← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 93

Sashe 84

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D’akin da take ganin yana shiga ta shiga sai kuwa ta hango shi a zaune a kan tiles hannun sa ya dafe kansa alamun ciwo da Sauri ta k’arasa wajan tace, “ciwon kan ne har yanzu? Ya kamata kaje asibiti.”
 Rik’e hannun ta yayi ya kalle ta cikin ciwo yace, “wannan ciwon kan bana jin zai barni, Ameena kin kasa yafe min har yanzu kin kasa sakin jiki dani ni kuma tsoron yi miki magana nake, haka nan Allah ya saka min shakkar ki a zuciyata. Dan Allah kiyi hak’uri ki fad’a min koda kalma daya ce da zanji dad’i kafin ciwon nan ya zama ajalina.”

Dakyar yake maganar ta zauna kusa dashi tana jin tausayin sa sosai tace, “na yafe maka wallahi har cikin zuciyata babu komai a raina, kawai na kasa amincewa da ba rayuwar baya na dawo maimaitawa ba shiyasa na kasa sakin jikina.” 
“Rayuwar baya ta wuce Ameena, rayuwar baya ta zama tarihi yanzu sabuwar rayuwa zamu yi dake in Allah yasa ina da tsahon kwana. Wallahi Ameena ina sonki, ina sonki son da nan miki shi a baya ba, ki amince dani na nuna miki wannan soyayyar kafin raina ya bar jikina.” Ya fad’a yana kwanciya a jikin ta ta rike shi idanun ta suna taruwa da hawaye tace, “na kasa baka damar ne, gani nake kamar baka canja ba, kallon komai nake kamar farkon auren mu na wancan lokacin haka komai ya dinga faruwa cikin kula da soyayaya amma daga baya komai ya watse. Ina jin tsoron hakan shiyasa Kaga ina baya da kai.”

Shima hawayen yake a jikin ta yace, “na canja baza’a sake maimaitawa ba Ameena, sai kin bani dama zaki tabbatar da abinda nake fad’a miki in baki bani dama ba baza ki kai ga sanin abinda nake nufi ba. Kiyi hak’uri ki bani dama wacce zan nuna miki waye Yuusf a wannan lokacin.”
“Na baka dama, daga yau na baka dama ka gyara abinda ka b’ata, in ka yaudare ni Alalh yana kallon ka bazai barka ba.”
“Har abada, babu ke babu kukan bak’in ciki sai dai kukan farin ciki Ameena. Akwai halina da nake dashi wanda ke kin san dashi ki yi hak’uri dashi a duk lokacin da nayi miki amma batun abubuwan da suka faru baza su sake faruwa ba.”

Ta goge idanun fa tace, “shikenan yanzu muje asibiti jikin ka yayi zafi sosai.” Ya sake kwanciya a jikin ta yace, “ina samun sauki a jikin ki, na sha magani ki barni a haka zan dawo daidai.” Rik’e hannun sa tayi tana maruza tafin hannun sa saboda ya sake samun sauk’i yana kwance a jikin ta har lokacin kuka yake yi tace, “ka daina zubar da hawaye shima zai saka maka ciwo.”
“İn na tuna abinda nayi miki bana iya sarrafa zuciyata sai na yi kuka.”
“To kayi hak’uri ai komai ya wuce.” Shiru yayi yana jikin ta har lokacin kafin ta kalli fuskar sa da take kirjin ta taga ya kulle ido alamun bacci zaiyi babu jimawa kusa baccin ya d’auke shi.

Kallon fuskar sa take yi sai tayi murmushi tana kawar da komai a zuciyar ta tana d’aura d’ammarar fara sabuwar rayuwa da mijin ta. A haka suka kwana dan itama bata san tayi bacci ba kiran sallar wayar sace ta tashe su. Shi ya fara motsawa ya tashi zaune sosai yana rik’e da wuya ya kalle ta yaga ta bud’e ido itama sai yayi murmushi ya kai nata kiss a forehead yace, “Ashe a haka muka kwana.” Tayi Murmushin itama tace, “Anyi Kira mu tashi lokacin sallah, bara na duba Zaytun” ta fad’a tana tashi da sauri ta shiga ta samu Zaytun din kuwa a zaune kamar aljanna tana game.

