← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 93

Sashe 48

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rukayya ta girgiza kai tace, "baki da laifi ko a wajan Allah, Allah yana gani fin karfin ki akayi."
"Da ban kai kaina bafa Rukayya? In da nayi zamana a inda Allah ya barni da yanzu ina nan hankalina kwance bani da wata damuwa ko fargaba. Amma na sakawa idanuna kwalli bana tuna komai bana hangen komai sai y'an uwan  da Ameena da Zakiyya, Kullum tunanina suna cikin jin dad'i ina cikin wahala, Kullum tunanina suna sama ni ina k'asa, Kullum hangena taya su suna hawa mota ni ina hawa napep? Taya su suke kwana a gida manya ni ina kwana a k'aramin gida?. gashi naje ga jin dadin ya zame min babban tashin hankali da ban tab'a zaton zan tsinci kaina a ciki ba. Ina ma na mutu na huta" ta fad'a tana sake fashewa da kuka salak mai tsuma zuciya ya kwantar da kanta a kafadar Rukayya tana kuka sosai.

Ameena tace, "k'addarar ki kenan, ko wanne bawa baya tsallake k'addarar sa. Kiyi hak'uri ki daina kuka." D'ago kanta tayi ta goge idanun ta tace, "kuka ya zamar min dole na tabbata yanzu ma na fara, Abba ko kuka ni bayayi saboda ya samu labarin kaf abinda ya faru kafin na auri Bello, haushina yake ji sosai ko gaisuwa ta baya amsawa. Ko iya wannan ya ishe ni tashin hankali."
"Kin b'ata masa rai ne a baya amma zai yafe miki in sha Allah" Ameena ta fad'a tana kallon ta.

Ta sauke Ajiyar zuciya tace, "Ko Ina da cutar hiv ma ban sani ba." Rukayya tace, "Haba Fiddausi baki da komai in sha Allah. Ki daina wannan fatan k'addara ce kuma kin gane kuskuren ki komai ya wuce." Murmushi tayi tana hawayen da yak'i tsayawa tace, "Son zuciya ya kaini ya baro ni, duk da akwai zugar Zakiyya amma ban d'auke shi komai ba don daga zuciya tane ba daga kalaman Zakiyya ba." Rukayya tace, "duk da haka zugar ta tayi tasiri a kanki, da tana nuna miki abinda kika yi ba daidai bane da wani abun baza kiyi ba. Komai take kika yi itace ta zuga ki, in kina da laifi a cikin d'ari kina da sittin ita kuma tana da arba'in, itace take d'ora ki akan komai. Ko hıra da shi Bellon da bata baki fuska ba da baki yi a gidan ta ba."

"Wallahi ba komai bace, son zuciyata ne dan da niyar hakan daman a zuciyata. ku meyasa batayi tasiri a kanku ba sai ni? Saboda zuciyar ku a wanke take kin saka niya mai kyau ni kuwa fa?." Sukayi shiru dukkan su kamar gidan rasuwa babu mai magana kafin Zakiyya tace, "ni kaina gashi ta dalilin hakan aure na yane neman b'allewa, na tabbata kuma hakkin hakan ne yake bibiyata."

Babu wanda ya iya magana a cikin su Ameena tace, "tun wancan lokacin da kike hangena Fiddausi kin fini kwanciyar hankali, dan baki San irin damuwar da nake ciki a gidan bane shiyasa nake burge ki a ko yaushe dan a ganin ki ina cikin kudi da jin dad'i bani da matsala. Ita Rukayya tazo ta tarar da kad'an daga cikin wani abun wancan lokacin, dakyar rana ta fito ta koma banyi kuka ba, na shiga tashin hankalin da baki san na shiga ba, kwanciyar hankali d anutsuwa na minti d'aya bani dashi a wannan gidsn da kike hangena. Shiyasa nake ce miki ki gode Allah yayi miki ni'imar da bai yiwa sauran mata ba amma sai kice kee ba haka ba kudi kawai shine kwanciyar hankali, ina sha'awar rayuwar gidan ki na wancan lokacin, saboda kwanciyar hankalin da kike da ita akwai nake hange, ke kuma kudin da nake ciki kike hange babu ruwan da da akwai kwanciyar hankali ko babu. At the end gani yanzu a gida babu auren."

Fiddausi ya kalle ta da sauri tace, "kina nufin Kun rabu da Yusuf?."
"Da kika tashi ai ba gidana kika je ba ko?."
"Wai yanzu babu aure tsakanin ku kenan?." Ameena tayi murmushi tace, "Babu Fiddausi, amma hakan yafi min dadi na samun kwanciyar hankalin da na rasa a gidan sa, kud'i ba komai bane ba wallahi indai babu kwanciyar hankali. Domin babu abinda zasu yi miki kina kallon su sun zama hoto, in kuwa akwai kwanciyar hankali haka za'a dinga ganin ki kin yi k'iba abin ki ko babu kudi zaki yi kyau kowa ya ganki sai yayi sha'awar ki." Fiddausi tace, "na tabbatar wallahi, ni zan bawa wani labari a yanzu Ameena. Rayuwar da nayi a gidan sa kamar rayuwar dabba haka yake komai nashi, nayi dana sanin abinda na aikata Allah y sani. Lokacin baya kuwa har Mama cewa take sai dai su Yaya su nuna min manyan gıda amma badai kwanciyar hankali ba, amma sai naga kamar ci min fuska suke yi."

