Sashe 61
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zubewa ya sake yi akan guwiar sa yace, “Alfarma d’aya, lokaci na biyu Yaya. Bazan iya rayuwa babu Ameena ba, bazan yi cigaba da zaman duniya babu Ameena ba. Ka taimaka min ka yi hak’uri ka sake bani ita nasan nayi kuskure amma zan gyara wallahi, zan canja wallahi, duk abinda ya faru bazan sake aikatawa ba zan rik’e ta hannu biyu Yaya zan tabbatar tayi farin cikin da bata…….” Marin da ya yiwa Yusuf sai da ya kusa fad’uwa ta baya, ya jure baya son Marin nasa amma ya kasa sai da ya aikata ya kalli Usman yace, “ja abokin ka ku bar nan kafin na zubar masa da haqoran bakin sa, sannan ina so ka ja masa kunne in sake zuwar min da wata banzar magana sai na karya k’asusuwan jikin sa. Ya san hana sonta ya wulak’anta ta? Yasan yana sonta yake dukan ta? Yasan yana sonta ya iya saka mata damuwar da ciwo ya kamata?. Ko so yake yace min duk wannan so ne? Ko so yake cemin ai kulawa ce ta jawo take da hawan jini a lokacin da take gidan sa?, har gobe magani take sha ta dalilin sa, kenan soyayya ce?. Ya manta Idon ta ya kalla yace alfarmar babar sa take ci da yanzu ya sake ta saboda ba sonta yake ba zaman dole yake yi da ita saboda mahaifiyar sa? Ya manta ne?. İn ya manta ni ban manta ba, ka fad’a masa wannan hawayen da yake, da wannan zubewa a k’asa bazai saka zuciyata taji tausayin sa ba, wallahi ya sake zuwar min da batun na sake bashi Ameena a karo na biyu sai nayi masa abinda ko a mafarki baiyi tununani ba.”
Kuka sosai Yusuf yake yi kamar k’aramin yaro ya kasa rik’e kukan ya kuma rasa waye zai fahimce shi a halin da yake ciki yace, “Yaya dama ta k’arshe ta k’arshe dan Allah.” Kama k’ugu yayi ya dafe kai yace, “ka matsar da Yusuf daga nan kafin alfarmar iyayen sa da yake ci ta kau a zuciyata nayi masa dukan da zai kasa tashi.” Usman ya d’ago Yusuf daga yadda yake yace, “ayi hakuri. Yusuf mu je.” Ya girgiza kai yace, “taya zan tafi bayan Ameena tana gidan nan? Usman kai kasan bazan iya rayuwa babu ita ba, ka fad’a masa wallahi na canja ba Yusuf din baya bane ba, ka sanar dashi yanzu bazan sake aikata kuskuren da nayi a baya ba. Usman ka fad’a masa kafin ya raba ni da rayuwata.”
Usman ya kalli Yaya Adam yaga yadda yake wuci babu damar yi masa wata magana sai yaji tsoro ya ja Yusuf yana k’in tawowa yana kallon Yaya yace, “Dan Allah Yaya, dan girman Allah badan ni ba, dan darajar iyayen ka” yana magana hawaye suna sauka Usman ya rik’e hannun sa suka fita shi kuma ya zauna a kan kujera Anty Aysha ma ta zauna kusa dashi zuciyar ta duk ta karye dan wallahi Yusuf ya bata tausayi sosai.
“Kayi hak’uri, ya tafi ai ka sassauta zuciyar ka ko babu komai akwai Zaytun Tsakani kuma mahaifin ta ne.” Baice komai ba ya zabura ya yi wajan Ameena tana zaune a d’akin amma tana jiyo duk abinda yake faruwa yana shigowa ya bita da kallo yace, “Ameena a lokacin da kika nema da zan baki tsakanin ki da Al’ameen gobe nake so ki fad’a min abinda yake ranki, in kina so kina so in bakya so bakya so” yana fad’a ta juya ya fita ta bishi da kallo ta sauke numfashi ta koma ta kwanta a kan gadon. Kuka Zaytun take har lokacin itama ta juya ta kalle ta tana rarrashin ta tace, “ya isa kukan Malama.” Ta matso kusa da ita ta goge mata ido ta kwantar da ita a jikin ya sai tayi bacci.
Yusuf ya gigice ya fita daga hayyacin sa kuka yake kamar ya mutu hankali Usman ya tashi sosai ya raba masa hankali daga tuk’in da yake yi. Nan da nan jikin Yusuf ya fara rawa haqoran sa na had’uwa da juna Usman yace, “Dan Allah Yusuf kayi hak’uri ka daina wannan kukan mutane suna kallon ka fa, in ka kwantar da hankalin ka komai zai zo da sauki amma sai anyi hak’uri.”
“Mutane dan sun ganni Usman ba komai bane, zafi nake ji a kirjina, kaina ciwo yake min, zuciyata bugawa take. Bana son rasa Ameena, bana son rasa Ameena a wannan lokacin ka taimaka min Usman.” Hankalin sa ya tashi sosai a haka suka isa gidan Yusuf ya faka motar ya fito ya zagayo zai fito da Yusuf din yaji zafin da yake jikin sa hankalin sa ya sake shi ya koma motar da sauri ya shiga ya sake jan motar zuwa asibiti.
