← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 93

Sashe 41

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cillar da wayar Alhaji yayi Allah ya saka a akan carpet ne babu abinda tayi ya zauna sai kuma ya mik’e tsaye kamar mahaukaci ya kalle su yace, “dole nayi muku hukuncin abinda kuka aikata min, sai Kun….” K’arar wayar sa ya saka bai gama fad’a ba ganin sunan malamain sa da sauri ya d’auka ya saka a kunne daga can b’angaren yace, “me yake faruwa nake ganin bak’i yana kokarin mamaye lamarin ka?.”

Alhaji Bello yace, “Na shiga uku, malam sun gudu matan guda uku duk sun gudu a lokaci d’aya.”
Malam yace, “sun gudu? Garin ya ka bari suka gudu a wannan yanayin da ake ciki? Ka manta ba’a so sirrin nan ya fita matuk’ar baka saki matar ba?.”
“Nan sani ba, masu kula dasu ne suka ci amana ta suka fita dasu ba tare da na bada izini ba. Malam ya zanyi yanzu?.”
“Ayi kokarin nemo su kafin su kai ga fad’awa wani ahinda yake faruwa, in hakan ta faru zan iya cewa shikenan lamarin ka ya lalace, kamar yadda ka sani lokaci d’aya komai yake b’aci haka zai faru a kanka.”

Hankalin Alhaji Bello ya kuma tashi rud’ewar sa tafi ta baya ya kalli inda suke a zaune sai yaga basa nan alamun sun gudu hankalin da ya tashi ya cillar da wayar, tv da take kusa dashi ya jawo ya da k’arfi ta fad’i k’asa ya saka k’afa yana taka ta cikin fitar hayyaci saboda rud’anin da yake ciki a wannan lokacin. “Na shiga uku ya zanyi?” Ya fad’a a bayyane cikin rashin sanin abinda zaiyi d’in, da sauri ya d’auki key ya fita dan ya tuna wani abu.

Su Fiddausi tunda suka farfad’o suke kukan a kai su gıda hankalina tashe sun kasa ko magana kawai a kai su gıda, ganin hakan ya saka aka had’a su da d’an sanda guda biyu aka shiga dasu mota za’a sauke Naja’atu a kaduna, Fiddausi a kano Aliya Katsina. Hankalin su bai kwanta ba sai suka ga an fita daga garin Abuja a nan ko wacce ta fashe da kukan farin ciki.

A safiyar Yusuf yana tsaye a kan titi a cikin mota ya fita yaje ya siyo fura da ya tashi da son sha yana tsaye ana check point. Tsaki yayi yace, “da safiyar nan ace za’a yi wani checking kamar b’arayi” ya fad’a yana kokarin juya motar ya koma. Ganin zai koma sai d’an sanda d’aya ya sha gaban sa suka kalli Yusuf yace, “ina zaka koma?.”

“Zan canja hanya zanyi ne ne gaji da tsayawa.” Ya bashi amsa yana kallon sa ba tare da tsoro ba. D’an sandan ya kalli Yusuf sosai yace, “oga ban yadda da wannan ba azo a duba motar.” Yusuf ya tab’e baki suka zo suna duba motar Yusuf ya bud’e musu boot yana jiran su gama abinda suke yi ya kama gaban sa.

Wani ihuu yaji sunyi da sauri ya kalle su a lokacin suna duba bayan motar nan da nan aka kewaye shi da bindiga babban cikin su yace, “fito!.” Yusuf yace, “me nayi?.”
“Ka fito akace malam.” Yusuf ya fito ya tsaya yana kallon wanda ledar take hannun sa yace, “safarar cocaine da safiyar Allah, ku saka shi a mota a tafi office.”
“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Cocaine kuma? Ni din aka ganta a mota ta?.” Tsaki yayi ya daki kewar Yusuf aka saka shi a motar da aka rubuta NDLEA aka tafi dashi.

