← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 93

Sashe 7

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

          Kukan Zaytun ne ya tashe shi  ya mik’e zaune ya kalle ya ta mik’a mata hannu ta taso wajan sa yace, "ya akayi Ammah." Ta rik’e shi sosai tana kuka alamun akwai abinda ya bata tsoro sai ya mik’e ya d’auke suka fita daga d'akin. Bai ga Asiya ba kai tsaye b’angaren Ameena ya wuce ya hau sama har dakin Ameena Zaytun tana kiran, "Mummy!." Ya kalle ta ya zaunar da ita akan gadon ya bud’e inda kayan Zaytun din suke an kwashe rabin su amma har lokacin akwai Saura sai dai basu da yawa ya d’auko guda d'aya zuciyar sa na bugawa sosai burin sa kawai ya bar d’akin.

Zaman d’akin ne yaji ya ishe shi sai yayi k’aramin tsaki ya d’auke ta suke fito da kayan a hannun sa ya koma wajan Asiya suka had’u a falo  ya mik’amata kayan yace, "Karb’i kije kiyi mata wanka taci abinci." Ta kalle shi tace, "ban gane bafa, Wai ta dawo gidan nan ne da zama ko ya ya?."
"Kiyi abinda nace kawai" ya fad'a yana kallon ta shima.

Zaytun din ta kalla taga ta kwanta a jikin Yusuf ta rufe ido tace, "to gashi nan ai tama k’i kallona balle ta sakko nayi mata wanka." Ya kalli Zaytun d’in yace, "Zaytun jeki Auntyn ki tayi miki wanka." Maqale kafada tayi tace, "A'a tsoro nake ji."
"Dodo ce ni da kike jin tsorona dan Uwar ko?" Asiya ta fad'a tana sake zare ido tana kallon ta.

Sai kuwa Zaytun ta fashe da kuka tana kiran Mummy, a fusace ya kalle ya yace, “Wai Asiya baki da hankali ne? Wannan yarinyar kike yiwa haka kika zagin ta?.”
“Ta koyo halin uwar tane ai shiyasa.”
“Kika sake min zagi a nan wallahi na buge bakin ki.”
“In nayi sai ya?.” Bai san lokacin da ya buge mata baki ba cikin b’acin rai ta kalle shi tace, “Akan y’ar Ameena?.” bai samu damar magana ba saboda kukan Zaytun ya hau sama ya zaunar da ita a kan gado tana kuka sosai yace, "Daina kuka Zaytun din Daddy me kike so?."
"Mummy! Mummy!" Ta fad’a da karfi tana sake fashewa da kuka.

"Wajan mummy zaki?." Ta d’aga kai alamun eh yace, "to ina zuwa" ya fad'a yana tashi ya shiga band’aki yayi wanka ya fito ya samu ta kwanta tayi shiru kamar mai bacci amma ba baccin take yi ba. Kai ya girgiza lallai ya kamata ya takawa Asiya burki akan yarinyar nan dan bazai dauki abinda take yi masa ba dole ta karb’i Zaytun domin y’arta ce .” Da sauri ya shirya ya d’auki kayan ta da ya d’auko da key na mota ya sauka ko kallon ta bai yi ba ya fita.

Da kallo ta bishi tace, "kan uban nan kayyasa, na rabu da uwa yanzu kuma a kawo min y'a? Wallahi bazata sab'u ba dole na sake shiri daman naga kamar ma bayi nake ba, kamar ina tufka Ana warware min ne dole na d’aura d’ammara domin bazan d’auka ba wallahi” ta fad'a tana d’aukar waya ta hau sama da sauri dan dole Umma taji labarin nan.

       Yusuf kuwa yana hawa mota kai tsaye gidan su ya wuce da Zaytun sai da ya faka motar ya kalle ta yace, "Zaki je wajan Ammah?." Ta girgiza kai tace, "nidai Mummy." Ya sauke numfashi yace, "to mu je mu gaisa da Ammah sai mu je wajan Mummyn ko?." Ta d’aga alamun eh ya fito da ita suka shiga cikin gidan.

