Sashe 92
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru kawai tayi bata ce komai ba shima yayi shiru zai sake magana ta rufe masa baki tace, “maimaita maganar shine yake saka ni tunawa da maganar, daina magana a kai shine yake sakawa na manta. In kana so na manta din a bar zancen kawai.” Kai ya d’aga alamun to ya yiwa hannun nata da ta rufe bakin sa kiss ya rik’e ta sosai a jikin sa yana sauke numfashi tace, “kar kace zaka zubar da hawaye dan Allah, kanka yana ciwo zai maka illa hakan.” Yayi shiru baice komai itama tayi shiru sai daga baya tace, “ni yanzu tago ma na aura, komai kuka. Wancan Yusuf din ban taba ganin yayi kuka ba, amma wannan ya rago ne.”
Dariya yayi itama ita tayi dan daman dariyar take so yayi yace, “ni ne ragon?.”
“Eh kai ne.”
“Haka kika ce?.”
“Eh hakan nace sai meye?.” Kallon ta yayi suka had’a ido ya girgiza kai yace, “ki bini bashi, Allah ya sauke ki lafiya zan baki mamaki.” Tayi dariya sosai ta saka gyara kwanciya a jikin sa shima dariyar yake yace, “badai ni ne rago b? Zaki gani.” A haka bacci ya d’auke shi ta kalle shi ta sauke numfashi a zuciyar ta fata da burin Allah yasa ya zamar mata haka har abada da tafi ko wacce mace farin ciki a rayuwar ta.
Bayan kwana biyu.
#Mai daki
#Book3
#Nana Haleema
#paid
Book3
045
Al’ameen tunda yaga Fiddausi ya saka a zuciyar sa ya samu matar aure hakan ya saka ya tambayi Ameena cikin hikima kuma bata gane ba ta fad’a masa har gidan su bata san abinda yake so ba kenan. Yana dawowa daga Abuja gidan su ya samu mahaifin ta kai tsaye ya sanar dashi waye shi da kuma alaqar sa da Adam da kuma abinda ya kawo. Abba yayi farin ciki sosai ya kuma bashi damar zuwa ya smau Fiddausin.
Da labarin yaje mata ita rasa gane waye ma Al’Ameen tayi kanta ya kulle dan bata gane ba amma tayi farin ciki sosai da sosai ko babu komai addu’ar ta ta karb’u Allah ya yafe mata ya kuma yo mata Zab’i na gari. Ranar da Al’ameen zai zo gabad’aya rasa nutsuwa tayi har sai daka ce gashi sannan ta samu ta daidaita kanta ta same shi a d’akin Abba ta shiga da sallama ya amsa.
Fiddausi ta gaishe shi ya amsa yana yace, “Malama Fiddausi sunana Al’ameen abokin Adam Yayan Ameena kawar ki. Na ganki a gida Ameena dana tambaye ta sai yake fad’a min baki da aure da bayanan ta tayi amfani nazo inda kike. Allah yasa zaki karne ni hannu biyu.” Fiddausi tace, “Allah sarki, na gode sosai da ka zab’e ni, amma Ameena bata baka labarina ba?.”
Yace, “bata fad’a min komai ba saboda iya abinda na tambaya kenan.”
“Da ka sani ka tambaya dan kasan Wacece ni kafin ka kawo kanka gare ni.”
“Gani gaki zaki iya sanar dani wacece ke.”
Fiddausi tace, “Nidai na tab’a aure har sau biyu, son zuciya da son duniya ya raba ni da gidna mijina na farko na auri mijina na biyu Wanda gidan ya kasance tamkar wuta saboda bala’i da uqubar dana tsinci kaina a ciki. Sakamakon son zuciyata shi na girba a gidana na biyu a nan na fahimci meye duniyar a nan nayi dana sanin duk abinda na aikata domin kuwa irin rayuwar da nayi a cikin gidan din mai muni ce duk tunanin ka bazai kawo hakan ba shiyasa har ka kawo kanka wajena matsayin mai sona. Dan da ace kasan abinda na aikata baza kazo kace kana sona da aure ba.”
Al’ameen ya zare glasses din idanun sa yace, “inda zaki fad’a min da kin cire ni daga rud’ani.” Ta sauke numfashi tace, “bazan maka k’arya dan na aure ka ba, zan fad’a maka dan nayi alqawarin babu wanda zan b’oyewa abinda ya faru dani koda zai fasa aurena sai dai ya fasa nidai na fad’i gaskiya. Na auri Alhaji Bello Sagagi nasan ka sanshi nayi kwanan farin ciki na wasu y’an kwanaki kad’an kafin farin cikin ya gushe daga duniya ta bak’in ciki ya maye gurbin sa.”
Kallon ta yake itama ta kalle shi tace, “Ya kasance dan homosexual ne, kuna nima ban tsallake ba yayi amfani dani sau d’aya.” Ta sake kallon sa dan tana son ganin yanayin sa tace, “wannan shine Gaskiyar magana, bana karya bazan kuma fara a kanka ba. Yayi amfani dani ta k’arfi bayan ya saka an d’aure ni, koma dai meye na aikata ba ban aikata ba. Wannan itace rayuwar Fiddausi a takaice. İn kuma kana so Kaji cikakken labarina zaka iya tambaya ta sai na fad’a maka..”
Ya kalle ta sosai dan ta burge shi yana qaunar wanda zai fad’a masa gaskiya a cikin lamarin sa babu b’oye-b’oye hakan ya saka ya zuba mata ido ya kuma ji tausayin ta sosai ganin ta goge hawaye. Al’ameen yace, “Zanen k’addarar ki kenan Fiddausi ko wanne bawa baya tsallake kaddarar sa, rabon ki fahimci kuskuren ki shine ya saka kika kai kanki gıda na biyu, kuma in ka tuba kayi nadama shikenan rayuwar ka zai zo da sauki kuma zaka ga sakamako mai kyau a lokacin da bakayi tunani ba Allah zai maka canji dan addu’a b’ata fad’uwa kasa a banza.”
