← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 93

Sashe 49

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kenan kina nufin Rukayya matar Ibrahim ce a yanzu?." Ameena tace, "eh mana Fiddausi." Fiddausi kamar an d'ora mata wani abun a kanta haka taji amma sai tayi shiru tana kallon k'asa kafin ta d'ago tana kallon su tare da kallon falon gidan tace, "kenan wai a gidan Ibrahim nake? A nan naci abinci nasha ruwa?."  Ameena tayi murmushi tace, "kamar ba gidan sa ba da ba ko? Gaskiyar Zakiyya da tace miki wancan daban wannan daban. Domin sanin wancan da kika yi kike kira talakan da bashi da komai wannan ya wuce ace masa Talaka."

Murmushi yaqe tayi ta kalli Rukayya da yake tsaye tace, "Allah ya sanya alkhairi, na taya ki murna." Mugun kishi Rukayya take ji a zuciyar ta amma bata so hakan yayi tasiri sai itama tayi murmushi tace, "na gode." Fiddausi tace, "ya kamata mu tafi." Ameena tace, "da wuri haka? Ko sallar la'asar ba'a yi ba ki bari ayi sallah rana tayi sanyi sai mu tafi." Waje ta samu ta zauna amma ta kasa sukuni gabad'aya sai ware ido take kana kallon ta kasan akwai abinda yake addabar ta a zuciyar ta.

Zakiyya tace, "ya naga kin canja? Kin manta ke kika bada wannan damar Fiddausi? Kin manta kince zaki zo gidan Kici abinci ku gaisa dashi?, to ga damar hakan ta samu meyasa yanzu kika canja kuma?." Kai ta sunkuyar bata ce komai b kafin ta d'ago tace, "babu komai kawai abin yazo min bazata ne." Amir ne ya dawo ya wuce ya ya shiga kitchen ya zuba abinci ya dawo ya zauna yana ci yace, "Ammi yau ma an bani kyau a makaranta, tsaya na d'auko" ya fad'a yana tashi ya shiga d'aki sai gashi ya dawo da ledar chocolate ya bata yace, "Uncle ne yace nafi kowa iya karatu shine ya bani." Tayi murmushi tace, "ka gode kaje Kaci abinci."
"Ammi dmaan Abba yace in na cigaba da kokari zai siya min keke ko?." Ta d'aga  kai alamun eh yayi tsalle ya koma yana cin abincin sa Fiddausi na kallon sa tana murmushi.
Abincin ya gama ci yace, "Amma ba'ayi wanka ba." Tace, "kaje ka kwanta ka huta anjima za'a yi." Ya amsa da to ya wuce ya shiga d'aki ya bar Fiddausi tana kallon sa.

Shiru babu wanda yake cewa komai sai kallon kallo kowa da abinda yake ransa a cikin su kafin Fiddausi ta katse shirun tace, "Ammi a bani aron Amir dan Allah mu tafi tare zuwa gida, nayi kewar sa sosai wallahi ina so ya zauna a kusa Dani." Rukayya ta kalle ta tayi ajiyar zuciya tace, "to." Wayar tace tayi k'ara a kusa da Fiddausi ta juya ta d'auko mata ta mik'a mata, ganin sunan da yake yawo a kai ta dan rufe ido fa bud'e kafin ta d'auka. abinda taji ya saka gaban ta ya fad'i sosai ta kashe wayar ta tashi ta fita bata ce komai ba.

#Mai dak
#Book3
#Nana Haleema
#Paid
#500

Book3
027

      Bud'e k'ofar tayi ta ganshi a tsaye yabi fuskar ta da kallo ta bashi hanya ya wuce ya bud'e gate din ya fita ya koma motar ya shigo da ita ya sake fita ya kulle gate d'in tana tsaye bata motsa ba ya kalle ta yace, "Lafiya kike?." Kai ta girgiza kawai ya d'an zubawa fuskar ta ido na wani lokaci kafin ya janye idon ya kalli k'ofar falon gadin takalman mata sai ya shiga setroom din sa da k'ofar take a compound din gidan daga can gefe ta bi bayan sa ya zauna  itama haka.

"Meye yake damun ki haka? Kukan me kika yi?." Numfashi ta sauke tayi shiru bata amsa ba yace, "Ina miki magana, me ya faru na ganki a haka?." Ta kalle shi sai idanun ta suka sake cika da hawaye suka sakko kan kuncin ta ya kulle ido ya bud'e yace, "magana nake miki ki fad'a min." Hannu ta saka zata goge idanun ta ya riga ta gogewa yana kallon ta itama haka tace, "Su Ameena ne suka zo."

Da mamaki yace, "yau  kuma zuwan Ameena ne ya saka ki kuka?." Ta girgiza kai alamun A'a yace, "ki fad'a min magana kin barni cikin tunani, me yake damun ki?." Bud'e k'ofar akayi tare da kullewa ganin Amir ya shigo ya saka shi cewa, "A'a Amir yau ko uniform ba'a cire ba?." Ya k'araso kusa da shi yace, "Abba Mama tazo." Ibrahim yace, "wacce Mama?."
"Mama da ta tafi unguwa bata je dani ba." Ya kalli Rukayya yace, "wa yake nufi?." Rukayya ta kalle shi tace, "Maman sa yake nufi."

Ibrahim yace, "yana da wata Mama ne bayan ke daman?. Look Rukayya ki fad'a min abinda yake faruwa mana bana son wanna nuk'u-nuk'un naki. Wacece Mama? Zuwan tane ya saka ki kuka?." Rukayya tace, "Mahaifiyar sa nake nufi." Zuba mata ido yayi na wani lokaci kafin yace, "shine ya saka ki kuka har haka? Shine ya baki damuwar da kuka kasa tambayata yau ya akayi na dawo da wuri?." Ta rausayar da kai tace, "Bana tare da nutsuwa ne shiyasa, amma..." ya katse ta yace, "Amma Me?." Sai ya kalli Amir da yake leken taga yace, "Amir koma d'aki yanzu zata zo."