Humaira ya gani a zaune tana karatu a falon ganin Zaytun ya saka ta bud’e mata hannu cikin fara’a tana fadin, "Zaytun d’ina." Sai kuwa ya tafi wajan ta a guje itama ya ajjiye kayan ta a kusa da ita yace, "ki mata wanka ki bata abinci sannan ki mayar da ita." Humaira ta kalle shi tace, "ina zan kai ta?."
Ya jiyo ya kalle ta yace, "zata fada’a miki" ya fad'a yana shiga wajan Ammah. Bai jima ba ya fito ya sake fita ita kuma suka shig wajan Ammah da ita.

        Fiddausi lokacin da jirgin su ya sauka a Nigeria dare yayi tana zaune a kusa dashi suna jiran driver da zai d’auke su ya kai su gida sai ga mota guda biyu d'aya babba daya k’arama amma dükkan su masu kyau ne bak’akme hatta glass din jikin su bak’i ne baka ganin na ciki sai dai na waje. Ya kalli Fiddausi yace, "Baby ki shiga wannan zai kai ki gıda, zanje office yanzu."
"Da daddare nan Baby?" Ta fad'a tana kallon sa da mamaki.

Ya mik’e yace, "bazan jima ba" ya fad'a yana shiga bayan Babbar motar ita kuka ta shiga k’aramar suka fita. Tafiya suke tana kallon garin Abuja ko ina da haske kamar ba dare ba amma shiru babu kowa sai jami'an tsaro da mota tsilli-tsilli. Duk inda suka bi Jami’an tsaro zasu tsayar dasu amma da anyi bayani sai a barsu su wuce.

Gaban wani babban gate taga sun tsaya kafin a bud’e a shiga ma sai da aka tsaya ana magana kafin su shiga suka yi tafiya suka sake zuwa wani gate din aka sake bud’ewa suka wuce, babban gida ne sosai iya ganin ka wajan ajjiye motocin ma abin kallo ne gashi ko ina da haske sosai kamar ba cikin dare ba. Driver ya kalle ta yace, "ranki ya dad’e mun iso." Fitowa tayi tana kallon gidan shi kuma ya fito da jakar ta yana kallon ta cikin girmamawa yace, "muje." Gaba yayi tana bin sa a baya tana kallon gidan domin kuwa yayi mata daidai da ra’ayin ta sai murmushi take yi suna har zuwa wata k’ofa ya bud’e yaja baya yace, "bismillah."

Shiga tayi taga babban falo ne sosai mai d’auke da k’ofofi da yawa amma dukkan suna kulle suke, falon babu kowa sai sanyin a.c yana da girma kuma yana da kyau sosai.  Ya nuna mata k’ofar da take can gefe yace, "Waccen k’ofar itace ta bangaren ki, ga mukullin." Ita mamaki take yi shi da yace an America zata zauna to me ya dawo da ita Nigeria har ana cewa ga b’angaren ta?.

Karb’a tayi ya juya ya fita ita kuma tana kallon falon taja jakar zuwa inda ya nuna din, bud’ewa tayi nan ta sake karo da wani falon mai kyau sosai komai sabo kuma komai akwai a cikin sa sai khamshi yake tana bin sa da kallo tare da girgiza kai, jakar taja zuwa inda take tunanin d’aki ne ta sake bud’ewa nan ma taga falo ne wanda sai ka sauka daga steps zaka shiga ta shiga nan ma tana kallon sa.