Rukayya tace, "sai ki gode Allah da ya ganar dake kuskuren ki tun yanzu, wahalar da kika sha kuma Allah ya sa ta zama silar wankewar zunuban ki." Ta sauke Ajiyar zuciya ta amsa da Amin Rukayya ta tashi zuwa kitchen Ameena ya tashi tabi bayan ta yana cewa, "ruwa nake son sha." A tsaye taga Rukayya tace, "nasan bayan wannan labarin na Fiddausi akwai abinda yake zuciyar ki, koda wasa kar ki nuna wani abu matar ibrshim ce ke a yanzu Fiddausi kuma matar Alhaji Bello." Tana fad'a mata hakan ta fita ta kyale ta ita kuma ta dawo da da ruwa da lemo a hannun ta.

Fiddausi ta kalle tayi murmushi tace, "kin yi nauyi Ashe." Murmushi itama tayi ta zauna tace, "me zan dafa mana muci." Fiddausi ta dafe kai tace, "kaina ciwo yake." Ameena tace, "daman bai kamata ki fito a wannan yanayin ba, kamata yayi a sanar damu muzo har gıda da kanmu." Fiddausi tace,  "nayi kewar ku ne sosai shiyasa, kunyar Mama nake ji da Abba shiyasa bana son zaman gidan."

Rukayya tace, "yanzu ya za yi da auren sa da yake wuyan ki?." Ta girgiza kai tace, "wallahi ban sani ba Rukayya, abinda na sani kawai na gama auren ko me za'a yi min bazan koma ba."
"Babu wanda zaice ki koma a irin wannan yanayin ai" Zakiyya ta fad'a tana kallon ta da tausayawa.
Ameena ta mike tace, "nice mai Lafiyar cikin ku bara nayi mana abincin." Shiga kitchen din tayi ta barsu shiru kamar gidan mutuwa babu mai magana a cikin su.

       Har aka gama abincin aka kawo babu wanda yace komai kuma sunci sosai ba kowa da abinda yake ransa dukkan su. Sallah ce ta saka suka tashi sukayi alwala sukayi sallah a lokacin sai da suka sake yin kuka saboda yadda Fiddausi yake addu'a a fili tana hawaye. Suka dinga rarrashin ta suna bata kalamai masu dad'i.
Fiddausi ta kalle su tace, "ina son ganin d'ana amma bani da karfin guiwar zuwa inda yake." Babu wanda ya amsa mata ta sake cewa, "har baban nashi ina da buk'atar ganin sa domin ma bashi hak'urin abubuwan da suka faru, nayi kuskure mai yawa duk da nasan babu lallai ya yafe min. Ku taimaka min na ganshi na bashi hak'uri ban san a inda zan ganshi ba." Nan ma shiru babu wanda yayi magana Rukayya ta kalli Ameena da Zakiyya suka had'a ido ta sauke numfashi bata ce komai ba.

Horn Rukayya taji a waje ta tashi tace, "ashe yau Alhamis, ina zuwa" ta fad'a tana tashi zuwa waje jim kad'an suka shigo da Amir jakar hannun sa tana hannun ta shi kuma ya rike luch box. Sallama da yayi ya aka Fiddausi ta kalle shi gaban ta ya fad'i tana kallon sa cike da mamaki yace, "Anti Ameena ina yini." Ta amsa yace, "Anti Zakiyya ina yini." Itama ta amsa tana murmushi ya kalli Fiddausi yace, "ina yini" yana fad'a ya wuce alamun bai gane ta ba.

Rukayya ta rik'e shi yace, "Ammi Yunwa nake ji." Ta kalle shi tace, "ga Maman ka" ta fad'a tana nuna masa Fiddausi da take kallon su da mamaki kamar idanun ta zai fito waje. Kallon Fiddausi yayi ya kalli Rukayya yace, "Mama na" ya sake kallon Fiddausi dan bai gane ta ba ya matsa kusa da ita tana kallon sa yana kallon ta. "Amir dina" ta fad'a murya tana rawa tana kallon sa shima ita yake kallo dan bai manta ta ba kawai dai ta canja masa ne.
Ta rungume shi sosai a jikin ta tana kuka sosai tace, "kayi hak'uri Amir kayi hak'uri ka yafe min ka aikata kuskure babba Amir, ka yafe wa Maman ka."

Sakin sa tayi ta rik'e fuskar sa tana kallon sa shima haka da alama har lokacin mamaki yake yi ya kalli Rukayya yace, "Ammi da gaske Mama ce?." Ta d'aga masa kai alamun eh yace, "kince taje Unguwa ta dawo?." Nan ma ta d'aga masa kai alamun eh ya kalle ta yace, "kika je unguwa kika barni, ni bana kula ki Ammi ce take sona." Lumshe ido tayi sai ga hawaye tace, "kayi hak'uri Amir yanzu na dawo babu inda zan sake tafiya." Dariya yayi yace, "fitsari nake ji" ya fad'a yana barin wajan da sauri.

Fiddusi ta kalli Ameena ta kalli Rukayya ta kalli Zakiyya tace, "Ya akayi Amir yake hannun ki?."
"Saboda mahaifin sa ta aura" Zakiyya ta fad'a tana kallon ta. Fiddausi ta kalle ta tace, "mahaifin sa? Kina nufin İbrahim?." Ameena tace, "yana da wani a mahaifi ne bayan sa?." Ta kalli Zakiyya tace, "amma kika ce min ba shi bane wani ne daban Mu'azzam." Zakiyya tace, "wancan Ibrahim din da kika sani daban da Wanda ta aura, shiiyass nace miki haka amma ai kin san mahaifin Amir ko? to shi ta aura. Amma ba Ibrahim din ki bafa wannan Mu'azzam sunan sa." Gaban Fiddausi ya fad'i matuk'ar ta juyo a hankali tana kallon Rukkaya kamar yadda take kallon ta.
Chapter 48 · 0% Book details