Sashe 69
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Zata kammala ne ai, balle ma kin mayar da hankali sosai a kai.” Tayi murmushi kawai Anti tace, “Zaitun ba’a dawo ba kenan?.” Kai ta d’aga kawai Aunty ta kalle ta tace, “Ameena na tambaye ki?.” Ta kalle ta tace, “eh mana Aunty.”
“Amma kar ki kalli tambayar tawa da wata fuskar kawai ki amsa min.” Ta d’aga mata kai tace, “zaki iya komawa gidan Yusuf in kika tabbatar ya canja duk abinda akayi a baya baza’a maimaita ba sai kadan?.”
Ameena ta sauke numfashi tace, “ni bama wannan tunanin ma.” Anti tace, “nasan bakya yi din ai, shiyasa na tambaye ki zaki iya komawa in akace ya canja daga yadda kika sa shi ya koma miki sabo fresh kamar lokacin da kike amarya?.” Tayi shiru na wani lokaci kafin tace, “ai bazai ma canja ba, yaje ya k’arata ni bana son zancen ma gabad’aya.”
“Kin kasa bani amsa kawai.”
“To ban san me zance bane ba.” Anti tace, “amsa kawai zaki bani.” Ameena tace, “inda da gaske zai canja din baza’a maimaita abinda ya wuce ba zamu zauna lafiya babu cuta babu cutarwa zan koma Aunty, zan koma kodan saboda Zaytun ko badan shi ba zan zauna saboda ita dan tana son mahaifin ta sosai indai yana waje bata cika nemana ba. Raba su zan cutar da ita sosai.”
Aunty tayi murmushi tana kallon Ameena kafin Anti tayi magana Ameena tace, “balle ma bazai komai ba shiyasa bana kawo shi cikin zuciyata, yayi rayuwar sa nayi tawa na tabbata Yaya Al’ameen zai rik’e min Zaytun ko bana da rai.” Aunty tace, “Gaskiya ne, amma koda ya rik’e Zaytun in ta girma sai dai ace Zaytun Yusuf ba Zaytun Al’ameen ba kin san da hakan ai ko?.”
“Na sani mana, ko yanzu da sunan sa ake mata amfani a makaranta.”
“Ameena Nidai zuciyata ta amince da Yusuf ya gane kuskuren sa wallahi, kin san wani lokacin baka gane kayi kuskure sai wani abun ya same ka kake banbance ashe a baya ka tafka asara wacce kafin ka mayar da ita zaka jima. Ki kalli k’awar ki Fiddausi da kike bani labari, sai a yanzu tasan tayi kuskure kuma ke kanki kin amince da ta tuba har cikin zuciyar ta koma meye yanzu baza ta sake gangancin aikatawa ba. Har kike cemin badan Rukayya ba da kince kina so Ibrahim ya mayar da ita gidan ta dan tayi nadama sosai ta kum tuba har zuciyar ta, kina so ace ta koma wajan Ibrahim ko badan komai ba saboda d’an ta haka ne ko?.”
Ameena tayi shiru bata amsa ba Anti tace, “kin yarda a baya tayi kuskure kuma yanzu ta gane kuskuren ta gyara kuma kin amince da ta gyara d’in tunda gashi kina so ta koma gidan mijin ta, meyasa shi baki yarda ya zai gyara kuskuren nasa ba?, kodan har yanzu akwai haushin sa da kike ji a zuciyar ki?.” Ameena ta kalle ta tace, “Anty kuskuren Yusuf yafi na Fiddausi a wajena, Yusuf bazai canja ba wani abun yana sene yake aikatawa halin sane ba wani abun ba kuma hali baya canjawa.”
