Sashe 59
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma Sakina tace, “Kamar yadda nazo nace miki auren su zai yu sai ya aure ta koda baya so yanzu nazo nace miki auren ya mutu ki yarda kawai.” Umma tace, “bazan yarda ba Sakina gaskiya, ina akace auren nan ya mutu ina zan saka raina .”
“To sai ki je da kanki ki yi duk abinda ya kamata Nidai bazan wahalar da kaina ba.”
“Hak’uri zakiyi mu cigaba da nema, wannan arzukin da ake samu duk tare ake ci.” Umma Sakina tace, “ba fa zai mayar da ita ba, Asiya tana da laifi a lamarin nan, na farko ke shaida ce bata da kunya, na biyu ga shegiyar k’azanta sannan ga satar da take yi masa dole koda aikin mu a kansa sai ya gaji. Ki tuna daman fa shi ba auren Asiya yazo yi ba, mu ne muka ga yana niyar guduwa muka kama shi yanzu kuma abinda muka saka muka d’aure shi ya sake shi tunanin sa ma shi ya akayi ya aure ta, kinga sai muyi hak’uri Allah ya kawo wani.”
Umma tace, “A’a dan Allah ki daina fad’ar haka, haka za’a yi hak’uri mu cigaba da nema ai bamu san inda za’a dace ba. Nawa muka samu da auren zai mutu yanzu fisabinillahi?.”
“To nidai na gaji Atika nayi iya yiwa wai uwar y’a ta siyi cokali.” Ta kalli Asiya tace, “kalle ta dan Allah kamar tsohuwa ba dole ma ya gaji da zama da ita b?, daman abinda muka yi ne ya rik’e shi yake hak’uri haka amma yanzu bazai iya ba, ni da naje gidan kasa zama nayi a kusa da ita saboda warin da take yi balle shi.” Asiya ta murgud’a mata baki tace, “duk bak’in cikin masu bak’in ciki wallahi sai na koma gidana.”
Umma Sakina tace, “iyeee! Nice nake bak’in cikin Asiya?.”
“To Umma Sakina in ba haka ba meyasa kike cewa wai ya gama aurena?. Kawai dan an fad’a miki sai ki yarda ki dinga k’ararwa aurena ya mutu?, ba dole nace bak’in ciki bane?.” Umma Sakina ta girgiza kai tace, “to bara kiji badan ni ba da yanzu baki auri Yusuf har kin sato abinda kika sato ba, badan ni ba wallahi da yanzu ya jima da yi miki shegen duka ya Koro ki gida ko ya had’a ki da y’an sanda ko y’an daba sun miki duka, ki gode Allah ma da sai yanzu kika dawo gidan. Ga uwar ki nice na shiga na fita akayi auren ku badan haka ba da yanzu kina nan babu mai so.”
“Allah daman yayi sai ya aure ni ko mutum baiyi komai ba, kuma ai naga in na sata har ke ake ci ba iya ni kad’ai nake cinyewa ba. Yauwa, kuma sai na koma gidan mijina wallahi koms mutum zai ce sai dai ya haddiyi zuciya ya mutu.” Umma Sakina ta kalli Umma tace, “Kina Jin abinda take cemin kina kallon ta ko ki bari baza ki ce ba.” Umma tace, “to Sakina ke ce wallahi kamar mai bak’in cikin, taya zaki dinga cewa wai auren ya mutu tsakani da Allah?.” Umma Sakina ta wara idanu ta kalli Umma tace, “Atika ni ce ma mai bak’in cikin? Nice nake yiwa Asiya bak’in ciki akan zata koma gidan Yusuf?. Lallai Atika baki da mutunci daga ke har yaran ki, ni nake yi muku bak’in ciki a akan auren Yusuf yanzu?.”
“Ni bance kina bak’in ciki ba ai, amma yanayin da kike nunawa kina magana kamar bakya son a mayar da auren sa da Asiya wallahi.” Umma Sakina tace, “bana so ta koma din bak’in cikin nake yi, muje a bak’in cikin nake kawai kuma baza ta koma ba.”
Asiya tace, “kin gani ko Umma dmaan abinda yake ranta kenan, k’ila ma ita taje tayi wani abun dan ya sake ni.”
“Kee Asiya dakata! Daga ke har uwar ki ni ba sa’ar yin ku bace nafi k’arfin ku walalhi, ki saita harshen ki kafin nayi miki dukan da zan b’alla miki d’aya hannun. Uban me nake samu da zaki ce bak’in ciki nake yi? Uban me Uwar tak’i take min ko ke me kike yi min?. Yusuf din waye da zanyi bak’in ciki a kansa? Waye shi a Nigeria fad’a min na nawa ne shi a jerin masu kud’in Nigeria?.”
