddausi tace, “hmm bari kawai. Babu abinda zamu cewa Allah sai godiya dan ni wallahi ban d’auka zan sake samun farin ciki irin wannan ba.”
“Ba’a fitar da rai daga rahama Alalh.”
“Ni zan baki labari” ta fad’a tana dariya suka tafa suna hira cikin farin ciki a zuciyar ko waccan su.
Sai bayan i’sha suka tafi Ameena sai murmushi take tun a mota yana kallon ta yana Murmushin shima yace, “wai lafiya kike? Wanne albishr aka yi miki haka?.” Tayi dariya kawai bata ce komai ba a haka suka koma gida Zaytun tayi bacci haka Nayla tana tsaye tana shafa turare a jikin ta ya shigo yana kallon ta ta madubin yace, “farin ciki yayi miki yawa yau, meye sirrin?.” Tayi dariya tace, “wato Allah gwanin hikima ne Beb, ya riga ya tsara rabuwar mu dakai a wancan lokacin shine silar canjawar komai, ya tsara dawowa ta wajan ka shine alkhairi koda bana son dawowar sa na dawo saboda rabon Nayla, Allah ya tsara min sabon aure ba alkhairi ne a wajena ba dawowa wajan ka shine alkhairi. a daya bangare Fiddausi sabon aure shine alkhairi a rayuwar ta.”
Ya rik’e hannayen ta guda biyun yana kallon ta yace, “Rayuwar mu darasi ce akan mutane, da farko babu kwanciyar hankali amma daga k’arshe an samu kwanciyar hankalin. Wannan kamar izina ce akan masu tunanin komawa gidan mijin da aka bari babu alkhairi domin damuwar da ta fitar dake ita zaki koma ki sake tararwa, eh akwai hakan sosai domin wasu chanjin na lokaci ne, Wanda Allah ya zab’a kuma inya canja ya canja kenan har abada, bazai sake kallon baya ba zai cigaba da amfani da canjin da Allah yayi masa.” Ta girgiza kai tace, “ban tabbatar ba sai da zaman mu yayi nisa, a baya gani nake kawai farkon zama ne zaka koma yadda kake. Amma gashi addu’a tayi tasiri komai ya zama tarihi.”
Yayi murmushi yace, “har yanzu alfarmar Ammah nake ci?. Kina gani ta silar soyayyar ki na samu ciwon da dashi zan mutu, wannan ciwon kan shine ya kusa sakawa na zama mahaukaci.” Tayi dariya tace, “dadi nake ji in nasan kana sona sosai fiye da baya. Murna nake farin ciki nake ji in nasan kana sona fiye da yadda kake son kanka, ina son a soni sosai, shiyasa nake jin dad’i a duk lokacin da ka furta kalmar ina sonki.”
“Ni kuma haushi nake ji in a tuna yanzu bakya sona. Zuciyata har rawa take in na tuna Beb alfarma nake ci take zaune dani, bayan tana gani sonta har ciwo ya saka min.”
“Wai haka nace maka bana sonka.”
“Haka kike ce mana.” Tayi dariya tace, “to yanzu na canja, ina sonka har zuciyata.” Ya girgiza kai yace, “kin fad’a ne dan naji dad’i amma ban yarda ba.”
Ta sake yin dariya shima dariyar yake yana kallon ta yace, “Gaskiya ne ai. A daure a bani gurbu soyayyar da nake miki zata fi haka in nasan kina sona.”
“Me zanyi da zaka yarda?.”
“Sai lokacin da kika fad’a min da kanki ba tare dana tambaye ki ba.”
Ya sake yin murmushi yace, “ai kuwa zan fad’a maka.”
“Ina jiran ranar tazo zanyi kowa murna.” Ta bishi da kallo shima kallon ta yake ganin sai kallon sa yake kamar mai duba wani abun a jikin sa yace, “ya dai?.”
“kayi budurwa?.” Ya kulle ido ya bud’e yace, “Wallahi har kin saka gabana ya fad’i, babu wannan labarin a tahirina a yanzu. An goge wannan tunanin ki ma daina shi.” Zatayi magana yace, “kar kice haka nace miki a baya ma, wancan lokacin daban wannan lokacin daban ya kamata ki dinga banbancewa.”Tayi dariya sosai tace, “kyaun da kayi ne yasa nasan ko baka ce kana so ba za’a ce Ana sonka.”
“An kuwa ce din, kawai dai bazan sake kallon wata mace a matsayin mace ba sai ke.” Ya bud’e baki zatayi magana yace, “dan Allah kar kice haka n fad’a a baya.” Tayi dariya sosai shima yayi dariya ta rungume shi cikin farin ciki da jin dad’i shima haka yana ji a zuciyar sa Ameena itace rayuwar sa.
Alhamdulillah!
19/july/2024.
_Kuskuren da muka yi a cikin labarin nan Allah ya yafe mana, abinda muka rubuta daidai Allah ya bamu lada. A nan labarin MAI DAKI ya tiqe Allah yasa an amfana da Sakon da yake cikin labarin a kuma yi amfani dashi yadda ya dace._
_Shawara, gyara, kuskure, duk k’ofa a bud’e take ga wanda suke ganin ya kamata ayi magana dani, vip, regular grp, arewabooks da y’an bati ma duk k’ofa a bud’e take ina jiran kowa zan karb’i kowa ta ko wacce fuska domin Karb’ar shawara ko gyara ko a nuna min kuskurena. Ina ji daku masoyana a ko da yaushe ina matuk’ar alfahari daku kune ni nice ku, Allah ya saka muku da alkhairi ya bar zumunci dake tsakanin mu ya had’a fuskar mu har a aljanna._
_Nana Haleema taku ce a ko yaushe, a jira ta cikin sabon labarin ta da zai zo nan bada jimawa ba in sha Allah. Ina sonku ina kuma ji daku masoyana, Allah ya bar qauna amin._
#Nana Haleema
#Mai daki
#End
#book 1&2&3
#