← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 93

Sashe 77

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murna tace, “ai wallahi bazai yi ba kinji ma na rantse.”
“To indai haka ne za so ace ta dawo din dan ni gani nake yadda yake sonta yanzu a baya ma bai sota haka ba, in kuma bata dawo ba wallahi shima zan zo hakan dan ina so ya samu farin cikin da bai bata ba, ke kin sani tamkar jinina nake jin yarinyar.” Murja tace, “to Allah ya bashi Lafiya ya bada abinda yake daidai.” Ta amsa da amin Ameena tana tsaye a bayan su ba tare da sun ganta ba tana jin duk abinda suke fad’a jikin ta ya sake yin sanyi sosai musamman kalaman Ammah da take cewa lokaci yake jira.

#Nana Haleema
#Fitattu biyar
#Mai daki
#Book3

Book3
039

        Ameena da take tsaye a bayan su duk tana jin abinda ake cewa ta sauke numfashi ta samu nutsuwa sosai sannan ta k’araso tana murmushi tace, “Ammah?.” Jin muryar ta sai Ammah ta juyo tana kallon ta murmushi ya bayyana akan fuskar ta tace, “A’a, Ameena kece a nan?.” Ameena tayi murmushi tace, “Barka da Rana Ammah.” Ammah tayi murmushi tana kallon ta cike da so tace, “Barka dai Ameena. Ya makaranta?.”
“Alhamdulillah. Barka da rana” ta fad’a tana kallon ta kusa da Ammah ta amsa tana murmushi itama.

Ammah tace, “Ina Hafsa take?.” Ameena tayi dariya tace, “tana makaranta.” Ammah tace, “Zaytun y’an makaranta, ana shan rubutu. Dan in tazo sai ta zane min ko ina da biro ita ga y’ar makaranta.” Ameena tayi dariya kad’an ta kalli Mubakar da yake dariya yace, “Ai bazan kula ki bane, wai duk nacin Muhammad sai kika zagaye aka barshi a corner.” Tayi dariya mai sauti tace, “Nidai babu ruwana. 
A gaban Ammah nake.” Yayi dariya yac, “Ai tasan labarin.” 

Tayi murmushi kawai Ammah tace, “waye babu lafiya na ganki a nan?.”
“Class mate dina ce babu lafiya shine nazo na duba ta yanzu.” Ammah tace, “Allah Sarki, Allah ya Kara Lafiya.”
Ameena tace, “Amin.” Tana son tambayar Ammah waye a kwance amma kuma ta san amsar a bayyane gani take ta nuna bata sani ba ta tambayi waye dan kula da lamarin Ammah.

“Ammah waye babu lafiya na ganki a zaune?.” Ammah ta kalli Mubakar sai yace, “Yusuf ne wallahi.” Ameena tace, “Ayya Allah ya k’ara Lafiya.” Mubakar yace, “Amin, ko zaki shiga duba shi?.”
Ammah tace, “ita da zata koma gıda me zata je tayi a wajan Yusuf?.” Ameena sai Ammah ta d’aure ta da jijiyoyin jikin ta sai tace, “Ammah ai dan zan tafi bana kasa shiga ba” ta kalli Mubakar tace, “raka ni.” Mubakar ya bud’e d’akin da yake tsaye a jikin sa ta hango Yusuf din a kwance Usman na kusa dashi a zaune.

Shiga tayi da sallama Usman ya amsa yana kallon ta sai ya kalli Yusuf da bai bud’e ido ba yasan kuma idanun sa biyu sai dai baya son bud’ewa saboda ciwon kan da yake damun sa, Usman yace, “Ameena kece da kanki?.” Tayi murmushi tace, “nazo samu ladan duba Mara lafiya.” Usman yayi murmushi shima yace, “kin kyauta ai.” Ta kalli Yusuf da yake a kwance ruwa har gida biyu suna shiga jikin sa ko wanne hannun ta kalli Usmsn tace, “Allah ya kara Lafiya.” Usman yace, “Amin ya Allah. Mun gode sosai.” Murmushi tayi ta juya zata fito taji Yusuf yace, “na gode Ameena, na gode da bani damar sake jin maganar ki duk da ban ganki ba a karo na k’arshe. Na gode Allah ya saki farin ciki kamar yadda kika saka ni yanzu.”