Sai bayan an kwantar dashi an saka masa ruwa da allurai sannan ya samu damar yin sallah ya d’auki waya ya kira Abbah ya sanar dashi suna asibiti sannan ya zauna yana jinyar sa. Yana zaune a cikin d’akin Abbah da Ammah da kuma Mubakar da Abie suka shigo suka kalli Yusuf daga inda yake Ammah tace, “Usman me ya same shi haka? Kaga fuskar da yadda tayi ja sosai.” Usman yace, “Ammah komai ma damun Yusuf yake yi, ance jinin sa ya hau sosai ga damuwa da tayi masa yawa har ta haifar da zazzab’i mai zafi a jikin sa da ciwon kai. Yace kirjin sa zafi yake masa ban san ya zanyi na yayewa Yusuf damuwar sa ba.”
Abbah yace, “meye yake damun sa hakan?.”
“Abbah jiya Bauchi muka je gidan Yayar Ameena yaje ya bata hak’uri akan abubuwan da suka faru, ya kasa tunkarar Yayan ta saboda abinda ya aikata tsoron hakan yake ji. Yau ya daure munje wajan sa k’arshe kaga sakamakon abinda ya faru. Wallahi Ammah Yusuf d’in baya dana yanzu akwai banbanci, yana son Ameena wallahi, in ya rasa Ameena a wannan kadon zamu iya rasa Yusuf Ammah.”
Mubakar yace, “in dai fahimta yaje bikon Ameena ko?.” Ya d’aga kai alamun Eh Mubakar yace, “lallai ma. Ai Yaya Adam din yayi k’ok’ari ma wallahi da bai fasa masa baki ba. Shi yanzu ba kunya ba tsoron Allah sai yaje yace a bashi Ameena dan girman Allah?.” Abbah yace, “laifin Usman din ne ma da yake biye masa har suka je suka samu Adam da maganar, yanzu in da k’anwar Yusuf d’in ce aka yiwa haka in mijin yazo ya same ku zaku sake bashi auren ta?.” Usman yace, “wallahi Abbah indai ya canja kamar yadda Yusuf ya canja zamu sake bashi. Yusuf ya canja, Yusuf ba na da bane ha wallahi yana son Ameena sosai.”
Abbah yace, “soyayyar banza da wofi, duk abinda ya dinga yi mata ya manta yana son nata sai yanzu zai tuna?. Haka akwai dan ya tayarwa da yarinya hankali zai je yace yana sonta dan kawai ya b’ata mata rai ya tuna mata da abinda ya wuce?. Shi yanzu waye ya bashi k’arfin guiwar zuwa ya samu Adam dan girman Allah?. Wannan ai kamar cin zarafin Adam din ne, duk abinda ya aikata bai gani ba har yana da zarrar da zai je wai ayi hak’uri?.”
Ammah tace, ‘“ni na kasa magana ma wallahi, yarinyar da ya yiwa wannan wulakancin shine yanzu ya koma mata yace wai yana son dawo da ita dan bashi ma da mutunci bai San abinda yake yi ba?.” Usman ya bud’e baki zaiyi magana ta dakatar dashi Tce, “dakata Usman kar ka kare shi dan ya kasance naka, kayi adalci akan abinda yake daidai kar ka zab’i son zuciya akan gaskiya. ni na haifi Yusuf nasan halin sa nasan abinda zaiyi nasan wanda bazai yi ba. Banda raini ma har yana da k’afar zuwa wajan Adam akan Ameena?.” Abbah yace, “yanzu dai a bar maganar nan kar a tashe shi a asibiti muke mu jira ya dawo daidai sai muyi maganar da zamuyi.”
Usman ne a tare dashi har bayan sallar i’sha duk da ya farka idanun sa a bud’e yake amma bai ce komai ba har lokacin idanun sa a bud’e yana kallon wani wajan daban. Mubakar ne ya shigo yace, “Usman kana nan ashe.” Usman yace, “eh yanzu zan tafi.” Ya kalli Yusuf yace, “ba yanzu zamu tafi da shi Yusuf din ba?.”
“Gaskiya basu ce ba akwai drip din da zasu saka masa gobe suka ce.”
“Muje gida akwai a saka masa gobe tunda ya farka daga baccin, zaman asibiti ai sai dole.”
“Da sai yafi ma.” Fita Mubakar yayi Jim kad’an ya dawo yace, “Yauwa muje, Yusuf muje” ya fad’a yana kallon Yusuf da idanun sa na kallon sama.
Sai da Mubakar ya tab’a shi sannan ya fahimci ma magana yake yi dan yayi nisa a tunani ba ganewa yake ba yace, “muje gida ko?.” Kai ya girgiza kawai ya sakko da k’afar sa ya saka takalmin sa suka fito duk shiga mota suka tafi. Gidan Ammah suka wuce a lokacin babu kowa a falon Ammah Yusuf kai tsaye d’akin da yake kwana ya wuce ya kwanta a kan gadon yayi shiru shi ba bacci ba shi kuma ba tunani ba. Sai kuma ya tashi ya shiga band’aki yayi alwala ya fito yayi sallah ya zauna ya dinga addu’a akan Allah ya sake bashi Ameena.
Mubakar ne ya shigo ya same shi a haka ya ajjiye leds akan gadon ya bud’e ya d’auko magani ya fito shi ya bashi yace, “likita ya ce kasha wannan maganin da Mun dawo gida.” Bai musu ba ya karb’a ya saka a baki ya bashi ruwa ya sha shi kuma ya fita.
Ba jimawa bacci y d’auke shi a inda yake zaune dan maganin da zai saka shi bacci aka bashi dan ya samu lokacin sosai kamar yadda baya samun baccin.