Sashe 47
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babu Wanda ya sake magana a cikin su sai ma tafiya da Taha yayi bai kuma maganar kudin ba duk suka fita aka barshi daga shi sai ita. Wani irin haushin ta da tsanar ta yake ji a zuciyar sa kalma d'aya yake so ya furta amma harshen sa ya sark'e ji yake ina ma a bashi umarnin furta wannan kalma da babu b'ata lokaci zai furta ta. Umarni kawai yake so a bashi ya furta ya tabbatar zai iya amma a yanzu harshen sa yayi nauyi matuk'a.
Zama tayi tace, "my love amfani akayi da kud'in fa abubuwan da babu a gida na siya shiyas, amma ba wai na d'aukar maka kudi bane ba." Ya d'ago ya kalle ta yace, "Ya akayi kika san pin din?."
"Gani nayi kana sakawa." Yayi murmushi yace, "lokaci kad'an Asiya, lokaci nake jira ina furta abinda nake son furtawa shikenan komai ya k'are Asiya." Ta turo baki tace, "me kake so kace?." Bai kuma magana ba daga wannan lokacin ta dinga kare kanta yayi mata banza haushin ta da tsanar ta zuciyar sa amma bashi da karfin guiwar aiwatar da abinda yake so tunda an samu canji da ko haushin nata baya ji, amma Umarni akwai yake jira a bashi ya furta wannan kalma a kanta.
A daren aka sallama su suka koma gida. Yana shiga b'angaren ta yaga wayar tasa a ajjiye y d'auka kawai baice komai ba ya fita zuwa b'angaren Ameena ya kulle kansa a ciki dan kar ma tazo ya dame shi.
Sai da ya zauna ya fara duba b'arnanr da tayi masa nan ya dinga ganin cire kudi kawai tayi wani ta turawa accounts d'inta wani na Maimuna har da na Babar su. A bayyane yace, "wanne irin dangi na kai kaina ni Yusuf?. Har account din babar su an saka babu abinda ya dame su kawai su kud'i suka sani. Ta wacce hanya ma na auri yarinyar nan ni Yusuf?."Ajjiye wayar yayi a gefe kawai ya dafe kansa da hannu biyu yana Jin abinda ya jima bai ji ba a zuciyar da yana motsawa, a hankali yaji hankalina dawo kwakwalwar sa zuciyar sa na bugawa da sunan Ameena lokaci d'aya kamar asiri. Wayar ya d'auka sai kuma ya ajjiye ya rasa abinda zaiyi kawai ya kwanta a kan kujerar ya kulle idanun sa da suka yi masa nauyi sosai.
#book3
#Nana Haleema
#Mai daki.
Book3
26
Kamar yadda suka tsara zuwa wajan Ameena haka akayi Zakiyya tazo suka tafi duk da har lokacin ba lafiya ce sa its ba amma tana son ganin k'awayen ta, a k'ofar gidan Yaya Adam suka tsaya Fiddausi tace, "sun canja gida ne Zakiyya?." Zakiyya tace, "kedai muje kawai." Fita sukayi daga motar suka shiga cikin gidan suka samu Anti a tsaye a falo tana kwashe abinda aka karya suka gaisa suka tafi d'akin Ameena din.
Tana tsaye a jikin madubi tana gyara dankwali suka shigo d'akin, amsa sallama tayi ta juyo tana kallon su sai kuwa ta wara idanu tace, "Fiddausi! Kece ko kuma dai bake bace?." Fiddausi idanu suka ciko da hawaye ta matso ta rungume Ameena hawayen suka sakko tace, "Nice, Ameena nice". Ameena ita sai idanun ta suka ciko tace, "Fiddausi kece kika koma haka ne ya faru? Ta fad'a tana kallon ta tace, "Innalillahi Fidy kece?." Fiddausi hawaye ya sakko mata yace, "Nice Ameena."
Sake kallon ta take yi kafin tace, "mu zauna." Suka zauna a kan katifar Ameena tace, "Fiddausi rashin lafiya kika yi haka? Ina kika shiga bam samun ki a waya? Me ya same ki fuskar ki duk tayi tabo haka." Fiddausi ta sauke Ajiyar zuciya tace, "Ameena labarin yana da tsaho sosai, ki shirya mu tafi gidan Rukky sai mu tattauna a can." Ameena tace, "gabana fad'uwa yake yi Fidy, kinga yadda kika koma kuwa?. Zakiyya wai Meya same ta haka?."
Fiddausi tace, "ki shirya mu je kawai." Ameena ta sauke numfashi ta saka kallon Fiddausi sai ta mik'e tsaye ya d'auki mayafi ta saka ta d'auki wayar ta tace, "muje." Tare suka fito Ameena ta kalli Anti tace, "Anti zamu je gidan Rukayya."
"A dawo lafiya." Ameena suka fita suka shiga mota suka wuce gidan Rukayya. Babu wanda yake magana a cikin su har aka je k'ofar gidan direban Zakiyya ya faka motar suka fito suka shiga cikin gidan.
Rukayya tana zaune a falo tana shan tea taji anyi sallama an shigo falon ta kalli wanda suka shigo tare da amsawa, a ranta tana ayyana ashe bata kulle gidan ba, bata san lokacin da kofin ya fad'i a hannun ta ba ta mik'e tsaye tana kallon su tace, "wa nake gani kamar Fiddausi?."
Fiddausi tayi murmushi ta k'arasa kusa da ita ta rungume ta sai ta sake ta ji ciki da ya tokare ta ta d'go tana kallon ta tace, "Rukayya nice."