Murmushi tayi tana jin sanyi a ranta nida farin ciki ta wuce zuwa wata k’ofar ta bud’e sai taga kitchen ne ta kulle ta bud’e wata taga waje ne amma ta baya, rufe wa tayi tace, "oh kenan nan ne hanyar shigowa ba tare da ka biyo ta baban falo ba, wow amazing" ta fad'a tana sake bud’e wata a nan taga doguwar hanya da d’akuna guda hud’u manya. Sai da ta duba ta zab’a taga wanda  yafi Kyau da girma sannan ta shiga ta ajjiye jakar ta shiga wanka.

Tana fitowa ta nufi wajan wardrobe da niyar zuba kayan ta abin mamaki duk kayan ta na gidan da ta fara sauka an dawo dasu d’akin, ta kama k’ugu tana kallo kafin tace, "kenan wai a nan zan zauna? Ko da yake bara na jira yazo muji ya abin yake" ta fad'a tana d’aukar Riga ta saka ta kwanta a kan gado tana juyo cikin farin ciki sai bacci.

     Mata ne guda biyu a tsaye a window suna kallon shigowar Fiddausi har aka raka ta part ta d’aya ta kalli daya tace, "Alhamdulillah lokacin fita na daga gidan nan in sha Allah yayi." D’ayar tace, "Ke kam kin ji dadi ina ma nice ke, na gaji da zama a gidan nan wallahi sam bashi da dad’i. Zaman gidan nan dashi gwara ace a prison kake" ta fad'a tana goge idanun ta da suka ciko da kwallah.

D’ayar ta dafa ta tace, "Zaki fita in sha Allah, Tunda wannan ta shigo wata ma zata shigo kinga kenan mune zamu fita nan gaba" ta sauke numfashi tace, "Allah sarki amarya tana murna ta shigo babban gida, tana murna tazo gidan jin dad’i, tana murna tazo gidan hutu bata san da kwanciyar hankali da gidan nan sunyi hannun riga. Hmmmm! Muna taya ta murna da shigowa gidan da zaman prison ya fishi dad’i, ina taya ta bak’in cikin shigowa gidan nan, domin kuwa zaman gidan nan sai ya saka ta kusa fita daga hankalin ta, domin kuwa zaman gidan nan ya kasance tamkar kabarin bature ne, daga waje akwai kyau da k’yalli amma daga ciki Allah kad’ai yasan abinda yake faruwa.” D’ayar tace, "muje mu kwanta dare yayi sosai ma had’u da amarya da safe. Dan na tabbata itama irin mu ce bata amince ba shiyasa ta dawo nan ayi mata ta k’arfi ko tana so ko bata so.” D’ayar tace, “abin tausayi wallahi. Allah yasa mu dace kawai.” Sallama sukayi ko wacce ta wuce b’angaren ta.

#mai daki
#Book3
#Nana Haleema
#Paid
#500.

Book3

005

Washe gari Fiddausi bata tashi ba sai goma da rabi na safe tana tashi bata fito ba sai da tayi wanka ta shirya cikin kaya masu kyau kana kallon ta Kaga matar Alhaji ta tsaya tana kallon kanta tana murmushi tace, "Gaskiya na dace ni Fiddausi, ba karamar sa'a nayi da na fito daga wancan gidan nazo nan ba wallahi. Kalle ni kai kana kallona kasan babu raini a jikina domin kuwa ko matar gwamna baza ta fad'a min kyau da jin dad'i ba" Tayi dariya tare da yin juyi tace, "kudi duniya ne, wannan b'angaren gabadaya ace shine nawa, ai akwai farin ciki sosai."

Cikin taku na isa ta fito zuwa falon nan tayi karo da wata babar mace a tsaye tana ganin ta ta duk'a tace, "Barka da fitowa Hajiya." Fiddausi ta bita da kallo tace, "barka dai."

Ladidi tace, "sunana Ladidi nice mai kula da b'angaren ki gabad'aya, nice mai share-share da girki da aike in ya tashi." Fiddausi ta sake jin wani abu na hawa kanta ya zauna aka d'ora k'afa kan d'aya tace, "Allah sarki, ke kika gyara falon?."
Chapter 7 · 0% Book details