Sashe 28
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zakiyya ta girgiza kai da mamaki lamarin da kuma tsoro tace, “zamu dinga addu’a in sha Allah babu komai, zamu samu wayar ta Mama kar ki damu.” Mama ta girgiza kai ta wuce d’aki ta bar Zakiyya a wajan itama ta juya ta fita jikin ta a sanyaye tunanin ta ya tafi wajan meye ya samu Fiddausi ba’a samun ta a waya…?.
#Mai daki
#Book3
#Nana Haleema
#Paid
Book3
017
Yusuf ya canja gabad'aya ya rame sosai ko yaushe yana gıda babu inda yake iya zuwa ko yaushe ka ganshi cikin tunani yake shi kansa bai San abinda yake damun sa ba balle ya nema wa kansa magani. Yana zaune a kan kujera yayi shiru yana tunani cikin kwanakin da ya rufe idanun sa Zaytun yake gani da Ameena amma ya rasa me yake jawo hakan. Ga zuciyar sa ta dinga bugawa a duk sanda ya tuna su sai yaji ruwa yana k'ok'arin taruwa a cikin idanun sa.
Asiya ce ta shigo tana kallon sa ta zauna tace, "My love me yake damun ka?." Ya kalle ta ya zauna sosai yace, "babu komai." Ta tab'e baki ya sake kallon ta yace, "har kin dawo daga bikin?." Ta cire mayafi tace, "eh wallahi, gidan zafi shiyasa na dawo." Baice komai ba yayi shiru yana kallon tv badan yana fahimtar abinda ake cewa ba sai dan ya tsani doguwar magana da ita.
"My love ina buk'atar a canja min mota gaskiya." Ya d'ago ya kalle ta yace, "har yaushe aka siyi motar da za'a canja miki?."
"Ai ko jiya aka siya dan nace a canja min yau ba wani abun bane ba Tunda akwai kud'in, kawai in za'a canja a canja in baza'a canja ba sai a fad'a min."
Banza yayi mata bai amsa ba ganin bai amsa ba sai tace, "Sannan kayan abincin gidan mu ya k'are fa, wai kana sane da wata yayi nisa amma baza a siyi abinci a aikata su Umma ba, Haba wannan fa ba daidai bane kana gani ga azumi yana gabatowa haka za'a shiga Ramadan din sai na tuna maka zaa kai musu abinci?."
Yusuf ya kalle ta yace, "na manta ne amma yanzu zan saka a kai musu." Asiya ta girgiza kai cikin b'acin rai tace, "in su Ammah ne baza ka manta ba." Da sauri ya kalle ta yace, "ke wai ban miki warning akan sakoAmmah a cikin maganar mu ba? Meyasa baki da mutunci ne wai?. Iyayena daidai suke da iyayen ki ne?." Ta murgud'a baki bata ce komai ba shi kuma yayi tsaki ya mik'e dan da ace ta tanka masa da Allah kadai yasan abinda zai mata ya bar wajan.
Sama ya hau ya tsaya a bakin taga yana kallon mai shigowa, ya rasa meyasa ya kasa d'aukar mataki akan Asiya duk abinda yake masa, ya rasa meyasa take masa abinda taga dama yake iya shiru ya kyale ta. Ya sauke numfashi ya kalli wajan tagar sosai ganin mata suna shigowa harabar gidan wajan Ameena, ganin ana ta magana dasu sai ya bud'e window din yace, "Baba Lafiya?." Baba ya d'aga kai ya kalli Yusuf yace, "Alhaji wajan Hajiya suka zo."
Yusuf yace, "barsu su shigo" ya fad'a yana kulle window din ya sakko shima dan yaga kamar ba Lafiya ba. Yana sakkowa sun gama shigowa falon d'aya daga cikin su ta nuna Asiya da take zaune tace, "gata nan, wallahi itace ta d'auka na ganta ganin idona, ashe matar gidan nan ce." Asiya ta mik'e tana kallon su duk da taji tsoro sossi amma bata nuna ba tace, "ku kuma lafiya kuka shigo min gida? Su waye ku?."
D'aya daga cikin su tace, "ai nasan kin gane ni kuma wallahi ke kika d'auki zoben, ko ki fito dashi ko kuma na had'a ki da y'an sanda yanzu wallahi." Yusuf da ya ke kallon su yace, "Dan Allah ayi abun a nutse, Meya faru?." Wacce take maganar tace, "ai naga tazo da rainin hankali, kuma wallahi in bata fito da zoben nan sai dai hukuma ta raba mu."
Asiya tace, "an ina na sanku har muka had'u da zan d'aukar muku zobe? Dan kun raina min hankali kaf gidan bikin a rasa wacce za'a ce tayi sata sai ni? Ku kalle ni ku kalli gidana Kun san nafi k'arfin nayi sata wallahi."
"Ke da kika ce baki san inda muka had'u ba taya kika san a gidan biki muka had'u?."
Asiya ta dan rud'e amma bata nuna ba ta kalli Yusuf tace, "My love ban san wad'annan mutanen ba akan me zasu zo gida na suna cemin barauniya? Nayi kama da mai sata ne?." Wacce take tsaye bata ce komai ba ta kalli Yusuf tace, "Zoben da ake magana a kai nawa ne, a kalla kudin sa ya kai miliyan biyu da wani abun. Wallahi in bata fito da zoben nan ba hukuma ce zata raba mu."
Yusuf yace, "ku ya akayi kuka san itace ga dauka Tsakani da Allah?."