Fiddausi ya girgiza kai ta goge idanun ta tace, “Haka ne, amma ni na cire rai da samun jin dad’i a duniya, fatana Allah yasa na cika da imani.”
“Haba kamar ba mai ilimi ba? Ai ba’a cire rai daga rahama Allah har a kwanta a kabari, Kiyi hak’uri ki ta addu’a alkhairi yana nan zuwa a gare ki. Sannan ina so daga ni kar wanda ya sake jin maganar nan. Gaskiyar ki da kuma yadda kika fad’a min baki b’oye min ba ya saka na sake jin gamsuwar auren ki domin baki aikata kina sane ba.”
Ta kalle shi da sauri jin abinda yace ya girgiza mata kai ya mayar da abin idanun sa sannan yace, “kar ki damu chanji yazo a rayuwar ki in sha Allah, zan wanke dukkan wannan baqin da ya shiga rayuwar ki, zan maye gurbin sa da fari duk abinda zai sanya ki farkn ciki zaki samu a tare Dani da izinin Allah” ya fad’a yana tashi yace, “ki bani lambar ki” ya fad’a yana bata waya ta karb’a hannu yana rawa ta saka masa dan abun take gani kamar a mafarki kamar sa yace yana sonta kuma yaji abinda ya faru da ita ya amince, ganin hakan sai yayi murmushi yace, “zamu yi magana in sha Allah” ya ajjiye mata rafar kud’i yace, “a gaida mutanen gidan, zan dawo zuwa lokacin magana mai k’arfi a shiga tsakanin mu” ya fad’a yana fita Fiddausi ta dinga kukan farin ciki.
A haka ya shiga gida tana kukan murna da farin ciki Allah ya kawo mata chanji a rayuwar ta Maman ta sai da tayi kuka itama musamman lokacin da Abba yake sanar dasu waye Al’Ameen sannan ya kuma amince yana kuma yi mata fatan samun sa a matsayin miji saboda ya cancanci ya kasance miji a gare a gare ta saboda ya had’a abubuwan da ake nema a wajan miji na gari.
Bayan wasu kwanaki.
Cikin ikon Allah aka fara shirin bikin Fiddausi da Al’ameen babu wanda ya kai Ameena murna da farin ciki dan ta taya kawar ta murnar samun sa ta kuma yi farin ciki da hakan. Sai da Abba ya saka akayi gwaje gwaje na cuwuka Allah ya taimaka babu wani ciwo a tare da Fiddausi sannan aka saka lokacin biki cikin lokaci kad’an akayi komai aka gama amarya Fiddausi ta tare a gidan mijin ta cikin sabuwar rayuwar da tayi mafarki a baya, a wancan lokacin bata samu ba sai yanzu da bata yi tunani ba allah ya bata ya had’a mata biyu ya bata rayuwar jin dadin da kuma kwanciyar hankali saboda kaddarar da ta karb’a ta kuma mayar da komai ga Allah. Ta kuma yi nadama ta k’arbi kuskuren ta ta amince yayi ta rok’i Allah akan ya canja mata kuma ya canja mata.
Rukayya sun koma Abuja a can suke rayuwar su da İbrahim sai dai ace Alhamdulillah domin kuwa yayi k’arfi cikin lokaci kad’an saboda ya rik’e addu’a ga kuma addu’ar iyaye ta rike shi a duk inda yake da kuma mace ta gari da take taya shi addu’ar dan ganin sun cigaba shi da ita.
Ameena ta haihu ta sake haihuwar mace aka saka mata sunan Maman ta Sa’adatu ake kiran ta da Nayla. Zaman farin ciki a gidan ta ba’a cewa komai domin kuwa ta tabbatar wani komawa gidan tsohon mijin alkhairi ne ba ko wanne ne yake zama abinda aka bari shi zaka tarar ba nata dai ya canja da gaske har zuciyar sa abinda ya rage kad’an ne a cikin halayyar sa.
Asiya kuwa ana nan jiya e yau babu wani cigaba a rayuwar su an samu Momi ta shiga dakyar cikin dangi Fauziyya ma an d’auka dakyar amma Asiya kowa akace sai yace sam shi bazai iya ba b’arauniya ce kuma ta raina kowa a haka suke zaune a gida ita da Maimuna babu mai so balle ya taya koda wasa duniya tayi musu zafi. Umma tayi nadama itama tayi danasanin tarbiyyar da ta d’ora su a kai wacce ake musu gori ko a cikin dangin tana kuma yi musu fad’a akan ake su d’ora nasu yaran a turbar da ta d’ora su.
Yusuf suna tare da Ameena a ranar Asabar kwana biyu da dawowar su daga Germany yaje yaga likita akan ciwon kan da bai kyale shi ba suna tafiya da yamma a mota kai da ka gansu Kaga masoya suka je gidan Yaa Adam da ya dawo yana Kano a lokacin. Suna shiga ta tarar da Al’Ameen a zaune ganin sa sai tayi murmushi tace, “Lah Yaya Al’ameens kana nan?.” Yayi murmushi yana kallon ta shima Adam haka suka zauna kafin suyi magana Adam ya kalli Ameena ya kalli Yusuf ya ce, “Yusuf ka rik’e amana ka kuma cika alqawari, ka tabbata mutum mai karbar gyara da kuskure a rayuwar sa. Naji dadin chanjin nan na tabbata ko babu raina zaka kula da Ameena har abada.”