← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 93

Sashe 33

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rukayya tace, “tamkar y’ar uwa take a wajena kamar Zuhra da Sajida haka nake jin ta a jikina wallahi. Mu saba sosai rashin ta zai saka naji babu dad’i.” Ya tab’e baki yace, “To yayi kyau.” Kallon da tayi taga ba ita yake kallon ba alamun baya son maganar sai ta canja maganar tace, “ya kuka yi da Alhaji akan maganar gidan?.”
“Maganar nazo muyi dake sai hankalina ya bar wajan. Alhaji ya bada goyan baya sosai bama shi kadan ba har su Yaya Sulaiman, suma kamar yadda kika ce haka suka ce.” Tayi dariya tace, “kayi magana dasu?.”
“Sai zuwa gobe zan musu magana sai mu fara shirya kayan mu neman gida indai da kud’i ba abu bane mai wahala.” Rukayya tace, “to Allah ya saka musu albarka gabadaya.” Ya kalle ta yace, “Amin. Makarantar su Amir da naje d’azu sun sanar dani Amir yana k’ok’ari sosai musamman a b’angaren addini, alkur’ani da an yi musu da ya rik’e hakan ya saka suka kira ni akan a cigaba da k’arfafa masa guiwa ana cigaba da bibiyar karatun nasa dan hakan shine ya saka shi yake iyawa da sauri. Principal din yace min da aka tambaye shi an ina ake koya masa yace Ammin sace.”

Rukayya murmushi take bata ce komai ba ya rik’e hannun ta yace, “ni dmaan nasan zaman ki da Amir alkhairi ne a cikin tasa rayuwar, domin baza ki barshi yayi kuka ba sannan baza ki yi masa tarbiyya banza ba. Amir da anyi kira yake tashi yayi sallah alwala in yana yi sai ka tsaya ka kalla saboda yafi wani babban iyawa. Haka akayi a masallacin juma’a da muka je da yana alwala kallon sa mutane suke yi ana dan Allah wannan d’an waye alwala babu kuskure kamar ba yaro ba, farin ciki hana ni magana yayi da alfahari nake sanar da mutane d’ana ne.” Murmushi take yi kawai hannun ta na cikin nasa yace, “mace ta gari itace take samar da y’ay’a na gari, Allah yayi miki albarka Rukayya shigowa ki rayuwar Ibrahim da ta d’ansa tanka haske ne a cikin duhun daji, Allah ya cigaba da baki ikon hak’uri dani.”

Tayi dariya ta kalle shi tace, “har wani abu ne dakai da za ayi hak’uri?.” Yayi dariyar shima yace, “ni nasan akwai ai ko ya y baza’a rasa ta inda nake yin wani abu bakya so ba, kinga ni ina hak’uri dake musamman a b’angaren wannan kunyar taki da ta kasa tafiya har yanzu.” Sai kuwa ta sake kulle fuskar ta tana dariya shima haka tace, “kin gani ko? To hak’uri nake dake akan wannan babu yadda zanyi.” Murmushi take yi ta bud’e fuska tace, “dukkan mu alkhairi ne a rayuwar junan mu, kai alkhairi ne a rayuwata samun ka yafi samun diamond.” Ya wara idanu yace, “kin San diamond kuwa?.”

Tayi dariya tace, “darajar sa bata kai da mijina ba.” Ya kwanta a jikin ta yana kallon ta yace, “in kika ce mijin nan naki ko sai naji kamar an d’auke ni sama ana zagawa dani.” Tayi dariya tace, “kana bani nishad’i.”
“Allah yasa na dinga baki nishadi har abada.”
“Allah ya amsa bakin ka.” Yace amin yana murmushi ko wanne su farın cikin kasancewa da dan uwan sa yake yi domin rayuwar su ta canja gabad’aya kamar ba Sune suka sha wahala a baya ba.

Yusuf yana zaune yana danna waya Asiya ta shigo ta bayan sa bai san ta shigo ba dan a lokacin transfer yake yi ta tsaya a bayan sa tana kallo har taga pin din da ya danna ya gama tura kud’in sai tayi dariya cikin farin ciki a sannan ta k’araso ta zauna tace, “Yauwa batun kudin siyayyar kayan jaririn cikina.” Kallon ta yake yi jin babu sallama babu sannu balle kuma gaisuwa yace, “ke baki iya sallama bane ba wai?.”
“Ban iya ba, abinda na saka a gaba shi kawai nake yi.” Kai ya girgiza yana jin d’acı a zuciyar sa da k’una da kuma tsanar ta mai muni tace, “nayi lissafi miliyan biyu zaka bani dan ko keken da za’a siya masa na kwanciya naira dubu dari biyu ne, akwai gado da sauran kayan sawa.”

Ya kalle ta yace, “ke wai baki da magana sai za’a zancen kudi?.”
“Su na fito nema, dole ka bani kuma koda baka so.”
“Sai ki kwace tunda naki ne.” Tayi dariya kad’an tana kallon sa kafin ta kalli ledar da take gefe ta d’auko tana dubawa ganin atamfa guda biyu da kuma lace kala biyu yace, “kayan bikin humaira ne Ammah tace a kawo miki.” Ta fito da katina daga cikin kayan tana kalla ganin bikin ma cikin satin ne tace, “lallai ma, jibi juma’a za’ayi kamu amma ba’a kawo min ankon ba sai yanzu da yake an daina min hankali, To baza’a saka ba” tayi tsaki tana cillar da kayan gefe.

