← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 93

Sashe 68

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana sallar magariba sai ga Ammah Mubakar ya kawo ta har lokaci Usman yana nan ya dai fita ya siyowa Zaytun take away tana cin abinci. Kallon Yusuf Amma tayi da yake kwance akan gadon ta kalli Usmsn tace, “meyasa baza ka bashi shawara kace masa Ameena ta barshi har abada ba? Meyasa baza ka fad’a masa gaskiya yanzu tayi masa nisa ba Usman?. Wannan kwanciya ciwon da yake yi ba shine zai dawo da Ameena ba, in zai k’arfafa zuciyar sa ya k’arfafa ya saka kuma a zuciyar tasa Ameena yanzu ba rabon aa bace.” Usman ya girgiza kai yac, “duk yadda zan miki bayanı baza ki gane ba Ammah, amma wallahi Yusuf yana son Amman ya kuma gyara kuskuren sa meyasa baza’a karb’e shi a lokaci na biyu ba.”

“Dan giyar?, Mai dukan matan?, Mai ce mata barauniyar?, Mai sakata a dsmuwar da ta fara shan maganin hawan jini?,Mai ci mata mutunci a duk sanda yaso?, me saka ta shan magani saboda fad’awa halaka shine za’a ce ya gane kuskuren sa?. Har yaushe daren yayi balle gari ya waye Usman?. Dan kana bayan sa ka dinga fad’a masa gaskiya kar ka fad’i son zuciyar ka, ka sanar dashi ya cire  Ameena daga zuciyar sa in ba haka ba dashi da zuciyar zasu tashi daga aiki.”
“Ammah zai iya rasa hankalin sawallahi Akan hakan,”
“Ya rasa mana, wasu rayuwar suke rasawa dan ya rasa hankali sai me?.”

Usman yayi Ajiyar zuciya bai ce komai ba dan ya lura Ammah tafi Abbah d’aukar zafi Mubakar yana gefe shi kansa tausayin Yusuf yake ji kafin yace, “tsohuwar matar sa Asiya ma aka sake kamata da sark’ar gold din Abbah ta sample din nan na Dubai taje zata siyar. Yanzu haka tana hannu yan sanda nace su cigaba da tsare ta sai gobe zanje sai ta kwana biyu a cell wallahi.” Ammah batayi magana ba ta k’arasa inda Yusuf yake ta tab’a jikin sa har lokacin zafi zauu kamar ba magani ne yake shiga jikin sa ba.

Zaytun ta kalla da take cin abinci itama a lokacin ta kalle ta sai tace, “Ammah Daddy yayi kuka, Mummy ma tayi.” Sai Ammah tayi murmushi kawai bata ce komai  ba Usman yace, “kodan wannan yarinyar Ammah ki daure a san abinda za’ayi Ameena ta dawo gidan ta. Kodan yarinyar nan ta taso a cikin iyayen ta dan Allah a shiga lamarin Yusuf.” Ammah tayi dariya tace, “Yanzu lokacin cin albarkacin yara ya wuce Usman, mata sun daina azabtar da kansu su zauna a gidan mazajen da suke wahalar da rayuwar  su akan yara, wannan zamanin da ka sani yanzu y’anci yafi zama a gidan uban y’ay’a ka gane?.”
Usman yayi shiru ya lura Amma tayi zafi sosai ba yanzu zata sauko ba. Har dare suna nan sai wajan sha d’aya na dare sannan Ammah suka tafi da Usman shi kuma Mubakar ya zauna dashi.

       Washe gari da safe Mubakar yaje station din aka fito da Asiya akayi masa bayanin komai an kamata da kayan sata tana kuma k’ok’arin siyarwa, an tambaye ta tace ta mijin tace. Ya kalle ta yayi dariya ganin yadda tayi bak’i sosai sai kuka take ga majina a hancin ta yace, “ni ba nine mijin ta ba kanin sane ni, amma sark’ar da ta sace ta uban mijin tace an bashi sample daga Dubai” ya fad’a yana ajjiye masa receipt yace, “gashi ka duba akwai sunan company da komai a jiki zaka tabbatar in ka kira ka fad’a musu sunan da yake kai zasu tabbatar maka da mallakin mai wannan sunan ne.” Nan akayi bincike akai aka tabbata abinda ya fad’a gaskiya ne dan sandan yace, “Yanzu satar ta ta har ta shahara tana yiwa uban mijin ta?.”

Mubakar yace, “ga zahiri nan ma ka gani, kaf unguwar su babu baruniya kamar ta. Kowa kuka yake da ita har haura gidaje take yi, a garin satar ta b’allo hannu.” Ya girgiza kai yace, “ah wannan barin ta cikin jama’a kuma ai illa ce, gwara a tura ta wajan alqali ya tura ta prison ta girbi abinds ta shuka. Asiya ta fashe da kuka jin abinda akace tace, “ku yi min rai dan Allah, Kuyi hak’uri na tuba bazan sake ba daga yau wallahi, Tsautsayi ne wannan ma amma daga shi na daina.” Mubakar yace, “karya kike baza ki daina ba, sata ta zamar miki jiki baza ki tab’a dainawa ba” ya kalli d’an sandan yace, “inda zai yu a kaina prison na sati d’aya taje taji ya ake ji in ta fito watakila zatayi hankali.” Asiya tace, “Dan Allah kayi hak’uri wallahi na daina, wannan din ma tsautsayi ne Ummana aka kama nake son biya mata kudin da ake binta na fito da ita. Kayi hak’uri ka yafe min na daina aikata abinda nake aikatawa.”