A bayan ta ta ganshi ta kalle shi suka kallo Zaytun din tace, “Game din yarinyar nan tayi yawa har tsoro take bani, Duk ranar da ta fasa min waya sai ka biya, kaine ka koya mata game.” Murmushi yayi yace, “na siya mata iPad ma mantawa nake ban d’auko ba, in taje school ta dawo sai tayi abin ta a daina mata gorin waya.” Ameena ta kalli Zaytun tace, “tunda kin tashi sai muyi sallah, tashi muje alwala” ta fad’a tana shiga band’aki Zaytun tabi bayan ta sukayi Alwala tare ta suka fito shima yayi alwala sukayi sallah a tare zuciyar da kamar an wanke ta da soso da sabulu haka yake ji.

Bayan sun idar ta tashi tace, “zan sauka na had’a m mata lunch box lokacin school ya kusa.” Ya kalle ta yace, “kiyi zamana ki yau Friday basai taje ba.”
“A’a bafa zamu fara haka ba, sai taje makaranta haka akwai baza ka saka ta dinga zaman gıda ba.” Ta fad’a tana fita sai ya d’auko Zaytun din suka sakko tare suka bita kitchen din.

Tare suka yi mata abu mata abinci ta saka mata a box din ta sake komawa sama tayi mata wanka ta saka mata uniform ta saka ta yaci abinci kafin mai school bus din su yazo ya d’auke ta su tafi. Yana dawowa daga kai ta wajan motar tace, “kaima kayi breakfast din kasha magani, zanyi wanka zanje school ina da test.” Ya bita da kallo yace, “karfe nawa zaki dawo?.”
“Zuwa ten ma na dawo.”
“Muje ko shirya din muje tare sai na jira ki gama mu dawo.”
“Baka da lafiya fa.”
“Naji sauki.” Tare suke hau saman tace, “da ka jira naje na dawo tunda bazan jima ba naga alama in kana zırga-zirga ciwon yafi damun ka.”

Yace, “in naje na sauke ki kafin ki gama zanje naga Dr akan ciwon kan nan dan damuna sosai, yace damuwa ce kuma yanzu na samu maganin damuwar but still ban daina ba.” Ameena ta kalle shi tace, “kaje asibitin ka dawo zamu yi daidai in ka dawo sai mu huta a gida.” Ya rik’o hannun ta guda biyun yana kallon ta yace, “da gaske hutawa zamuyi in kin dawo?.” Tace, “eh ina zamu je to?.”
Ya girgiza kai yace, “babu, muje kinshirya din to.” Murmushi tayi kawai ta shiga d’aki ta shiga wanka shi kuma ya zauna yana jiran ta.

Tunda ta fito yake binta da kallo ta kalle shi tace, “baka shirya ba?.” Kai ya d’aga kawai yana kallon ta ta tsaya  ita kuma bata motsa ba saboda kunyar sa take ji daman tun can baya ita bata daina kunyar sa ba balle yanzu da suka jima basa tare. Ganin hakan sai yayi murmushi ya taso yace, “na tabbatar wannan kunyar taki har mutuwa.” Tayi dariya kad’an ya matso kusa da ita ya rungume ta ta baya suna kallon madubi shi da ita kafin tace, “ka rame sosai, fuskar ka ta canja kamar ba kai ba.”
“Ke kuma kinyi kiba, jikin ki ya canja kamar ba ke ba.” Tayi dariya shima yayi dariya yayi shiru alamun akwai abinda yake tunawa itama haka sai ga kawar tace, “ina Asiya?.” Gaban sa ya fad’i sosai ya kalle ta yaga kallon sa itama take sai yace,”kar a fara test din bakya  nan” ya fad’a tana zare jikin sa ya koma gefe, tasan baya so ya amsa ne sai ta wuce ta d’auki kaya sai ta fita dan taga alamun bazai bar d’akin ba.