“Nasan halin sane ai, shiyasa nace miki akwai abinda dole sai ya sake faruwa in kika koma saboda hali ne baya canjawa, amma wallahil azim ina tabbatar miki da cikin kashi d’ari na abinda ya faru a zaman ki dashi na baya tamanin zai ragu iya ashirin ne zai rage kawai saboda bazai sake gangancin aikatawa ba sboda kar ki sake nisa dashi. Ko a yanzu nasan kin tabbatar da Yusuf yana sonki so bana wasa ba, namijin da zai durkuss a gaban ki yana kuka kamar wacce ta haife shi akan kawai ki yafe masa ko ki koma gidan sa ki sake kallon sa in akace akan so da kuma bada hak’uri ya aikata hakan.”
Ameena ta girgiza kai tace, “ni nasan masifar da na shiga a gidan sa da Anti.” Tayi murmushi tace, “nima bance ki koma ba ai ina fad’a miki ra’ayina ne inda nice wallahi wajan sa zan koma, in na auri wani na raba yarana wannan tana nan wannan tana can gwara ace shi kad’ai ne uban yarana gabad’ayan su. Har Bauchi yaje akan yaya ta baki hak’uri tun kafin yazo nan,Nidai zuciyata ta amince da ya canja wallahi amma ko meye shine yayi wasa sa damar sa kina da ikon da zaki ce baza ki koma ba.”
Ameena tayi shiru bata ce komai ba tana tunani kafin ta sauke numfashi tace, “Gwara a barshi kawai wannan da aka samu yasa sai mutuwa ce zata raba mu.” Aunty tayi murmushi tace, “Amin Amaryar Al’ameen.” Sai ta kasa murmushin da ta saba in akace amaryar al’ameen ta kalli Aunty ta dan saki fuska kawai amma batayi murmushi ba.
Yusuf tunda ya farka yak’i magana sai kallo kawai da yake bin su dashi dakyar aka bashi tea yasha a safiyar yana zaune yana shan tea din Mubakar ya shigo ya kalli Abbah da yake zaune yace, “Abbah ga sark’ar ka.” Ya fad’a yana mik’a masa ya karb’a ya kalle shi yace, “an ina ka samo ta?.”
“Jiya aka kama matar sa Asiya taje kasuwa zata siyar akan miliyan d’aya da rabi, saka sanar da Yusuf ya tabbatar sark’ar kace sai yace naje na karb’o sarkar.” Ammah tayi dariya tace, “Da gaskiya manager bank din nan da yace satar tasu ma ta k’ananun b’arayi ce, yanzu wannan sark’a ko yaro a yasan tafi kudin da ta siyar da ita.”
Abbah ya kalli Yusuf da yake kallon wani wajan daban kafin ya kalli Mubakar yace, “yanzu tana ina?.”
“Na saka a sake ta, da wallahi so nayi taje prison ko na sati ne tausayi ta bani tana ta kuka ga hannun ta a karye shiyasa na kyale ta.”
“Gwara da ka kyale ta din ai yafi.” Usman ne ya shigo da sallama aka amsa suka gaisa da su Ammah ya kalli Yusuf yace, “ya jikin?.” Kai y d’aga masa kawai amma baiyi magana ba yace, “Zan wuce akwai aikin da zanyi anjima zan dawo.”
Yusuf ya kalle shi yace, “ka tsaya ka raka ni wani waje.” Yadda maganar take fita a sark’e sai da su Ammah suka kalle shi dan baiyi magana ba sai lokacin Usman yace, “ina kuma zamu je yanzu? Bauchi zamu koma ko gidan Adam?. Yusuf ya kamata kayi hak’uri da Ameena ka cire ta daga zuciyar ka kawai indai kana son ka tsira da Lafiyar ka.” Yayi murmushi yace, “riga ce da zan saka a lokacin da naso kuma na cire a lokacin da naso Usman? Zuciya ce fa ban San taya zan cire a lokaci d’aya ba kamar yadda kake fad’a. Ka tsaya muje dan Allah kaine kawai kayi hak’uri dani kake saurarona.”
Usman yace, “naji, amma na fad’a maka akwai abinda zanyi yanzu, sannan ina ma zamu je?.”
