← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 93

Sashe 54

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ban tab'a daina son Ameena, ban tab'a jin son Ameena ya fita daga zuciyata ba, wallahil azim ko da muna tare ina son Ameena son da ban yiwa Asiya shi ba" Yusuf ya fad'a yana kallon Usman da yake kallon sa shima yace, "karya ne wallahi, ban yarda ba, babu macen da ake  so ake qauna za'a yi mata abinda ka yiwa Ameena. Ka daina son Ameena a lokacin ka hango Asiya ka dinga mata wulakancin da ko kai akayi baza ka kawo akwai soyayya a zuciyar wanda ya aikata maka ba wallahi."
"Wallahil Azim a rana d'aya ban tab'a jin son Ameena ya ragu daga zuciyata ba, nasan nayi kuskure wani abun ina sane wani abun bana sane, wani abun halina ne ba asiri bane ni na sani. Bana bincike akan duk abinda Asiya zata fad'a min kawai ina hawa kai na zauna ne nayi hukunci kawai ba tare da na bincika na gano gaskiya ba. Wannan shine kuskurena Usman, nasan na tafka kuskuren da gyara shi zai min wahala amma dan Allah ka taya ni gyara wannan kuskuren na samu Ameena tace na yafe maka komai dan Allah."

Usman yace, "wannan fa duk ihuu kake bayan hari, tun da ya kamata kayi wannan maganar ai ba yanzu ba Yusuf. Ko zuwa wajan Ameena ma kayi zata ga kama raina mata hankali sai yanzu zaka zo bata hak'uri."
"Bazan iya ba a wancan lokacin, ma fad'a maka ina so zuciyata tana so amma gangar jikina sai ta gaza aikata hakan Usman. Ban San me ya shiga kaina ba gangar jikina ita take sarrafa zuciyata, Allah ne kad'ai yasan abinda yake zuciyata shine shaida ta badan babu mai yarda dani" ya fad'a yana kuka sosai Wanda ya bawa Usman mamaki ya zuba amsa ido kawai yana kallon sa ganin kuka yake kamar wanda ya rasa uwa da uba a lokaci d'aya.

"Ka taimaka min Usman naje na bawa Ameena hakuri dan Allah." Ya girgiza kai yace, "Gaskiya bazan je ba, abubuwan da kayi mata bazan iya had'a ido da Ameena nace tayi hakuri akan abinda kayi mata ba gaskiya kayi hak'uri."
"Usman yanzu baza ka iya taimaka min ba?." Usman tausayin da yake ji a zuciyar sa amma baya son nuna masa hakan sai yace, "Bawai bazan iya bane ba Yusuf in na tuna abubuwan da suka faru ne a baya, yarinyar nan har hawan jini ta samu saboda damuwar ka taya kake so na tunkare ta nace tayi hak'uri?."

Kuka Yusuf yake yi sosai Usman duk yayi sanyi ganin namiji kamar Yusuf na kuka abin sam babu dadi gani ko kad'an, ya tashi ya dawo kusa dashi yace, "Ka daina wannan kukan mana Yusuf matata tana gidan nan fa in ta fito taji kana wannan kukan ai babu dadi."
"Ko waye zai gani ban damu ba, burina ka amince min muje mu samu Ameena na bata hak'uri. Na San nayi kuskure babba ya kamata ka fahimce ni ina so na gyara wannan kuskuren da nayi."
"Hak'uri zaka bata ko kuma bikon auren ta zaka je?." Yusuf yaja numfashi sosai hawaye suka dake sakko masa yace, "hakurin shi nake da karfin guiwa a kai, bazan iya zuwa bikon ta ba Usman, bazan iya ba."