Fita yayi yaja k'ofar ya kulle shi kuka ya kalle ta kamar zak magana sai ya fasa ya zuba mata ido kafin  ya sake cewa, "ko abinci baki bani ba." Ta mik'e tace, "yi hak'uri ina zuwa" ta fad'a tana fita zuwa falon da suke. Tana shiga falon da Fiddausi suka had'a ido da alama kallon ta inda zata b'ullo take yi sai tayi mata murmushi itama Fiddausin tayi Rukayya tace, "na barku ku kad'ai ko? Mai gidan ne ya dawo zan bashi abinci ina zuwa" ta fad'a tana  shiga kitchen.

Ba jimawa ta fito da abincin ta wuce su ta shiga ta ajjiye masa ta zauna a gefen sa tana kallon sa, zuba masa tayi a plate maimakon ya d'auka sai ya kalle ta kamar zai magana sai ya fasa ya d'auki abincin sa yaci tana zaune sai da ya kusa gama cinyewa ya kalle ya yace, "Wai wannan canjin ne meye?."
"Abinda naji ne ya saka ni a damuwa."
"Ni kuma sai ya shafe ni?."
"Kayi hak'uri bai shafe ka ba."
"Shiyasa gaki nan kamar yadda kike Kullum." Tayi shiru tana kallon sa ya tashi ya bud'e k'ofar da take kusa dashi sai gashi a d'akin sa ba tare da ya koma wancan falon ba.

Fita tayi ta koma wajan su tana shiga Ameena tace, "Tunda mijin ki ya dawo zamu wuce mu." Rukayya tace, "Da wuri haka?." Zakiyya tace, "gwara muje sai kifi samun lokacin kula dashi." Tayi murmushi ta kalli Fiddausi da ta zubawa waje d'aya ido tace, "na kira  miki Amir?." Fiddausi ta kalle ta tace, "Da naji dadi." Sai fiddausi ta bata tausayi ta shiga d'akin Amir din suka fito tare ya kalli Fiddausi yace, "Bye Mama" yana fad'a ya shiga d'aki ya barta a wajan baki bud'e tana masa dariya amma a cikin zuciyar ta zafi take ji sosai.
Murmushin yaqe tayi tace, "babu komai." Zakiyya tace, "muje ko?." Tare duk suka mik'e suka fito zuwa harabar gidan Fiddausi taga mota mai kyau a ajjiye ta bita da kallo amma bata ce komai ba. Har bakin mota Rukayya ta raka su da alqawarin zata je gidan su Fiddausi.

       Lokacin da ta koma wajan sa ta shiga kai tsaye ta same shi a zaune yana ta binciken takarda ta zauna kusa dashi tace, "yau ka dawo da wuri." Kallon ta yayi sai ya share bai magana ba ya cigaba da abinda yake yi ita kuma ta dafe goshiin ta gabad'aya labarin Fiddausi ya hana zuciyar ta sukuni ko kusa. Banza yayi mata shima bai kula ta ba sai waya da yake amsawa yana ajjiyewa tace, "kaina ciwo yake min."
"Dole kanki yayi ciwo ai, kin sha kuka."
"Bara nayi sallah." Baice komai ba ta tashi ta shiga band'aki yayi alwala ta fito ta samu baya nan tasan ya fita sallah shima ta tayar da sallah ta zauna akan sallayar bayan ta idar kawai tunanin Fiddausi ya sake zuwa ranta sai kuka.

Tana cikin kukan ya sake dawowa ya zauna ya hard'e hannayen sa waje d'aya yana kallon ta yace, "bazan ce me aka fad'a miki ya saka ki kuka ba amma ko meye ki kawar dashi a yanzu ki fuskance ni dan ni ne a gaban kik damuwar ta tafi, na dawo gida baki tambaye ni dalilin dawowa ta da wuri ba, nazo da labari mai dadi amma ban samu fuskar fad'a miki ba bayan kin san kece abokiyar shawarata sai na fad'a miki zanji dad'i a raina. Tun daga can na k'unso labarin ina so na fad'a miki amma da nazo sai naga akasin yadda na fita na barki. Akan wani abu da bai shafe ni ba zaki canja min haka? Akan me?." Ta goge idanun ta ta kalle shi tace, "Wallahi in na tuna ne bama sanin na fara kuka Khalil,  zuciyata zafi take ban san ana samun hakan a gaske b sai d'azu."
"Ban tambaye ki ba ai, bance a fad'a min ba, haka bana so naji wani abun. Ban san abinda ya faru ba dan haka baza'a canja min ba, ni nayi laifin?." Ta girgiza kai alamun A'a yace, "to meyasa zai shafe ni?."

Ta goge ido sai tace, "kayi hak'uri."
"Ba laifi kika yi ba, amma ki sani zan dakatar da duk abinda zai saka ki damuwa sake zama dake har yayi magana dake, in ma su Ameena din ne suke saka ki a wannan yanayin zan dakatar dasu dan bazai yu a zo har gidan ki saka ki damuwa a koma a barki a cikin ta ba. Ciki ne dake kwanciyar hankali ce ta kamace ki ba tashin sa ba." Tasowa tayi daga inda yake ya dawo kusa dashi ta shiga jikin sa ta rike shi gam shima ya rike ta yayi shiru bai ce komai ba.
Chapter 49 · 0% Book details