“Zamu je duk inda ya kamata ma ace mun je” ya fad’a yana sako k’afar sa zai sakko Usman ya dakatar dashi yace, “ka zauna naje na dawo sai muje duk inda zamu je.” Yusuf yace, “ka tabbatar zaka dawo?.” Cikin taussyin da yace, “zan dawo.” Usman ya kalli su Ammah da suke kallon su ya fita baice komai ba shima Yusuf din sai ya mayar da idanu ya kulle.
Adam yana fita gidan Al’ameen ya shiga ya samu baya nan ya dinga yi masa waya bai d’auka ba yayi tsaki ya zauna yana zaman jiran sai daga baya sai gashi ya dawo ya kalle shi yace, “tun d’azu nake kiran ka baka d’auka.” Suka shiga cikin gidan Al’ameen yace, “Naje dubiya ne wallahi, a nan naga Zaytun ma a hannun wani yaro ashe kanin baban ta ne suke cemin babban ne a kwance babu lafiya, da zan je na duba shi ka to kana ta kira na sarkin masifa shiyasa na dawo.”
Adam yace, “Yusuf din ne asibiti?.”
“eh, haka akace min wai tun jiya.”
“Allah Sarki. Muyi maganar da ta kawo ni yanzu.” Al’Ameen yace, “kafin wannan Adam, kana ganin Ameena bata son mijin ta kuwa?.” Ya dago ya kalle shi sosai yace, “bata son sa, ko tana son nasa ma baza ta koma masa ba. Kai dan baka San waye shi bane shiyasa a jiya naga ya baka tausayi.” Yayi murmushi yace, “kai ma ya baka tausayi ba ni kad’ai ba. Abinda na gani duk abinda zai saka namiji kamar sa kuka har ya zube guiwa a k’asa a gaban mace yana neman afuwar ta ba abu bane kad’an Adam. Gazawar takai gazawa, mace ba mahaifiya ba ka zube kana bata hak’uri kana kuka ki nadamar k’arya kayi sai an kalle ka an sake kalla. Ganin hakan sai jikina yayi sanyi sosai domin itama Ameena akwai feeling a tare da ita akan shi kawai dai abinda yayi mata take tunawa.”
“Nima ai abinda yayi mata nake tunawa bawai yana sonta ko babu son ba.”
“Eh haka ne, amma ana kuskure ana kuma gyara kuskuren a lokacin daka fahimta, ya gane kuskuren sa kuma ko nan gaba akace ya sake abinda yayi Allah bazai yi ba.”
“Tsaya, yanzu me kake nufi da wannan jawabin naka?.” Al’ameen yayi murmushi yace, “indai Ameena tana son zama dashi a karo na biyu Adam ni mai iya sake hak’ura da ita ne a karo na biyu na bar masa ita. Amma in ba itace ba ita tace tana so ba za’a cigaba da shirye-shiryen biki.” Adam ya harare shi yace, “son da kake mata dmaan bashi da auki? Yanzu har kana da bakin da zaka ce zaka iya sadaukar da ita ga wani namijin daban?.”
Ya girgiza kai alamun eh yace, “son da nake mata ne ya saka zan iya hak’ura da nawa farin cikin na bata Adam. Ni yarinyar su ma nake tausayi wallahi, tana son mahaifin ta sosai.” Adam ya bishi da kallo yace, “to bata son sa, bazata koma ba. Ka tsaya muyi magana akan auren ka da ita ka daina kawo min batun tsohon mijin ta dan Allah.” Al’ameen yayi murmushi yace, “to sirkina, Ina ji.” Dariya Adam yayi wacce bai shirya mata ba shima dariyar yayi kafin su tattauna akan batun auren da yadda Adam yake so komai ya kasance Al’Ameen ya amince da hakan shima sosai kafin Adam ya tafi.
#Mai room
#Book3
#Nana Haleema
#Paid
#500.