← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 93

Sashe 18

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma tayi dariya tace, “ki jira bak’i su tafi za’a fad’a miki waye a cikin su.” Zama tayi a gefen gadon bayan Umma ta fita Zuhra ta shigo tana kallon ta tare da fad’in, “Yaya wai ya na ganki ba’a nutse ba?.”
“Zuhra wallahi gabana fad’uwa yake ban San meyasa ba.”
“To Yaya meye na fad’uwar gaban ke da zaki yi farin ciki?.”
“Na kasa tantance yanayi na wallahi.”
“Zaki tantance in Baba yace Kizo.”

Tana nan zaune har akayi kiran sallar magriba a lokacin Baba ya fito ya raka bak’in waje suka tafi bai dawo gida ba ya wuce masallaci yayi sallah sannan ya dawo gida duk wanda ya ganshi yasan yana cikin farin ciki sosai daga kallon fuskar sa zaka gane hakan. Sai murmushi yake tun a hanya yake ta basa yara sadakar y’an chanjin da suke aljihun sa yara sai murna suke yi.

Yana shiga gida ya kira Umma ta jima a wajan sa sannan aka kira Rukayya ta shiga gaban ta yana fad’uwa ko kallon su ta kasa yi, waje ta samu ta zauna Baba ya kalle ta yace, “Rukayya kina ya jiran tsammani ko?.” Ta sunkuyar da kai tana murmushi shima yayi murmushi yace, “kar ki damu alkhairi ne a baibaiye dake Rukayya, alkhairi shine ya kai kinga wannan lokacin.” Bata ce komai ba ya mik’a mata kud’i yace, “Karb’i wannan.” Rukayya ta kalli abinda yake mik’a mata taga kud’i ne zasu yi dubu d’ari ta karb’a Baba yace, “kud’in sadakin kine Rukayya.”

Gaban ta ya yanke ya fad’i ta kalli Umma taga sai murmushi yake tana goge hawaye da alama na farin ciki ne ta sauke kai k’asa Baba ya sake yin murmushi yace, “nasan mun saka zuciyar ki a rud’ani ko?.” Bata ce komai ba Baba yace, “farin ciki da nishad’in da ya cika zuciyar mu, kowa farin cikin ganin d’an uwan sa matsayin siriki ya saka aka kasa b’oye wannan farın cikin sai da aka karb’i sadakin ki a matsayin matar aure, shaidu sun shaida d’aurin auren ki a d’azu Rukayya ga goro da alawa. Mahaifin k’awar ki Fiddausi shine ya bada sakadin gabad’aya naira dubu d’ari.”

Dam dam dam gaban Rukayya yake bugawa ta d’ago ta kalli Baba suka had’a ido sai yayi murmushi yace, “Kinga lokacin ko Rukayya? Lokacin da kike fad’awa Umman ki kice Umma lokaci ne in lokacin aurena yazo zanyi amma bata ganewa, yau gashi da lokacin yazo basu tafi ba sai da aka d’aura auren ku. Zaman ki a gidan nan ya k’are, zaman ki matsayin wacce babu aure shima ya wuce yanzu matar aure kike Allah ya rubuta baza ki kai gobe babu igiyar aure a kanki na. Kamar mutuwa ce kiji ana cewa haka ta shiga d’aki lafiya lau amma sai gawar ta aka fito da ita saboda lokacin zaman ta a duniya ya k’are lokacin na komawar ta ga Allah yayi, koda ciwo ko babu ciwo sai anje. To haka auren ma; ban tabbatar da hakan ba sai yanzu, da lokacin auren naki yayi gashi bamu shirya ba ba zato babu tsammani anyi auren ba tare da dukkan mu munyi tunanin hakan zai faru ba. Wato in akace ka barwa Allah lamarin ka wallahi baza ka tab’a dana sani ba, in akace kana addu’a Allah ya zama maka na gari kuma mafi alkhairi wallahi baza ka gushe ba sai kaga alkhairin da zai same ka.”

Baba ya sake cewa, “Rukayya hak’urin da kika yi, da zab’in da kika barwa Allah, da kame kanki da kika yi a gida kika tsare mutuncin ki gaba da baya Allah bazai bari ki wulak’anta ba duniya da lahira. Kin karb’i k’addara kin jure duk wani abu daga wajan mahaifiyar ki da y’an uwan ki da k’awayen ki dama mutanen Unguwa, kin kawar da kai daga duk wata magana da ake miki, kin jure hanaki aiki da karatu da nayi kin zauna a gida har aka aurar da k’anwar ki aka kawo kudin kanwar ki ta biyu amma a fuska baki nuna bak’in ciki ba sai dai kice Allah ya sanya alkhairi kina farin ciki kina murna. Taya Allah zai bari ki tozarta Rukayya? Addu’ar da kike yi itace ya canja k’addarar ki Allah ya fito miki da miji mai nagarta ya aura miki shi a lokacin kad’an wanda baki yi tunanin hakan ba.”

Kuka Rukayya take yi sosai wanda ake jin sautin sa sosai a falon Baba yace, “ba kuka zakiyi ba, ki gode Allah Rukayya yayi miki abinda bai yiwa sauran mata ba yayi miki zab’in da ina tabbatar da baza ki yi dana sani ba. Lokacin yazo ko nace yama wuce daman lokaci baya jira sai dai a jira shi, ke kin jira shi gashi da yazo sai yazo da gaggawa akayi komai aka gama cikin hukuncin Allah.” Kuka take mai sauti Umma kanta kuka take yi domin kuwa taga kalmar LOKACI NE da Rukayya take yawan fad’a mata a yanzu taga lokacin da take cewa zai zo amma bata san ko yaushe ba gashi yazo a lokacin da dukkan basu shirya ba sannan ba suyi tunanin zai zo da sauri haka ba.