Sai Yamma su Fiddausi suka shiga garin Kano bayan an sauke Naja’atu lokacin da ta ganta a kano farin ciki ya mamaye zuciyar ta sai kuka kawai take yi saboda farin cikin da ya cika mata zuciyar ta. Har k’ofar gidan su aka tsaya Fiddausi ta fito ita da d’an sandan guda d’aya ta shiga cikin gidan shi kuma ya tsaya daga waje ba tare da ya shiga ba.

Had’a ido sukayi da Mama tana shiga amma Mama bata gane ta ba sai ta sake kallon ta tace, “Baiwar Allah daga ina haka?.” Sai kawai ta zube a wajan ta a kuka muryar ta ko fita bata yi tace, “Mama Fidd…au…si ce” ta fad’a a rarrabe tare da zubewa a wajan a sume. Mama tayi ihuu tayo kanta tace, “Fiddausi” ta fara girgiza ta amma bata numfashi Mama tace, “Alhaji! Alhaji! Alhaji!! Ga Fiddausi ta dawo kazo a kaita asibiti ta suma.”

Abba da yake waje suna magana da d’an sandan jin ihun Mama ya saka ya shigo ciki da gaggawa aka d’auki Fiddausi aka wuce asibiti da ita dan dole taga likita. Emergency na asibitin murtala aka kai ta akayi sa’a akwai gado aka kwantar da Fiddausi aka fara bata taimako da take da buk’ata.

Cikin mintina kad’an y’an uwa an cika kowa yazo Mama yake tambaya tace ita bata sani ba a tambayi Abba. Har dare suna wajan Fiddausi bata farfad’o ba har wannan lokacin gashi ba’a barin shiga gwara Mama ta shiga ta gano ta amma bayan ita babu Wanda yake shiga. Sai lokacin da zasu koma Abba ya kalli Mama da y’an uwan Fiddsuin yace, “waye zai zauna a wajan ta? Mai jinya akwai zasu bari ya shiga.”

Mama tace, “ni zan zauna, an kawo min abin kwanciya ma.” Abbah yace, “shikenan ko mai ake ciki ki yi min waya komai dare.” Mama ta amsa ya d’auki kud’i ya bata yace, “koda za’a nemi wani abun sai ki yiamfani dasu.” Mama tace, “to sai da safe.” Tafiya sukayi ita kuma Mama ta shiga ciki dan komawa inda Fiddausin take.

Har safiya babu wanda yaji labarin ba’a ga Yusuf ba Asiya bata fad’a tace bai kwana a gida ba, waya ake yi tana shiga amma ba’a d’auka. Abbah da yake masa waya yana zaune yace, “Yusuf yana da shiririta wallahi, tun daren jiya mukayi zai kawo min sak’o har yanzu shiru gashi amfani zanyi dashi yanzun nan.”

Ammah tace, “ka tura Mubakar gidan ya gano maka in yana nan.” Baice komai ba ya kira Mubakar a waya yace, “jeki gidan Yusuf kace masa ya baka Sak’ın ka kawo min amfani dashi zanyi, yasan jirgi na k’arfe sha biyu zai tashi amma bazai hanzarta ya kawo min ba.” K’aramin tsaki yayi ya kashe wayar ya ajjiye Ammah tace, “Kuma da aka fara yi masa addu’a wallahi na ga canji a tare dashi sosai. Kaga yanzu bashi da wajan zama sai gidan nan bai cika zama a can ba sai dai kwanciyar bacci da take Kai shi.”

Abbah ya kalle ta yace, “Nima na gani, Matsalar daga wajan sa take ai shiyasa. Baya ibada yadda ya kamata kuma matar sa itace Matsalar.”
“Da wannan, dama ya sake ta su rabu kowa ya huta.”
“Ya dawo da Ameena?” Ya tambaya yana kallon ta dan yaga yanayin ta. Ammah ta sauke numfashi ta girgiza kai tace, “Ameena ai tayi masa nisan da bazai same ta ba a yanzu.”