Kukan da yake yi yafi damun Usman ya kalle shi yace, "naji zamu je a same  ta amma ka bari ka sake nutsuwa sosai zata fi sauraren mu in ta ganka a nutsu wallahi yanzu sai ta d'auka ki ka samu matsalar kwakwalwa ne ya saka ka koma haka."
"Ta kira ni mahaukaci ma ban damu ba."
"Kai kace mata darajar Amma take ci kake zaune da ita, meyasa yanzu kace min kana sonta kuma?." Shiru yayi kawai bace komai ba yasan daman kafin a fahimce shi zai sha wahala sosai ma kuwa.

Ya tashi ya goge idanun da yace, "in zaka taimaka min anjima nake so muje." Usman yace, "shikenan to kayi min waya." Yusuf ya fita Usman ya bishi da kallo a bayyanr yace, "nadama Mara amfani kake yi Yusuf, ni nasan Ameena baza ta sake sauraren ka ba, kayi wasa da damar ka domin a yanzu tayi maka nisa."

       Bangaren Fiddausi ta d'an fara farfadowa babu laifi kullum cikin tunanin da ya zamar mata kamar aboki ko yaushe suna tare ko kuma tana kuka. Tana zaune a tsakar gida tana wanke kwanuka Abba ya shigo ta juyo ta kalle shi tace, "Barka da dawowa Abba." Ya kalle ta sai ta bashi tausayi sosai dan sharrin zuciya ne kuma ba kowa ne zai iya sarrafa zuciyar sa ba musamman in kana kallon kowa naka yana auren mai kudi kai kana gidan talaka sai mai imani sosai.

"Barka dai Fiddausi, ke kike wanke kayan?." Jin abinda Abba yace sai tayi murmushin jin dad'i tace, "eh Abba."
"To sannu, Allah yayi albarka. İn kin gama kizo " ya fad'a yana shiga d'akin sa. Farin ciki kamar me haka Fiddausi taji tayi dariya sosai cikin karsashi ta gama aikin ta tashi ta shiga d'akin Abban ta same shi da Mama a zaune.

Zama tayi ya kalle ta sosai yace, "ya labarin mijin naki?." Tayi shiru kanta yana k'asa yace, "ba ina takura ki akan maganar bane Fiddausi, har yanzu mijin kine akwai auren sa a kanki dole mu neme shi muji ya sake ki ne ko yaya."
"Wallahi Abba ban San inda zan same shi ba." Abba yace, "to haka zaki zauna da aure a kanki? Ke ba bazawara ba ke ba mai aure ba Fiddausi?." Shiru tayi bata amsa ba idanun t suka ciko da hawaye yace, "wannan kukan da kike ba shine mafita a alamarin ki ba" ya kalli Mama yace, "bakya yi mata fad'a ne?." Mama tace, "ina yi mata wallahi, amma kuka da tunani ya zamar mata abokan hira a yanzu."

Abba ya kalle ta yace, "meye amfanin tunanin da kike yi Fiddausi? Kina ganin tunanin shine maganin damuwar ki ne?." Tayi shiru bata amsa ba yace, "damuwa da tunani ba shine maganin hankalin da kike ciki ba, ki tashi cikin dare ki yi sallah ko fad'awa Allah damuwar ki yafi ki zauna kina wannan koke-koken na banza da wofi. Zaman kukan da salati kike da yanzu wani abun ya fara warware miki." Fiddausi tace, "ka yafe min Abba, nayi maka laifin da kayi fushi dani, nayi nadamar abinda na aikata ka yafe min kar fushin ka ya sake jefa ni a wata masifar." Abba yace, "na yafe miki Fiddausi dmaan ni ba laifi kika yi min ba kawai ina jin haushin abinda kika aikata, amma yanzu tunda kin gane kuskuren ki shikenan Allah ya yafe mana baki d'aya." Mama tace, "amin ya Allah."

