← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 93

Sashe 80

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adam yace, “Amin ya hayyu ya qayyum. Kayı masa bayani in ya dawo hankalin sa naga yanzu ba komai yake ganewa ba. zaku iya tafiya daman maganar ce su Alhajin sa duk sun san da maganar to ayi abinda za’ayi bana son b’ata lokaci. Sannan Ameena bata son yayi magana da ita daga nan har a mayar da auren, to ko waya kar ya kira ta ya kyale ta.”  Usman ya amsa ya kalli Yusuf da yayi shiru ya k’asa cewa komai yace, “tashi mu je Yusuf.” Yusuf  ya kalle shi yace, “naje ina?.”
“Muje gida wajan Ammah, kazo muje zaka ji komai daga baya.”
“Ban yi godiya ba, na rasa me zance da zan nuna na gode.”

“Rik’e Ameena shine zai saka su san ka gode, ka tashi muje zamuyi magana daga baya.”  Har zasu fita Yaya Adam yace, “yauwa sai batun kayan da za’a zuba na gidan ko? Ni Nama manta wallahi” ya fad’a yana kallon Al’Ameen. Al’ameen yace, “nima haka, babu damuwa ya bamu gidan zamu samu masu had’a gida in 24hrs zasu had’a gidan ya zama neat.” Usman ya kalle su yace, “na ari bakin sa naci albasa, basai anyi komai ba Yaya mu da aka bamu Ameena bama buk’atar ku siyi komai duk zamuyi da kan mu.” Al’ameen yace, “saboda me? A al’adance hakkin mu ne.” Usman yace, “mun sani, Mun d’auke muku shi ne.” Adam yace, “shikenan Allah ya nuna mana.” Ya amsa da amin a haka dai suka fita amma Yusuf ganin abin yake kamar a mafarki.

Yana fita Al’ameen ya sauke Ajiyar zuciya yace, “Yanzu muka suke hakkin da yake ka mu matsayin mu na yayyen Ameena. Har zuciyata na amince dashi a yanzu wallahi, bana jin komai nasan zai rik’e ta rik’on da bai yi mata a baya ba.” Adam yace, “kasan tun a baya ni ba wani son sa nake ba kawai dan tana so ne ya saka na amince mata. Amma a yanzu sai nake gani kamar ba wancan Yusuf din bane wani daban. Zuciyata ta amince dashi Allah yasa kar ya watsa mana k’asa a idanu.” Al’Ameen ya murmusa yace, “Babu Ameena a kaddarar Al’Ameen, yanzu sai na mayar da hankali nemo matar aure.”

“Na d’auka ka cire aure ai daga rayuwar ka.” Ya harare shi yace, “da yake ba mutum bane ba ni ko?.”
“Waye ya sani, abu a duhu”. Yayi dariya yace, “ka samu baki magana yanzu ai da yake ba batun Ameena, amma da zan baka amsa a gaba.” Shima yayi dariya suka cigaba da tattaunawa akan batun Ameena din da yadda suke so abin ya kasance saboda tafiyar da zasu yi.

         Yusuf a haka suka shiga gidan Ammah suna shiga ya tarar da Abbah da Ammah da kuma Mubakar a zaune yana zuwa ya zube a gaban iyayen nasa da suke zaune akan kujera guda d’aya yace, “wani abu ne ya faru nake so a tabbatar min gaske ko ko mafarki nake, Usman yace min ba mafarki nake ba amma zuciyata ta gaza fahimtar hakan. Da gaske yanzu Ammah ina zaune a gaban ku ba mafarki bane?.” Abbah yayi murmushi yace, “ba mafarki kake ba, Adam ya amince zai sake baka auren Ameena.”

Numfashi ya sauke mai k’arfi yace, “Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!.” Abinda yace kenan ya sunkuyar da kansa  k’asa yana ji zuciyar sa na harbawa sosai da sosai ya kalli Abbah da yake kallon sa yace, “Jikin ka yayi sanyi ko? Ni kaina ban so hakan ta kasance ba gwara ma na fad’a maka gaskiya. Ban so ka sake mallakar ba Ameena ba sboda baka san mahimmacin ta ba, ba kuma ka cancanci sake rik’e ta ba a rayuwar ka.”
“Na sani Abbah, wallahi na sani na tabbatar da rashin ta tamkar rashin rayuwata ne wallahi.” 

Ammah tace, “Ameena ta amince zata dawo gare ka saboda ni da kuma Zaytun ba dan wai tana sonka ba. Dan haka in ka sake wulakanta Ameena Yusuf ni ka wulakanta, in ka sake cin zarafin Ameena ni Hafsa ni ka yiwa, in ka saka Ameena kukan bak’in ciki zuciyar Hafsa ka  bak’antawa, in ka yaudare ta Hafsa ka yaudara. Yusuf in ka sake d’aga hannu ka daki Ameena Allah ya isa ban yafe maka, in ka yiwa Ameena abinda zata cutu har ta samu ciwo ban yafe maka ba, ba kuma zan yafe ba” Da sauri ya girgiza kai ya rik’e hannun Ammah yace, “Ko baki ce haka ba Yusuf yayi hankali yasan abinda yake yi a yanzu bazai sake aikata abinda ya wuce ba wallahi. Ina son sake zama da Ameena bazan sake yin abinda zai raba mu ba ki amince dani. A wannan Karon zan baki mamaki zaki tabbatar ba wancan Yusuf din bane, wancan Yusuf din daban wannan ma daman Ammaha, ki yarda Dani Allah yana ganin zuciyata.”