"Saboda na kamata tana bincika min a jaka, dana kamata sai tace min tissue take nema ban d'auka barauniya bace na d'auka mace ce mai aji wacce dan ta duba jaka ta ba komai bane ashe mai halin b'era ce. Ina kwatanta ta aka ce min itace kuma halin tane na biyo ta ta bani, wallahi ko ki bani zobe na wallahi ko ki kwana a wajan y'an sanda."
Asiya tace, "babu abinda zan bayar saboda babu abinda na d'auka." Wacce take magana da Yusuf tace, "haka kika ce?." Asiya tace, "eh haka nace." Tayi kwafa ta juya ta zata fita Yusuf yace, "dan Allah ki tsaya abun bai kai haka ba" ya kalli Asiya yace, "in kin san kin d'auka ki fito musu da abin su."
"Yanzu my love kaima kana tunanin na d'auka din ne? Babu abinda na d'auka balle na bayar barazanar su baza tayi min komai ba."
Basu ce komai ba akwai suka juya suka fita Yusuf ma bashi da ta cewa ya kalli Asiya yace, "Asiya" tayi saurin dakatar dashi tace, "ban d'auki komai balle na bayar ka gane ko?" Tana fad'a ta bar wajan ya tsaya ya rasa abinda yake masa dad'i ya zauna a wajan yana tunanin tsautsayin da ya kai shi auren Asiya a cikin rayuwar sa gabad'aya.
Kusan mintina ashirin da fitar su sai ga su sun dawo da y'arr sanda mace suna shigowa Asiya na sakkowa da jaka da mayafi zata fita tace, "Yauwa gata nan." Jin magana ya saka Yusuf tasowa ya fito yana kallon su yace, "Officer Lafiya?." Matar ta kalle shi tace, "ta d'auki abu kuma tayi gardama shiyasa na nuna mata bani da mutunci wallahi sai ta fito dashi."
Asiya ta tsorata ta kalli Yusuf tace, "my love babu abinda na d'auka." Yar sandar tace, "Ko ki fito dashi a yanzu ko kizo muje can sai ki fito dashi." Ta rik'e Yusuf tace, "kar ka bari a tafi dani ban d'auki komai ba Kaga kuna ciki ne dani dan Allah kar ka bari a tafi dani."
Yusuf ya kalle ta yace, "Dan Allah Kuyi hakuri abin duk bai kai haka ba, matar aure ce kuma juna biyu ne da ita zubar da mutunci ne ace an ganta a police station. Dan Allah ku tsaya muyi magana ta fahimta."
"Ai ta nuna taurin kaine shiyasa na nuna mata na fita iya iskanci. Da ta tashi satar ai ta manta ita matar aure ce tayi dan haka nima zan manta da Hakan, officer ki kama ta muje kawai."
Yusuf yace, "baza'a yi haka ba, dan Allah ku zauna muyi magana wacce zamu fahimci juna." Officer tace, "Ai matar taka ce take da taurin kai da basai nazo nan ba, da ta amsa ta bayar duk da ba haka ba amma ta k'i."
"Nifa babu abinda na d'auka, duk abinda za'a yi sai dai ayi amma ban d'auki komai ba babu wanda zai kama ni kuma." Yar Sandar ta kalli Yusuf tace, "kayi hak'uri kawai zamu je da ita." Yusuf yace, "baza'a yi haka ba dan Allah kiyi hak'uri" ya kalli Asiya yace, "Asiya ki saita harshen ki."
"Bazan saita ba, haka kawai azo har gida ayi min sharrin sata a gaban ka kuma ka yarda?. Babu Wanda ya isa ya kama ni kuma wallahi sai nayi k'arar su suma." Yusuf ya rasa abinda zai ce sai kallo kawai yar sandar tace, "indai kin san kina da gaskiya kizo muje yanzu zaki dawo." Asiya ta kalle shi taga yayi shiru sai tayi tsaki tace, "muje din sai me" ta fad'a tana bin bayan su suka fita shi kuma dai Yusuf yana tsaye yana kallon su domin kuwa gwara ma aje da ita din watakila tayi hankali nan gaba kar ta sake dan ya tabbatar tayi.
Sai bayan sun fita ne ya tuna ya kamata ya bisu ya fito amma kafin ya hau motar ya fita ya neme su ya rasa. Waje ya samu kawai ya faka ya tsaya ba tare da yaje ko ina ba zuciyar sa tana fatan Allah yasa suyi mata dukan tsiya kowa ya huta. Yana cikin motar Abbah ya kira shi yana d'auka yace, "kana ina?." Yusuf yace, "ina mota."
"Yanzu DPO din police station din nan na cikin gari ya Kira ni wai har gida an kama matar ka tayi sata, kai kana ina?."
"Abbah a gabana suka tafi na rasa me zanyi, nace ta fad'a in ta d'auka tak'i sai rashin kunya take musu shiyasa ban hana su tafiya da ita ba gwara taje tayi hankali." Abbah yace, "Baka da hankali ai, malam ka wuce kaje ka fito da ita In ma ta d'auka ka d'auki alhakin biyan kudin zoben ku dawo gida." Da to kawai ya amsa ta kashe wayar yana d'auki hanyar station din.
Yana zuwa yaga Asiya a zaune a gaban DOP ana magana tayi shiru ta sunkuyar da kai ga zobe nan kato a kan table din sa. Ganin Yusuf ya shigo ya samu waje ya zauna suka gaisa da shi ya kalli Yusuf yace, "ai ban san matar ka bace sai da tayi min bayani da cikakken sunan ka gashi bani da lambar ka dole na kira Alhajin ka na sanar dashi."