Sashe 3
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rukayya tayi shiru bata ce komai ba har lokacin ya ake cewa, “Na amince dake dari bisa dari zuciyata ta amince da auren ki, ban san naki b’angaren ba zaki amince ko kuma akasin hakan. Ina rok’on ki dan Allah in zaki amince dani ki amince dani dan Allah, in kika tashi akasin haka ma ki k’i ni saboda zuciyar ki badan wani dalili naki ba.” Rukayya ta d’ago idanu ta kalle shi ta girgiza kai tace, “har yanzu in na kalle ka ina kallon ka matsayin mijin k’awata wacce nasan sirrin gidan ta, bana jin zan iya abinda kake cewa domin ina kallon abun tamkar cin amana.”
“Amma ai na rok’e ki nace miki kar ki tuna baya ki d’auka baki san Ibrahim ba yanzu yazo gare ki, wannan ne kawai zai baki damar amfani da zuciyar ki Rukayya. Amma in kika kalle ni ta wannan fuskar da kike fad’a zaki amfani da tunani ne kawai ba tare da zuciya ba.” Ganin tayi shiru bata ce komai ba yayi murmushi yace, “Na gode da damar ganin ki da kika bani, ina fatan sake dawowa a sake maimaita irin wannan zaman, amma ina fatan salon kalaman ki zuwa lokacin sun canja.” Ya mik’e tsaye yana kallon ta daga zaune ko motsi bata yi ba yace, “na barki lafiya Malama Rukayyan Ibrahim, ki gaida mutanen gidan” yana fad’a ya fita ya barta a zaune a wajan zuciyar ta na sake maimaita mata _Malama Rukayyan Ibrahim._
Har Baba ya shigo bata sani ba ya kalle ta yace, “A’a Rukayya baki shiga gidan ba? Lafiya dai ko?.” Ta kalli Baba tare da mik’ewa tace, “Lafiya lau Baba, yanzu zan shiga” ta fad’a tana wuce Baba ta shiga cikin gida ya bita da kallo yace, “Allah yasa lokacin tashin ki yazo Amin.”
Rukayya tana shiga falon Umma suka had’a ido da Umma tasan feedback take so ta bata sai ta zauna kusa da ita tace, “Umma Mun gama.” Umma tace, “to kin amince dashi?.” Shiru tayi ta sauke numfashi tace, “wallahi bana ce ba Umma, amma ki taya ni addu’a kawai Wanda ya kasance alkhairi a gare ni Allah ya zab’a min.”
“Amin” Umma ta furta a takaice ita kuma ta mik’e ta shiga d’aki.
Tana shiga wayar ta nayi k’ara taga sunan Umar ta tsaya tana kallon wayar ba tare da ta d’auka ba, Umar yana sonta sosai yana kuma qaunata ta sani, gashi dan gayu matashi mai kudi mai kyau, in ta aure shi ita kanta tasan ayi dacen wanda yake sonta. Gashi yasan dajarar iyalan sa sau d’aya bai tab’a yi mata maganar matar sa ba balle ya aibata ta akan wani abun. Kulle ido tayi ta bud’e ita bata da zab’i kawai ta barwa Allah zabi wanda ya zab’a mata shi zata karb’a hannu biyu.
A can New York bayan sun gama waya dasu Ameena tana zaune a gefen gado Alhaji ya shigo ya kalle ta sai ya d’auke kai ya karasa inda ya ajjiye kayan ya bud’e ya d’auki abinda zai d’auka ya mayar ya rufe har lokacin bai kalle ta ba.
Da sauri ta tashi ta tare gaban sa tana kallon sa tace, “Haba Baby wai fushi kake dani haka?.” Bai mata magana ba ya wuce ta ta bishi da kallo har ta daina ganin sa ta zauna tana kallon wani wajan daban zuciyar ta babu dad’i ko kad’an dan tunda taga yayi haka tasan fushi yayi. Kaya ta saka kamar yadda ta saba tsukewa dan wandon da ta saka iya rabin cinyar ta ya rufe, rigar kuwa gabad’aya cikin ta a waje yake haka bayan ta ma an kwashe tsakiya.
Tayi kyau sosai ita kanta ta sani domin jikin ta akwai d’aukar kwallaiya ta fito ta zuba tea da yake cikin kettle ta fara sha ta zauna a falon tana zaman jiran dawowar sa. A lokacin su dare yayi dan akwai tazarar awa shida tsakanin su da Nigeria amma baza kace dare bane saboda hasken da yake cikin falon. Tana zaune tana kallon tv tana shan tea ya sake shigowa tana ganin sa sai ta ajjiye tea din ta mik’e tsaye ta k’araso kusa dashi tana kallon sa shima iya yake kallo tace, “Baby wai fushi kake?.”
Hannun ta ya rik’e dan bazai iya tsallake tarkon nan nata ba yace, “ba fushi nake ba Baby, kawai ina mamaki daman akwai abinda zan nema na rasa a wajan ki?.” Jan ta yayi zuwa kan kujera ya zauna ya zaunar da ita a jikin sa yana shafa jikin ta tace, “To ai na baka hak’uri kuma na fad’a maka hakan sab’on Allah ne kaima kuma ka san da hakan.”
Ya juyo da fuskar ta yana kallon ta yace, “Na fad’- miki ba halina bane kawai ina so na tabbatar da abinda ake fad’a min ne.”
“Ai bai kamata ma ka dinga mu’amala da irin wannan abokan ba Baby, duk wanda zai dinga sab’awa Allah har ya dinga baka labarin dadin abun ai ba na gari bane Babyyyy…” ta ja sunan da k’arfi cikin wani salo mai daukar hankali a lokacin da yake tsaka da shafa jikin ta.