Baba yace, “A cikin kwanakin nan za’a yi komai na bikin ki ki tare a gidan ki. Da Muna cewa zamu had’a auren ku dana Zuhra ashe ke lokaci tashin naki yazo na Zuhra bai zo ba kuma lokaci baya jira.” Ya kalli Rukayya yace, “ki gode Allah, kije ki yi sujjjadar godiya ki godewa Allah dan ya yi miki ni’imar da bai yiwa sauran mata ba da yawa ba a duniya, yayi miki zab’in da baza Kiyi kuka ba koda nan gaba. Tunda kika ce kin bashi zab’i bazai miki zab’in da zaki yi dana sani ba. Shi ya halicce ki komai na rayuwar ki shine ya tsara, wannan auren naki ba yana daga cikin hukuncin sa, shi zaki godewa ba kuka ba Rukayya.” Idanun ya ta goge tana Jan numfashi Baba yace, “nasan kina ta tunain waye mijin naki ko?.” Yayi murmushi kad’an yace, “kar ki damu, kije ki shirya an jima mijin ki zai zo ku gaisa ku tsayar da lokacin da kuke ganin kun shirya zaku tare. Tashi kije.”

Jikin ta a sanyaye ta mik’e zata fita sai ta koma ta zauna tace, “Na gode Baba, Allah ya saka maka da gidan aljanna. Allah ya azurta sauran mata da mahaifi kamar ka Baba, bani da abinda zance sai dai nace Allah yasa zaman kabari yafi maka zaman duniya dad’i, Allah ya da ranka yasa ka cika da imani.” Umma tana amsawa da Amin tana hawaye Rukayya ta tashi ya fita jikin ta a sanyaye sosai.

Farin ciki ya hana Rukayya sukuni kuka take yi tana sallar i’sha tana godewa Allah tana murna da ta kasance mai bautawa Allah, tana murna da ta kasance mai mik’a masa lamarin ta, ta gode masa da ya saka mata imanin zai amsa rok’on ta bata tab’a ji a zuciyar ta baya Karb’ar kukan ya ba, gashi ya karb’i kukan ta ya amsa ya kuma biya mata a lokacin da batayi tunanin hakan ba.

Ta jima a sujjada tana kuka tana mik’a godiya ga Allah sannan tayi sallama lokacin Zuhra ta shigo ita kuma ta mik’e tsaye Zuhra cikin murna ta rungume ta tana kuka itama tana kuka. Zuhra tace, “ki gode Allah Yaya, Allah ya share miki hawayen ki.” Kuka take yi sosai kafin ta raba jikin ta dana Zuhra ta k’arasa wajan jakar ta ta d’auko kud’i ta bawa Zuhra tace, “dan Allah kiyi sadaka yanzun nan, ki bawa wanda kika san zai y farin ciki a daren nan Zuhra.” Zuhra ta Karb’a ta fita ita kuma ta zauna a gefen gadon tana jin abun kamar a mafarki wai itama a yanzu matar aure ce.

Tana zaune so take ya tantance yanayin ta amma ta kasa ita dai tasan tana farin ciki a zuciyar ta amma kuma dai taji kamar ba Rukayya ba Umma ta shigo ta zauna a kusa da ita tace, “Rukayya!.” Ta kalli Umma jin sunan da ta kira ya tabbatar mata itace dai Rukayya tace, “Na’am.” Ta sauke numfashi tace, “Mijin ki yazo yana jiran ki a setrroom din Baban ku.”

Gaban ta ya fad’i ta rik’e hannun Umma tace, “Gabana fad’uwa yake Umma.” Umma ta rik’e hannun ta tace, “Nima kaina haka nake ji balle ke Rukayya, fad’uwar gaban ta alkhairi ce a wannan lokacin. Tashi kije kar a barshi yana jiran ki.”
“Umma ji nake kamar bazan iya zuwa ba.”
“Zaki iya, tashi kije Rukayya lokacin da kika jima kina jira ne yazo yanzu, taya zaki ce baza ki iya ba? Mijin ki ne yanzu ba mai neman auren ki ba, tashi maza kije in kin dawo sai muyi magana.”

A sanyaye ta mik’e ta fita daga d’akin cikin hijjabin da ta idar da sallah ta nufi d’akin Baba gaban ta yana cigaba da fad’uwa sosai ba kad’an ba. Kafin ta shiga sai da ta tsaya ta dinga jawo duk addu’ar da tazo bakin ta kamar wacce tayi laifi take tsoron hukunci, “Ki shiga mana Rukayya.” Muryar Baba taji a bayan ta hakan ya saka ta shiga babu yadda zatayi ganin yana tsaye yana kallon ta, kanta yana k’asa k’afar ta kawai take kallo tana shiga ciki. Tsayawa tayi cak ba tare da ta cigaba da tafiyar ba taji anyi murmushi mai sauti ance, “k’araso mana Rukayya, ko nazo nazo na k’araso dake ne?.”

#Mai daki
#Book3
#Nana Haleema
#Paid
#500

Book3
012

Jin muryar wanda bata kawo ba a zuciyar ta ba ya saka gaban ya sake fad’uwa ta d’ago kai ta kalli inda yake yana zaune a cikin manyan kaya shadda fara kal sai kyalli take yi kansa da hula annurin fuskar sa ya bayyana a zahiri kana kallon sa zaka san yana cikin farin ciki sosoi sai murmushi yake yi yana kallon ta tare d’aga mata gira guda d’aya cikin salo na nuna soyayya da shaik’in da yake ciki a wannan lokaci.
Chapter 18 · 0% Book details