Abba yace, "Ya kamata ki dinga bibiyar lamarin mijin ki tunda da dai bai sake ki ba akwai auren sa a kanki har yanzu." Zatayi magana akayi sallama daga waje Mama ta amsa tana tashi ta fita Jin muryar mace,daga k'ofar d'akin Mama tace, "A'a Rukayya, shigo mana." Shiga Rukayya tayi ta k'arasa ta durkusa har 'kasa ta gaishe da Abba ta gaida Mama suka amsa da sakin Fuska Abba yace, "ya wajan mijin naki?."
"Alhamdulillah."
"In kin koma kice ina gaishe shi da kyau." Tace, "in sha Allah." Mama tace, "Fiddausi tashi ku shiga ciki zata gashi da tsugunon." Fiddausi ta tashi suka fita ita da Rukky  zuwa d'aki.

Rukayya ta zauna tana kallon ta tace, "Fiddausi har yanzu baki canja ba, ni sai naga kamar kin sake ramewa wallahi." Fiddausi tace, "to Rukayya ina jin dad'i a wajena balle nayi kiba? Wallahi kullum da tunani nake kwanciya nake tashi, bani da wani sukuni gabana yayi ta fad'uwa." Rukayya tace, "to wannan ai ba mafita bace addu'a zaki dinga yi ki kawar da komai daga zuciyar ki, wannan tunanin da kike ba komai bane face ciwo da zai saka miki." Fiddausi ta kalle ta tace, "in nace miki zan cire damuwa wallahi karya nake Ruky, ayi shiru dai kawai amma ni da jin dad'i ba yanzu ba, watakila sai na mutu ma. Koda yake ma ina jin dad'i a wajan wacce tayi..." da sauri ta dakatar da ita tace, "India zaki dinga irin wannan maganar Allah zai daina zuwa wajan ki, wannan wacce irin magana ce? Kin fitar da rai daga rahamar Allah ne?, kuma shi laifin da kike magana ai Allah ya gani yasan ba da son ranki bane tilasta ki akayi Allah kuma bazai kama ki da laifin kin aikata ba. Dan Allah Fiddausi ki dawo hankalin ki ki mayar da hankalin ki ga rokon Allah komai zai wuce wallahi."

Fiddausi tayi murmushi tace, "ina son neman yafiyar mijin ki amma ban san da wanne ido zan kalle shi ba." Rukayya ta kalle ta suka had'a ido ta sauke numfashi tace, "da idanun da kika saba kallon sa ko yaushe Fiddausi, na tabbata da zai yafe miki."
"Kunyar had'a ido nake dashi."
"İn kana neman abu daurewa ake a manta da abinda ya wuce." Tayi Ajiyar zuciya tace, "zan k'ok'arta nazo gidan ki taimaka min na bada hak'urin, nayi abubuwa da yawa wanda yafe min sai mai zuciyar imani, amma zan iya cin albarkacin ki ya yafe min." Rukayya tayi murmushi tace, "ko badan ni ba zai yafe miki Fiddausi, badan kar nayi saurin cewa ya yafe miki ba da nace ya jima da yafewa. Amma gwara kiji daga bakin sa zaki fi samun kwanciyar hankali."

Fidy tace, "yaushe zaki kawo min Amir? Ina kewar sa sosai a taimaka min ko kwana biyu yazo yayi." Rukayya ta dafa ta tace, "Amir d'an ki ne fa Fiddaui ke kika sha wahalar haihuwar sa, meyasa kike cewa a taimaka miki?." Zatayi magana Ruky tace, "Dan Allah ko daina cewa haka in sha Allah Amir zai zo yayi kwanaki a gidan nan." Tayi murmushi tace, "Rukayya tunda na tafi na tuna ne Amir banda lokacin da mukayi waya dake? Ban tuna da Amir ba ina ganin zan sake samun wani a wancan gidan da nake so shiyasa nayi banza dashi duk da ina son kayana. Dan nace ki taimaka min naga Amir ba laifi bane tunda a hannun mahaifin sa yake dole sai na neman alfarma kafin na ganshi."
Chapter 54 · 0% Book details