Bai sake mata magana ba itama bata kuma cewa komai ba domin bata hayyacin ta shima a lokacin haka shafa jikin ta yake yi har ya raba ta da komai na jikin ta cikin soyayya da shauk’in junan su. Sun yi nisa dukkan su babu kamar ita da take kasa yana sama yadda yake sarrafata ya saka idanun ta a kulle yake gabadaya jikin ta ya gama yin sanyi.
Jin abinda yake kokarin yi ya saka ta zabura ta ja baya ta fad’o daga kan kujerar tana kallon sa tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudu tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta, zata yi magana yayi saurin zuwa kusa da ita yace, “Fiddausi dan Allah ki barni iya yanzu kawai daga yanzu bazan sake ba dan Allah ki barni.”
Fiddausi tayi d’aki da sauri jikin ta yana rawa sosai ta rarumi towel ta daure jikin ta tana sauke numfashi kamar tayi gudu mai tsahon gaske zuciyar ta sai bugawa take, a lokacin ya shigo yana cewa, “Yanzu Fiddausi daman baza ki iya bani abinda nake so ba?.”
“Bazan iya ba wallahi bazan bari kayi luwad’i dani ba, ni musulma ce bazan sab’awa Allah ba akan gwaji kawai, bazan iya ba ka hak’ura da gwajin dan bazan tab’a aikatawa ba.”
Ya matso ya rike kafadarta yace, “na fad’a miki ba halina bane, an fad’a min dad’in da abin yake dashi Ina so na gwada kuma ke kadai nake da ita Fiddausi. In ba’a wajan ki baba wajan wa zan samu? Dan Allah ki taimaka min kar kiyi min haka.”
Fincike jikin ta tayi tace,” Zan iya yi maka komai amma banda na bari kayi amfani dani ta baya ba, kayi hak’uri bazan iya ba wallahi.”
“Na fad’i miki bawai ina son hakan bane zan gwada ne kawai.”
“Gwajin ma wani babban zunubi ne tunda kasan sab’on Allah zaka yi, kasan haramcin abinda kake niyar aikatawa dan haka laifi kake kokarin yi? Kasan da cewa al’arshi girgiza yake a duk lokacin da aka aikata abinda kake niyar yi dani da sunan gwaji?. Wallahi bazan ba na fad’a maka.”
Da hannu ya tankad’a ta fad’a kan gado ya saka k’afa ya take hannun ya yace, “Ko bakya so sai na gwada a wajan ki kawai zan d’and’ana naji abinda ake ji.” Ganin da gaske yake yi fa ya saka ta dage ta ture shi ta shiga bandaki a guje.
K’ofar ya k’arasa yana bubbugawa yana fadin, “Fiddausi! Ki bud’e ko ka b’allakofar, bana son shirme ki bud’e nace Malama.”
“Wallahi bazan bud’e ba, bazan bari ka saka na aikata babban laifi daga cikin manyan laifuka ba” ta fad’a muryar ta har rawa take yi kamar zatayi kuka.
“Shikenan na fasa amma ki fito.”
“Bazan fito ba.”
“Shikenan na fita” ya fad’a tana barin wajan da sauri. Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta fito tana sauke numfashi tana lek’owa kamar munafuka ganin baya nan sai tayi sauri k’arasawa ta kulle k’ofar ta jingina da k’ofar tana sauke numfashi.
A hankali ta k’arasa ta zauna akan kujera tana kallon d’akin kamar da wani abun a ciki tace, “na shiga uku, me hakan yake nufi wai?.” Gumi ne yake tsatstsafo mata ta saka hannu ta share gumin ta kwanta da baya ta rasa tunanin me zatayi. Hankalin ta ya tashi sosai abinda ko a mafarki bata zata ba sai gashi yana k’ok’arin faruwa da ita.
Sau hud’u kenan yana yunkurin yin luwadi da ita shin bai tab’a tsamari kamar yau ba, sai tayi magana sai yace wai labari aka bashi gwaji yake so yayi yaji ya ake ji. Hannu biyu ta saka ta dafe kanta sai kuma ta mik’e jikin ta a sanyaye ya koma band’akin. Ta jima a cikin sannan ta fito ta saka doguwar riga ta fito falon ta kalli kayan ta na d’azu ta tsuguna ta kwashe kayan ta ajjiye akan kujera ta zauna sharaf akan kujerar tana sauke Ajiyar zuciya cikin tunani.
Tun tana zaman na dad’in rai har ta gaji babu shi babu alamun sa, a nan bacci ya kwashe ta har alarm d’in wayar ta da yake tashin ta da asuba ne ya buga ta tashi tana kallon falon kafin ta mik’e ta shiga d’aki taga baya nan alamun bai dawo ba. Alwala tayi ta dawo tayi sallah tana zaune akan sallayar sai kuma bacci ya kwashe ta akan sallayar.
Bubbuga hannun ta taji ana yi hakan y saka ta bud’e ido ta tashi zaune tana kallon sa shima haka sai yayi murmushi yace, “a nan kika kwana ne?.” Ta girgiza kai alamun A’a kafin tace, “da na idar da sallah ban San bacci ya d’auke ni ba.”
“Tashi ki zauna sosai to” ya fad’a yana mik’ar da ita ta zauna akan gadon ya zauna kusa da ita yace, “kiyi hak’uri abinda ya faru jiya bazan sake ba kin ji.”