Ya kalli Abbah yace, “Abbah kana ji Ameena zata dawo wajena, Abbah zan sake samun Ameena.” Sai hawaye suka cigaba da zuba na farin ciki Abbah ya kalle shi yace, “sai ka rik’e ta fiye da rik’on da kayi mata a baya, in ka sake wulakanta Ameena kaima Allah sai ya wulakanta ka.” Yusuf ya girgiza kai yace, “har abada bazan sake ba, wallahi bazan kuma ba komai ya k’are ya kuma zo k’arshe.”

Mubakar yayi murmushi yana kallon sa yace, “sai hankalin ka ya kwanta ya dawo jikin ka yanzu kodan Lafiyar ka. Sai kuma ka nutsu dai kar ka sake hango wata figaggiyar kace zaka aure ta, daga nan sai ka cigaba da wulakanta Ameena a kanta. Ita kuma daga k’arshe ta kashe ka.” Ya kalli Mubakar yayi murmushi kawai  gabad’ayan su baza su fahimci nadamar da yayi bane shiyasa suke fad’ar duk abinda yazo bakin su san gani suke bai yi nadamar ba. Da Gaskiyar su amma zai tabbatar musu da an samu chanji.

          Ranar Yusuf baiyi baccin ba kwana yayi farin ciki yana sallah yana gode Allah yana kuka, a haka ya kwana bacci sai b’arawo shima mai cike da mafarkan Ameena. Haka ya tashi da safe da wannan farin cikin duk da har lokacin ba Lafiya ce dashi ba amma haka yake k’arafafa jikin sa dan tabbatar da farin ciki a zuciyar sa. A ranar Yusuf masu aikin gidan su ya saka akayi abinci mai yawa aka tara almajirai aka dinga rabawa ana kuma bada sadakar kudi, ya d’auki Usman suka tafi emergency na asibitin murtala suka dinga rabon kud’i duk wani mara Lafiya a wannan lokacin Yusuf ya d’auki nauyin sa har yar jinya sai da ya bata kudin cin abinci a wajan nan. 

Ya samu lada a ranar matuk’a hakan da  yayi ya nuna godiyar sa ga Allah, yadda ya saka farin ciki a zuciyar wanda ya taimakawa babbar godiya ce da yayi ga wanda ya halicce shi, kai da ka ganshi kasan yana cikin walwala bakin nan a bud’e ya kasa rufe shi shi. 

         A b’angaren Ameena baza ka fassara yanayin ta ba komai tana yin sa yadda ta saba bata canja ba ita ba farin ciki ba ita ba akasin sa ba. da safiyar tana shan tea Yaya Adam ya fito ya same ta Anty Aysha tana bayan sa yace, “Ameena sai ina na ganki da mayafi a gefe?.” Ta kalle shi tace, “makaranta zanje.”
“Kina amarya ina ke ina zuwa wata makaranta?” Anty Aysha ya fad’a tana kallon ta. Ameena tayi murmushi kawai Anty tace, “ai ajjiye mayafin nan zakiyi, mu kira mai lalle tazo tayi miki kunshi aure fa zakiyi.” 

Ameena tace, “A’a dan Allah a barshi Anty, bana son son yin komai a barni a haka.” Anty tace, “kamar ba amarya ba?.” Ameena tayi murmushi tace, “nafi son hakan ne” ta fad’a tana tashi ta d’auki mayafin tace, “sai na dawo.” Bayan ta fita ya kalli Aysha yace, “Kamar bata farin ciki da hakan.”
“To bama ce tana yi  ko bata yi ba, tsoron abinda ya faru a baya ne a zuciyar ta amma ni na tabbatar maka tana son komawa wajan sa.” Yaya adam yace, “Allah yasa.”

     Ameena na fita sai ta fasa zuwa makarantar kawai tayi gidan Rukayya ta same ta ita kad’ai Amir baya nan ta baje akan kujera tana sauke numfashi. Ameena tace, “na gaji.” Rukayya tace, “aikin me kika yi?.”
“Noma.” Rukayya tayi dariya tace, “Yanzu kenan gobe ke amaryar Yusuf ce?.” Ameena ta  mik’e zaune tace, “shine abinda yake damun zuciyata Rukayya, Anya banyi ganganci ba kuwa? Na baro wahala na sake komawa wahala?.”

Rukayya tace, “meyasa kike haka ne wai? Ki yi fatan alkhairi ga rayuwar ki mana me ya na wannan zancen dan Allah?. Kin yarda yayi nadama meye to na kasa amincewa dashi Ameena?.”
“Wallahi ban sani ba Ruky, kawai hango abinda ya wuce nake yi wanda ke baki san su ba.”
“Babu abinda za’a sake maimaitawa na fad’a miki Ameena, dan Allah ki daina wannan maganar kawai mu cigaba da addu’a akwai rabo mai k’arfi a tsanani tunda kika ga Allah ya sake had’a ku a karo na biyu. Kuma addu’a kike ba dare babu rana, su Yaya Adam duk suna yi miki Tunda kika ga hakan to Allah ya rubuta baki da mijin duniya sai shi.”

Ameena ya sauke numfashi tace, “haka ne Rukayya. Ni kaina na tabbatar da hakan dan addu’ar da nake yi a kai na tabbata Allah ne ya amsa.” Rukayya tace, “to kin gani, babu komai sai alkhairi wallahi.” Tayi murmushi Rukayya tace, “kunyi magana dashi ne?.” Ta girgiza kai tace, “nace kar ya neme ni har sai bayan an mayar da auren, in ba haka ba Muna sake had’uwa zan iya canja ra’ayi wallahi.” Rukayya tayi dariya tace, “mai aljanun y’an gayu. Bara na kira Fidy da Kiyya su sha labari” ta fad’a tana d’aukar waya ta kira wayar Maman su Fiddausi aka b’ata Fidy ta had’a compresse call suna yi tana basu labari ana ta murna da farin ciki.
Chapter 80 · 0% Book details