Waje ta kalla sai suka had’a ido da Ammah tana kallo d’akin sai Ammah ta d’auke kai Ameena ta sauke numfashi tace, “Amin.” Tana fad’a ta fita ta dawo wajan Ammah tace, “Ammah zan koma gıda kafin Yaya ya fara yi min waya.” Ammah tace, “ai bara nazo ki sauke ni a gida Mubakar yana nan tunda Usman tafiya zaiyi.” Ameena tace, “To Ammah.” Ta kalli Mubakar tace, “d’auko min kayan nan Ameena zata sauke ni.” Mubakar ya shiga ciki ya d’auki kayan suka je har bakin motar Ameena aka saka kayan a baya suka shiga motar suka tafi.

Ammah ta lura da Ameenan kamar bata cikin walwala tayi shiru bata cewa komai sai Ammah taso kawar da shirin tace, “Ashe bikin ki yazo Ameena babu labari?.” Ta kalli Ammah tayi murmushi tace, “naso sanar dake ke wallahi, ayi min afuwa.”
“Ba wata afuwa, ai na d’auka ni za’a fara kawowa mijin sai gashi a manta ma bani.”
“Allah Ammah ba haka bane ba, makarantar nan ce ga saka ni a gaba” ta fad’a tana murmushi Ammah ma dariya take tace, “Allah ya tabbatar da alkhairi.” Ameena sai taji wani iri a zuciyar ta tace, “Amin Ammah.”

Hira Ammah take ta janta da ita har suka zo gidan Ammah ta fita tace, “Bud’e na d’auki kayana.” Ameena ta fito ta d’auko kayan wayar ta na k’ara ta duba ganin sunan Yaya sai ta d’auka Ammah taji tace, “Ina hanya Yaya.” Ammah tayi murmushi bayan ta kashe wayar tace, “Maza jeki tunda neman ki yake.” Ameena tac, “Ammah a gabana zan bari ki d’auki wannan kayan? Zan shigar miki dasu” ta fad’a tana d’auka ta jefa wayar ta cikin motar ta d’auki kayan Ammah sai murmushi take tana kallon ta suka shiga har falon Ammah ta ajjiye kayan Ammah tace, “Na gode Daughter, Allah yayi albarka.” Ameena ta amsa kafin ta tafi saboda tsoron fad’an Yaya.

Ameena tana komawa gida taga Yaya Adam din ma baya nan tace, “wai daman baya nan yake min waya?.” Yayan Bauchi tace, “baya nan ya fita. Kema ai kin jima daga dubiya sai hira?.” Ameena ta zauna tace, “Ammah n gani fa a asibiti muka tsaya muka gaisa k’arshe ma ni na dawo da ita gida shine dalilin jimawa ta.” Anty Aysha tace, “Waye babu lafiya kuma.” Ameena ta kalle su tace, “Yusuf ne” tana fad’a ta tashi ta shiga ciki duk suka bita da kallo Anty Aysha tace, “Yusuf ya kamata yaci albarkar Ammah Ameena ta amince dashi.”

Yayan Bauchi tace, “naga alama Ameena baza ta amince ba ai.” Anty aysha tace, “Ko yanzu ta amince ai ta bashi wahala.” Sukayi dariya suna hira Ameena tana jin su ta jingina da bango ta lumshe idanun ta. Eh tabbas da gaskiyar su Yusuf ya kamata yaci albarkar Ammah kodan kalaman da taji tana yi a d’azu, Ammah uwace zata so Yusuf fiye da ita kuma in Yusuf ya rasu ta wannan dalilin zata dinga kallon ta kamar itace silar mutuwar d’anta. Ameena a bayyane tace, “in na yiwa Ammah haka naci amanar qaunar da take min, amma kuma taya zan koma wajan Yusuf bayan abubuwan da suka faru?.”