Dariya yayi sosai ya fita ya koma daki shima ya shiga wankan yana jin farin ciki a zuciyar sa da ganganar jikin sa. Tare suka fita ta tafi makaranta ya tafi asibiti, ta riga shi dawowa lokacin da ta dawo baya nan bata jima ba Zaytun ta dawo tayi musu abinci tayi wanka ta canja kaya ta yiwa gidna turaren wuta kamar yadda ta saba ita kanta khamshin sa take yi. A lokacin ne  ya dawo ciwon kan yana neman danne shi sai da ya kwanta kafin lokacin sallar juma’a sannan ya dawo daidai yayi wanka ya tafi masallaci.

Da ya dawo ta gama had’a abincin yana shigowa tace, “Beb Bismillah ga abinci.” Jin sunan da ta kira shi sai yaji dadi sosai yace, “thanks you my choice.”
“A canja min wannan sunan” ta fad’a bayan ya zauna tana zuba masa abincin yace, “wanne kike so.
“Daga zuciyar ka.” Yayi shiru alamun tunani kafin yace, “nima Beb din zance.” Sukayi dariya a tare yana cin abincin tace, “ya kuka yi da Dr din?.”
“Hoton kwakwalwa za’a sake yi yace ko abin ya tab’a min kwakwalwa ta. Amma ji nasan normal nake bana hauka ai?.” Sai tayi dariya ya bata tausayi sosai tace, “baka yin komai.” 

Yayi murmushi yace, “nayi haukan a lokacin da zan rasa ki, ashe damuwar ce tayi hawa har ta tab’a kwakwalwar.”
“Yanzu zata tafi in sha Alalh.”
“Allah ya biye bakin ki. Ina Ammata?.”
“Tana gidan Ammah, nima jira nake ka gama muje mu gaishe su zuwa dare ma dawo.” Ya girgiza kai yace, “muje dai mu dawo amma ba zuwa dare ba.”
“Meyasa?.”
“Saboda Ina son kasancewa da ke Beb.” Tayi dariya b’ata ce komai ba ya gama cin abincin suka tafi gidan Ammah.

#Nana Haleema
#Mai daki
#Book3

Book3
42

         Kamar yadda kusan ko wacce juma’a suke taruwa haka yaga yan gidan nasu gabad’aya suna nan har Humaira ta Abuja ce kawai bata nan suka shiga da sallama Ammah ta amsa ganin Ameena sai Murmushin ta ya k’aru itama Murmushin tayi ta k’arasa suka gaisa dasu dukkan su shima ya zauna suka gaisa kafin Abbah yace, “Yanzu muka gama waya da Adam ai, ashe ya koma cross river.” Ameena tace, “eh yana can kusa sati d’aya ma.”
“Allah Sarki, Allah ya taimaka ya bada nasara.” Ameena ta amsa da amin tana murmushi.

 D’aga ido tayi suka had’a ido da Humairah sai taga Tana d’aga mata m gira tana kashe mata ido sai tayi dariya a bayyane tace, “Allah ya shirye ki.” Itama dariyar tayi Abbah ya kalle shi yace, “kaje asibitin?.” Yusuf yace, “eh naje,wannan hoton kwakwalwar za’a sake yi suka ce. Ni na gaji da wannan hoton wallahi in anyi suce babu komai.” Abbah yace, “to ka tafi Saudia german mana a duba ka a can,  in da matsala ai su zasu gani zaman da kake da ciwo baka san ne yake kawo maka shi ba illa ce.”
Chapter 84 · 0% Book details