Mubakar yace, “duk bala’in kifa sai kin je prion. Gadon tsiya ke a cell uwa a cell, banga amfanin mata irin ku ba a duniya, kamata yayi a biku duk a bindige.” Kuka Asiya take sosai tana bashi hak’uri dakyar ya hak’ura yace a kyale ta amma da sharad’in in aka sake kamata da wannan laifin sai ta tafi prion tace ta yarda. Aka bata damar tafiya shi kuma ya karb’i sark’ar ya tafi  bayan yayi musu alkhairi.

Asiya a haka ta tafi gida jiri yana d’aukar ta tana kuka sosai duk abinda ta tara a gidan Yusuf ya k’are ta dawo bata da komai ko zare bata dashi, a haka ta shiga gidan tana shiga ta zube a tsakar gida suka yi kanta suka Momi tace, “Lafiya? Ina kika shiga aka neme ki aka rasa yau kwana biyu?.” 
“Ruwa zan sha, ku bani ruwa na sha.” Da sauri aka kawo mata ruwa ta sha ta kwanta a wajan tana kuka sosai. Maimuna tace, “muka dinga jiran ki kince zaki kawo kud’in da za’a fito da Umma shiru yanzu gashi dakyar aka bada ita ance nan da sati in bata bada kud’in ba sai ya tafi prison, ina abinda kika ce zaki je ko siyar din?.”

Asiya tana daga kwance tace, “Sun kwace komai, an kwace komai daga hannuna, bani da komai yanzu komai ya k’are. Kwana na biyu a wajan y’an sanda sai yanzu aka fito dani. Na shiga uku ni Asiya komai ya lalace min.” Maimuna jin haka sai kowa yayi shiru Umma ta ta fito tana kallon ta tace, “sai ki tashi daga wajan ki shiga ciki sai maqota sun sake sanin halin da muke ciki ko me?. Abin kunya ne ace naje cell kema kin kwana biyu a cell.” Asiya bata tashi ba bata daina kuka ba tace, “Umma duk ke kika jawo min, da baki saka an sake ni ba da yanzu ina gidsn mijina ina rayuwar farin ciki, amma yanzu kalli yadda na koma komai ya lalace min bani da ko sisi, ko waya bani da ita bani da komai.”
Umma tayi tsaki kawai bata ce komai ba ta koma ciki duk suka barta a wajan sai da ta gaji dan kanta ta tashi ta shiga d’aki tana ki kamar tayi hauka saboda tashin hankalin da take ciki.

            Adam yana tsaye yana amsa waya Anti Aysha tazo ta tsaya a kusa dashi taji yana cewa, “tun lokacin meyasa baki fad’a min yaje gidan ki ba?.” Shiru yayi alamun ana bashi amsa sannan yace, “sai yaje duk inda zai je ko wa zai nema a bayana yake, ni kuma bazan sake bashi Ameena a wannan Karon ba.” Shiru ya sake y kafin yace, “shikenan dai sai kin shigo” ya fad’a yana kashe wayar ya kalli Aisha yace, “Ya dai?.”

Tace, “Yaya Samira ce?.”
“Itace, ashe Yusuf yaje gidan ta tun kafin yazo nan zuwan farko.” Tayi murmushi tace, “Yusuf da gaske dai neman biko yake yi.”
“Ai bashi da hankali ne, Ba kuma zai samu ba.” Tace, “ka daina cewa haka in Allah yayi zata koma din fa? Kaga akwai yarinya a tsakanin su ni wallahi ko dan ita a raina ina so ta koma saboda yarinya ta taso ba a cikin iyayen ya babu dadi wallahi. Ni kasan a haka na tashi har gobe babu wata shak’uwa tsakanina da Abban mu saboda nan tashi dashi ba.” shiru bai amsa ba ya d’auki abinda zai d’suka ya fita daga d’akin.

A falo ya hango Ameena ya tsaya daga inda yake yana kallon ta yaga tana zaune tana duba littafi amma sai yaga ta rufe ta dafe kanta ta d’ago tayi k’aramin tsaki ta zame ta kwanta a bangon kujerar. K’arasowa yayi ya kalle ya yace, “Ameenatu ya dai?.” Sai ta d’ago ta kalle shi tace, “Babu komai Yaya.”
“Yau babu school?.”
“Eh yau Sunday ai sai gobe in Allah ya kaimu.”
“Allah ya kaimu” ta amsa da amin yace, “jiya Muna magana akan lokacin bikin aka katse mu, yaushe ne zaku yi exams din?.” 

Ta kalli Yaya tace, “nan da sati biyu ne, har na exams din uku kenan in Allah ya kaimu.” Ya girgiza kai yace, “bikin sai a saka shi sati ukun kinga sati ne hudu kina hutu ko?.” Ta d’aga Kai alamun eh yace, “hakan za’a yi, zan sanar da Al’ameen din sai ki fad’a masa abinda kika shirya sai ku san abinda zaku yi.” Ta kalle shi tace, “to Yaya.” Ya juya zai fita sai ya juyo ya kalle ya yace, “babu wani abu dai ko?.” Ta girgiza ka tace, “babu komai.” Ya juya ya fita ta lumshe ido ta bud’e ta cigaba da karatun ta.

Tana zaune sai ga Anti ma ta fito tana tsokana ta tayi dariya tace, “wato Anti ku da yake kin gama boko shiyasa in kina ganina sai ki ta min dariya.” Anti ta zauna tace, “ina fa aka gama? Da ya aka kammala masters din ma balle a gama?.” Tayi dariya tace, “mu gashi digree muke so ta kammala tak’i.”
Chapter 68 · 0% Book details