“Indai kin amince zaki koma ki d’auka a ranki baza su sake faruwa ba. Ameena Yusuf yayi nadamar da ya kamata ki gani a zahiri, Yusuf ya cancanci ki tausaya masa kodan saboda mahaifiyar tasa. Ameena son da Yusuf yake miki a yanzu bai miki shi a baya ba kema nasan kin tabbatar da hakan,  a jikina nake jin baza ki sake shiga yanayin da kika shiga a baya ba, domin in kayi sake kwai ya kubce daga hannun ka ya fashe da zarar ka sake samun sa rokon da kayi masa a baya ba irin sa zaka sake yi ba yi ba. Zaka fi yi masa rik’o mai mahimmaci domin tsoron kar ya sake sub’ucewa. Indai zuciyar ki ta amince zaki koma wajan sa kodan saboda Ammah ki koma, na tabbata da zarar kin koma zaki ji a ranki duk soyayyar da kike masa a baya tana dawowa a hankali Ameena.” Yayan Bauchi ta fad’a tana kallon ta itama ita take kallo.

Ameena ta fara hawaye tace, “tsoro nake ji Yaya, bana son sake shiga yanayin da na shiga a baya. Amma bana jin dad’i in naji Ana zancen mutuwa ta dalilina.” Yaya ta dafa kafadar ta tace, “kar kiyi wannan tunanin ki d’auka komai ya canja kamar yadda yace, ke yanzu kina ganin Yusuf zai sake aikata abinda yayi ne a baya? Tsakani da Allah a ranki Kina Jin zai yi haka?.” Ta girgiza kai alamun A’a Yaya tace, “kin fahimta Ashe, akwai halin sa wanda zaki sake tararwa yana nan ke kin san su amma wannan manya-manyan halayen da yayi miki wanda daman ba nasa bane arowa yayi ya saka wallahi bazai yi ba. Ni tunda naga yanayin sa nake ji a raina ina ma ki koma din saboda yanzu yasan darajar ki da mahimmaci ki sai yafi rik’e ki akan baya. Ke har Al’Ameen din son da Yusuf yake miki a yanzu baya miki, a baya kece kike masa wannan son har nake miki fad’a a yanzu kuma shine. Ki tuna abubuwa nawa kika jure saboda wannan son? Abubuwa nawa kika daurewa saboda son, to shima haka zai daure ya jure saboda son da yake miki.”

Ameena ta sauke numfashi tace, “ina bukatar yin tunani a kan lamarin nan.”
“Istikhara zakiyi akan Allah ya zab’a miki wanda yafi alkhairi a tsakanin su.” Ameena ta girgiza kai tace, “To Yaya zanyi in sha Allah.” Yaya tayi murmushi tace, “burina ki samu rayuwa mai kyau Ameena, in kina ganin wajan Yusuf baza ki smau ba koma wajan Al’ameen din duk wanda kika d’auka a wajena daidai ne.” Ameena tayi murmushi ya goge idanun ta tace, “Allah zai zab’a mana Yaya.” Tace, “shikenan babu ke babu damuwa Tunda kika ce Allah, amin.” Ameena tayi murmushi ta shiga band’aki ta bar Yaya a tsaye a wajan.

      Kwanan su Rukayya biyu da dawowa Nigeria taje gida wajan su Umma ta kai musu tsaraba ta shiga har wajan Fiddausi ta bata tsarabar doguwar riga da ta siyo mata ai kuwa taji fdad’isosai ta dinga murna. Ameena tana ta cewa zata je bata samu taje ba sai ga Rukayya tazo da kanta.
Chapter 77 · 0% Book details