Asiya tace, “Bak’in cikin dai ya fito.” Bata san ta mari Asiya ba sai da taji Umma tace, “Yanzu meye na dukan ta kuma dan Allah? Daga magana sai ya zama fad’a?.” Umma ta kalle ta tace, “ni zaku fad’awa Ina bak’in ciki akan lamarin Asiya? Duk abinda nayi baku gani ba sai da komai ya lalace zaku ce nice nake muku bak’in ciki?. A gaban ki take min rashin kunya kin kasa yi mata magana abinda banyi zaton faruwar sa ba. Na d’auka uwa suke d’auka ta kamar yadda suke d’aukar ki domin ina shiga na fita a cikin lamarin su ba tare da na gajiya ba. Ashe rashin mutuncin da rashin tarbiyyar da ake fad’a a kan gidan nan gaskiya ne sai ya yanzu na tabbatar da Hakan, to wallahi daga yau babu ni babu lamarin ku duk abinda da kike ganin na gaza kuje ku yi da kanku” ta fad’a tana d’aukar jaka zata fita Umma tace, “Ko da ke ko babu ke zamu yi ai da zamu iya, ya zaku dinga mana gori kamar kece kika had’a auren nasu tun farko?.” Umma Sakina tace, “Allah ya bada sa’a, kud’ina da nake bin ki kafin naje gida a tura min babu d’aga k’afa wallahi daga yau in ba’a turo min ba ke kin San abinda zanyi” Tana fad’a ta fita Umma tace, “a je dai, kud’i zan biya ai akwai kud’i a wajan Asiya zan biya ki kije can ki k’arata. Na daina had’a sirrina da ko wacce k’awa walalhi, kawai Kizo kina cewa wai auren ya mutu kenan har abada.”
Asiya tace, “ai duk laifin ki ne Umma da kike sauraren wannan figaggitar matar.”
“Ai yanzu komai ya wuce, kina ji tura mata dubu d’ari biyar shine kudin da take bina. Har tayi min gorin kud’i nida nake dake?.” Asiya tayi sak tace, “Dari biyar Umma? Haba ku dinga tausayi na mana yanzu da ba auren nan ne dani ba balle in wannan sun k’are a samo wasu, in na bada dari biyar ni kuma fa dan Allah?.” Umma ta kalle ta da mamaki tace, “baza ki bayar ba kenan?.”
“Gaskiya da sauki” ta fad’a tana tashi ta shiga d’aki tana cewa, “haka kawai a tatike min abinda na tara tun ba’a je ko ina ba, Haba ai ya dole ma na koma gidan mijina wallahi na gaji da zaman gidan nan komai Asiya kawo kud’i kamar wata bank?.”
Umma ta bita da kallo ta girgiza kai tace, “Asiya baza ki bayar ba kenan?.” Shiru taji bata amsa ba ta bita tana cewa, “dole ki bada kud’in nan in ba haka ba nafi kowa sanin halin Sakina wallahi. Saboda ke naci bashin nan ki daure ki amince ki bada kud’in, akan ki lokacin da kika sace kudi a account din sa naci bashi akayi aikin aka kuma rufe bakin sa dan haka dole ki biya.” Asiya tace, “tabdi! Nidai gaskiya bazan iya bada wannan kud’in ba” ta fad’a tana sake fita daga d’akin dan da gaske baza ta bayar ba.
Bayan sallar azahar Usman da Yusuf suna zaune a cikin mota a k’ofar gidan Adam Yusuf sai addu’a yake karantawa a zuciyar sa sannan ya daure ya fito dan dole yasan sai ya fito din Usman ma ya fito suka k’arasa wajan mai gadi suka gaisa Yusuf yace, “Mai gidan yana nan?.”
“Baya nan ya fita tun safe amma nasan yanzu zai dawo.” Yusuf ya kalli Usman sai Usman yace, “muje ma dawo anjima.” Yusuf ya motsa kenan zasu bar wajan sai ga motar Yaya Adam ta shigo layin mai gadin yace, “gashi nan ma.”
A k’ofar gidan ya tsaya ya sauke glass ya kalli Yusuf yace, “Yusuf kaine tafe a ranar nan?.” Al’ameen da suke tare ya kalli Yusuf din ya fito daga motar yana kallon sa Yusuf bai ma kula dashi ba yace, “eh, wajan ka muka zo.” Yaya Adam yace, “wajena kuma? To Allah yasa dai Lafiya. Ku shigo mana” sai kuma ya kalli Al’ameen yace, “Dan Allah duk abinda akayi ka tura min na gani bana so lisssfin ya dinga kwace min.” Banza Al’ameen yayi masa baice komai ba sai yayi dariya yace, “Meye na b’ata ran kuma?.” Hararar sa yayi shi kuma yayi ya shiga da motar ciki Yusuf da Usman suka bi bayan sa sai lokacin ya lura da kallon da Al’ameen yake masa duk sai ya tsargu.
Tare suka shiga har falon Zaytun na wasa tana ganin Yaya Adam tayi wajan sa a guje kafin ta k’arasa sai ta hangi Yusuf sai ta canja hanya tayi wajan sa. Yayi dariya yace, “lallai ma yarinyar nan zaki zo hannu na.” Ya fad’a yana zama shi kuma yana rik’e da ita suka k’araso suka zauna Yaya Adam yace, “bamu gaisa bama.” Suka gaisa Yaya yace, “Ya su Alhajin duk suna lsfiya?.”
“Lafiya lau kowa da kowa.”
“To ma sha Allah.” Shiru Yusuf yayi Yaya Adam yace, “ina jin ka, kace kazo wajena, Meya faru?.”
Yusuf ya kalli Usman shima shi yake kallo kafin ya sunkuyar da kansa k’asa yace, “Daman nazo bada hak’uri ne akan abinda ya faru.”
“Hak’uri? Akan me to Yusuf? Meya faru din?.” Yusuf ya kasa magana yayi shiru Yaya yayi murmushi yace, “ya ka kasa magana ka fad’a mana na dawo na gaji Ina so ne huta kafin lokacin sallah yayi.” Yusuf yace, “dan girman Allah Yaya ayi hak’uri da abinda ya faru a baya a yafe min.” Yaya Adam ya bishi da kallo ya girgiza Kai yace, “Wai in an afahimta ayi hak’uri akan abubuwan da ka yiwa Ameena kake nufi?.”