Rukayya tace, "Na gani Fiddasi, yaushe kika dawo? Ina kika shiga ko a waya bama samun ki?. Tun ina gida nake zuwa wajan Mama tace min anje har Abuja anje ba'a samun ki, ina kika shiga?." Suka zauna Akan kujera Ameena tace, "Kiyi magana Fiddausi kin saka zuciyar mu a rud'ani."
Tayi Ajiyar zuciya tace, "abubuwan da suka faru da yawa, abinda na sani nayi dana sanin kai kaina wannan gida da sunan naje gidan farin ciki." Rukayya tace, "ki fad'a mana Meya faru? Me ya same ki?. Ina shi Alhajin da kika aura yake?."
"Alhaji Bello na barshi ana Abuja ban San halin da yake ciki ba, guduwa nayi yadda muke ganina film a hauro daga window din bandaki ta nan na hauro Ameena."
"To me ya faru?" Rukayya ta fad'a tana kallon ta. Ta sauke numfashi ta lumshe ido ta bud'e tace, "Alhaji Bello dan luwadi ne, ba kuna iya neman maza ya tsaya ba har matan sa bai bari ba."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Ameena da Rukayya suka fad'a a tare suna kallon ta ko wacce da firgice a tare da ita idanun su a waje cikin tashin hankali. Fiddausi Tce, "Inda iya wannan ne ma da sauki, abubuwan da zaku ji a kansa yanzu sai Kun nemi ruwa a kusa daku." Babu wacce da iya magana Fiddausi ta basu labarin abinda ya faru kaf babu abinda ta b'oye musu sannan tace, "a mafarki aka ce min abinda nan zai faru dani zan karyata nace karya ne badai ni ba, sai gani nayi rayuwa dashi har ya samu nasara a kaina."
Kuka Rukayya take yi haka Ameena ma har Zakiyya ma zuciyar ta sake karyewa kuka suke gabad'aya su aka rasa wacce zatayi magana a cikin su, Fiddausi tace, "Amma ko me ya faru dani nice na jawo, nice na zab'i son zuciya na bar zab'in da Allah yayi min na tafi neman kud'i da rasu uwar jin dad'i, ga kud'in ina rayuwa a ciki amma sun kasance basu da amfani a wajena, ga jin dadin amma babu farin ciki."
Ta kalli Rukayya da take kuka sosai tace, "kin tuna abinda kika fad'a min? Akwai gidsn kud'in da babu farin ciki a cikin sa, ga kud'in amma baza su saka ni farin ciki ba saboda babu kwanciyar hankali. Amma na toshe kunne na bana ji bana gani sai da na tabbatar na cikawa kaina buri na auri Alhaji Bello. Abinda baku sani ba tun ina gidan Ibrahim nake tare da Alhaji Bello, wani lokaci da tsautsayi ya kaini wani private hospital a nan muka had'u ya d'auke ni ya kaini gidan Zakiyya daga nan muka fara waya dashi har had'uwa muke muyi zance na manta da ina da aure. A gidan Kiyya zamu had'u dashi muyi hira ayi soyayya kamar bani da aure, ban kiyaye hakkin aure a kaina ba shiyasa shima bai kiyaye ba da ya aure ni. Na tabbata zunubin kula shi da na dinga yi ina aure shiyasa Allah ya hukunta ni da abubuwan da suka faru Dani."
Ta girgiza kai tace, "Na zubar da ciki da kaina saboda na samu damar auren sa ba tare da idda ba, har gidan su Ibrahim naje a gaban iyayen sa nace ya sake ni. Ban tabbatar da nayi kuskure ba sai yanzu wallahi, ban san da cewa na fita daga aljanna na kai kaina wuta ba sai yanzu, Ameena, Rukayya, Zakiyya ban San inda zan saka raina ba, zuciyata zafi take min na rasa abinda yake damuna ba balle nayi maganin damuwa ta."
Ameena ta goge idanun ta tana kallon ta tace, "tabbas kinga rayuwa Fiddausi kin shiga cikin jarabawa, kin ga abinda baki tab'a gani ba a cikin rayuwar ki. Amma ki gode Allah da ya hukunta ki tun yanzu ba tare da kin koma gare shi ba. Dan ka smau Allah yayi maka hukunci a duniya ma rahama ne wallahi, wasu sai sunje ga Allah sannan suke ma fahimtar sunyi kuskure a lokacin babu damar neman yafiya. Ke kuwa fa? Kina da damar da zaki tuba Allah ya yafe miki duk abinda kika aikata."
"Ameena naga banbancin tsakanin rayuwar da nake hange da wacce kuke fad'a min, na dandana zaman kwanciyar hankali sannan na d'andana zaman kud'i babu kwanciyar hankali, ko wanne an rarraba min shi yadda zan fahimta sosai. Walalhi ban tab'a yin kukan rashin kwanciyar hankali ba a baya sai dai son zuciyata, amma tunda na saka k'afa ta an Abuja na tabbatar nayi ban kwana da farin ciki Ameena. Nayi dana sanin rayuwar da na daukarwa kaina" ta fad'a tana sake fashewa da kuka.
Ta sake cewa, "babban abinda yake d'aga min hankali bai wuce in na tuna nayi luwad'i ba" muryar ta tana rawa tace, "zuciyata rawa yake yi in na tuna da wannan abin ya faru a kaina, ina jin kamar na kashe kaina sboda wannan bak'in cikin da nake ji a zuciyata. Rayuwata gabad'aya ta lalace, ina zan kai wannan zunubin dana d'orawa kaina? Saboda masu aikata luwad'i akayi ruwan d'ufana, a duk sanda aka aikata shi al'arshin Allah girgiza yake yi saboda munin sa. Amma ni Fiddausi nice na aikata, ni Fiddausi nice na aikata saboda son zuciya irin tawa."