“Kee!.” Ya furta yana kallon ta zuciyar sa na tafasa sosai fushin sa ya bayyana a kan fuskar sa ta kalle shi tace, “na fad’a, sai me?.” Bata yi tsammani ba taji ya mare ta daman kiris yake jira ya mik’e tsaye tana kallon sa itama ta mik’e kawai ta chakumi wuyan rigar sa tace, “na rantse da Allah kar ka kuma dukana ina fad’a maka ka daina wannan kuskuren amma ka k’i ka daina.” Ya cire hannun sa daga jikin sa yace, “ke wacece da kika mayar da Ammah tamkar abokiyar wasan ki? Asiya in baki shiga hankalin ba zaki yi dana sani wallahi.”
“Bazan shiga hankalin nawa ba, an fad’a kuma baza’a dinka kayan ba sai kayi abinda zakayi. Naga dama ko bikin ma bazan je ba akwai abinda za’a yi min ne?.”
“Gwara ma kar kije ai zuwan ki bashi da amfani, da ki je ki yi sata ai gwara ki zauna a gida ki saci kanki.”

“Naji ni sata nake kai kuma giya kake sha, d’an giya kawai mai sab’awa Allah wanda yake aikata abinda ya haramta. Gwara ni wanda ya yiwa abin sa ajiyar banza nake d’auka na gyarawa zama kai kuwa fa? Dan giyan banza da…..” kalmar da ya tsana kenan yaji tana fad’a masa a duk lokacin da hakan ta faru yana saurin harzuk’a zuciyar sa ta tafasa bai san lokacin da ya sake marin ta ba ai kuwa kafin ya d’auke hannu sa ta kai masa mari itama ya rik’e hannun nata ya tsaya yana kallon ta tace, “Baka isa ba wallahi, kai baza ka sake dukana na kyale ka ba dan ba jaka bace ba ni. An fad’a kuma d’an giya kayi abinda zakayi” tana fad’ar hakan ta kwace hannun ta bar masa wajan ya bita da kallo har lokacin mamaki yake da ya bari sake Marin sa zatayi kenan?.

Wani irin kuzari ne yazo masa a lokacin wanda ya jima bai ji irin sa ba yabi bayan ta da sauri ya samu tana k’ok’arin shiga d’aki ya zari wayar fanka ya k’arasa inda take ya manta ma ciki ne da ita ya fara dukan ta ta ko ina tana ihuu tana cewa, “Allah ya iss, Shege mugu dan giya. Wallahi sai kayi dana sani abinda kayi min sai na d’auki mataki a kanka.” Hankalin sa ya gushe dukan ta kawai yake yi bai kula da jinin da ya fara zuba daga jikin ta ba burin sa yayi mata dukan da zata kasa tashi ko nan gaba zata daina yi masa abinda take yi.
Sai da ya gaji dan kansa ya cillar ya bar wajan ya fita daga gidan gabad’aya yana jin zuciyar sa na tafasa sosai domin fushin zuciyar da tsanar ta da take ciki ne yayi tasiri a gangar jikin sa.

Momi ce ta hau saman a lokacin tazo gidan Asiyan ta kira ta akan tazo ta kwana gobe ta karata asibiti ganin halin da yake ciki gata a kwance kamar bata numfashi hankali ya tashi tayi waya gida hankali tashe ta fad’a. Hankalin ta ya tashi gashi bazata iya sauka da Asiya ba ga masu aikin duk sun gudu dole ta jira har su Umma suka zo aka d’auki Asiya aka fita da ita hankalin su ya tashi sosai.

Karb’ar gaggawa aka yiwa Asiya a asibiti aka shiga bata taimako gaggawa dan a ceto abinda yake cikin ta. Da yake private ne likitan yana fitowa ya kalli su Umma yace, “dukan ta akayi?.” Umma tace, “bamu sani ba tana gidan ta muka je muka same ta a haka.”
“Duka ne dan jikin ta akwai shatin duka sosai, dukan da aka yi mata ya jawo cikin ta da ya kai matakin zama mutum ya mutu, in mijin ta yana kusa ya saka hannu a nan za’a yi mata aikin gaggawa domin cire shi,”

Umma ta dafe k’irji tace, “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, d’an ya mutu?.” Likita yace, “ya mutu, ayi a saka hannu dan za’a yi mata aiki a cire.” Yaya Maimuna tace, “Babu wani babba a kusa damu yanzu, wannan Maman ta tace ni kuma yayar ta zan iya saka hannun?.” Likita ya yiwa nurse nuni da ta bata takardar ta saka hannu suka koma dan cire yaron cikin Asiya.

Momi tace, “lallai Yusuf ya d’auko ruwan dafa kansa, sai yayi dana sanin abinda ya aikata mana.” Umma ta kasa cewa komai sai kallo kawai da take yi tana kwafa dan Allah kad’ai yasan abinda zata yiwa Yusuf a wannan lokacin. Suna nan har washe gari an yiwa Asiya aiki an cire yaron a lokacin Umma bata nan tana barin asibitin gida taje tayi wanka ta shirya ta sake fita kai tsaye wajan ya’n sanda taje ta sanar dasu duk abinda yake faruwa aka had’o ta da y’an sanda guda biyu suka tafi gidan Yusuf kai tsaye. Koda suke je mai gadi yace ya fita bata yi k’asa a guiwa ba tace su wuce store d’in sa ta tabbatar yana can. kai tsaye can suka wuce dan kamo shi dan tayi alqawarin sai yasan y’ar ta ya yiwa duka har d’ancikin ta ya mutu, daga kan Asiya bazai sake dukan wata mace ba koda ance yayi ta tabbatar bazai yi dan zata koya masa hankalin da nan gaba shine zai hana wani aikata irin abinda ya aikata.

#Mai daki
#Book3
#paid
#Nana Haleema
#500

Book3
020
Chapter 33 · 0% Book details