Abbah yace, “koma meye dai shi ya kawowa kansa, nan kika nuna bakya son auren sa da yarinyar nan ya dage sai anyi yanzu ga abinda yake faruwa nan. Ya d’auko mana k’ananun mutane marasa tarbiyya ya kawo mana zuri’ar mu, addu’a ta Kullum Allah yasa ma kar ta haihu dashi dan baragurbi zai zamar mana gashi bamu isa muce ba namu bane ba.” Wayar da Mubakar yake yi ya saka Amma batayi magana ba ya d’auka ya saka a speaker Mubakar yace, “Abbah Yusuf baya gidan nan.”
“Ka tambayi matar da Ina yaje.”
“Baba isihu ya tabbatar min da tunda ya fita jiya da safe bai sake dawowa ba har yanzu.” Abbah ya kalli Ammah ya ce, “to Ina yaje?.”
“Baba yace min ce masa yayi zai je ya siyo fura ya dawo har yanzu bai dawo ba.”

Abbah yace, “duk da haka ka shiga ciki ka tambayi matar s.” Mubakar ya amsa ya kashe wayar, Ammah tace, “to ina yaje?.” Abbah yace, “watakila ko yayi tafiya ne bamu sani ba.” Waya ce ta sake shigowa Abbah ya d’auka Mubakar ne sai yaga sabuwar number ya d’auka ya saka a speaker daga can b’angaren aka ce, “Muna magana da mahaifin Yusuf?.” Abba yace, “eh shine.”
“Muna kiran ka daga nan NDLEA akan d’an ka Yusuf yana hannun mu.”
“NDLEA!? Me Yusuf din yayi da yazo hannun ku?” Abbah ya fad’a a gigice yana tambayar sa.
Ya cewa Abbah, “National drugs law enforcement agency, kamar yadda Kaji ita nake nufi NDLEA. daga nan muke yi maka waya akan mun kama d’anka yana hannun mu tun jiya.”

“Innalillahi wa’inna ilahiri raji’un! Dan Allah yana wanne station din ku?.”
“Muna nan club road, kazo kafin mu tura case din zuwa kotu.” Abbah yace, “gani nan zuwa yanzu in sha Allah.”

Ammah tace, “Yusuf din aka kuma kamawa?.” Ya kalle ta yace, “wannan yafi wancan illa, an kama shi da miyagun kwayoyi tunda kika ji NDLEA ne a case din.” Bai sake cewa komai ba ya fita Ammah ta mik’e tsaye tace, “Allah ka kawowa Yusuf sauk’i a lamarin sa, nasan sakayya ce take bibiyar sa yake fad’awa wannan iftila’i kala-kala, ya Allah ka yafe masa ka sassauta masa wannan lamarin da yake faruwa dashi.” Kuka Ammah take yi sosai a lokacin Mubakar ya shigo ganin tana kuka hankalin sa ya tashi yace, “Ammah Lafiya? Me ya faru haka kike kuka?.”

“Yusuf aka kama Mubarak, wai a NDLEA, me Yusuf yayi suka kama shi?.” Mubarak ya wara idanu yace, “NDLEA Ammah? Yusuf din?.”
Ammah tace, “Nan fa Mubarak.” Ya d’aga k’afa zai tafi ta rik’e shi tace, “zo ka fad’a min me mutum yake yi a kai shi can.” Mubakar yace, “Ammah ki bari ina zuwa.”
“Sai ka fad’a min zaka bar wajan nan.”
“Ammah in aka kama mutum da k’waya ko kayan maye shine ake kai shi can, kuma wallahi basa sakin mutum gashi wahalar da mutane suke yi domin shine hukumar yak’i da kwayoyi” yana fad’a ya fita ta zauna tayi shiru kawai tare da tagumi.
Chapter 41 · 0% Book details