Sashe 53
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma tace, "Nidai a san abinda za'ayi yanzu dan Allah." Umma Sakina tace, "kaina ya kulle bani da abin yi a yanzun nan, sai dai zuwa da safe na d'auki hanyar gurin malam wajan wannan tsohon malamin da yayi mana aikin had'a auren Asiya din sai muji ya za'ayi." Umma tace, "Dan Allah Sakina, in auren nan ya mutu..." kafin Umma ta karasa tace, "mu muka mutu wallahi, Muna ji Muna gani kudin nan da muke samu zamu daina." Umma tace, "hakan ma bazai faru ba in sha Alalh akwai mafitar da zamu samo." Umma sakına tace, "Amma in komai ya daidata babu ke babu sake zuwa gidan su Yusuf gaskiya ki daina zubar mana da mutunci. Su kansu iyayen Yusuf din suna nan suna yi miki kallo wani iri saboda haka kawai sai ki d'auki k'afa kije kice anyi wannan anyi wancan."
"A dai gyara auren komai zai yi daidai in sha Allah."
Umma Sakina fa tab'e baki Umma ta tashi tace, "zan koma dare yayi sai naji magana mai dadi." Sallama sukayi Umma ta fita zuciyar ta cike da fatan samun nasarar mayar da Asiya gidan Yusuf.
Umma na shiga gida suka had'u da Baba ya kalle ta yayi murmushi yace, "kin d'auka auren da aka gina shi ba akan gaskiya ba zaiyi k'arko ne? Kin d'auka zaki ta samun nasara ne a duk abinda kika saka a gaba babu fad'uwa a ciki?. Meyasa baki shiryawa wannan ranar ba kika d'ora y'ar ki akan turba mara kyau? Meyasa baki shiryawa wannan ranar ba kike karb'ar duk abinda ta sato dga wajan mijin ta ta kawo miki?. Atika ai yanzu kika fara gani wallahi ko Fauziyya kika aure itama haka zata dawo miki gidan haka Momi indai baki d'ora su akan gaskiya ba a haka zaku k'are gabad'aya ku. Wani lokacin kece kike sakawa ta d'auko ta kawo miki, baki tab'a cewa ki daina ba kullum zuga ta kike kina cewa in ya deke ta ta rama, a hakan kike so kuma a zauna da ita har abada?."
Umma ta zo suya saboda haushi tace, "A kanka, wallahi akan tsiya zata k'are ba dai a kaina ba. Kuma duk bak'in cikin ka sai Asiya ta koma gidan Yusuf sai naga wanda zai haka faruwar hakan."
"Ni kuma nace miki bazata koma ba, yadda ta dawo yanzu bazai sake mayar da ita ba dan duk Wanda ya rabu da k'aya baya so ta sake sokar sa."
"İn yazo mayar da ita din ka hana, ban tab'a ganin uba mai bak'in ciki ba sai kai, kuma wallahi sai ta koma dani da kai mu zuba mu gani." Ya girgiza kai kawai ya fita dan yaji dad'in sakin da aka yiwa Asiya sosai har zuciyar sa ko babu komai zasu sake yin hankali in rabo.
Umma na shiga wajan su Asiya ta kalle ta tace, "Umma ya akayi?."
"Za'a San abinda za'ayi kar ki damu."
"Umma ina son mijina bana son rabuwa dashi. Kuma wallahi bai dake ni ba fad'uwa nayi akan hannuna shine ya karfe, dan Allah a mayar dani ina son mijina."
"Dan uban ki nace miki za'a san abinda za'ayi meyasa kike son sake b'ata min rai bayan wanda uban ki yayi yanzu? Mtswww" ta fad'a tana fita Asiya ta bita da kallo babban tashin hankalin ta bai wuce ace mijin ta yak'i mayar da ita ba dan gani take zata iya hauka baza ta iya zaman gidan su ba gabad'aya, ta saba da zama a.c bazata iya aiki da mafici ba.
#Mai daki
#Book3
#Nana Haleema
#Paid
#500
Book3
029
Kwana biyu kenan da sakin Asiya babu wanda ya yiwa Yusuf magana tana gida su har kwana a gida yake yi, babu Wanda yake masa maganar ta shima har lokacin baiyi maganar ta ba dan bama ya so ya tuna ya zauna da ita matsayin mata. A safiyar ranar talata yana zaune yana shan tea a falon Ammah har lokacin yana nan a firgice bai dawo daidai ba Abbah ya fito ya kalle shi yace, "Yusuf zaman gidan da kake bashi da amfani ka koma wajan sa'anar ka in ba haka ba zaka ga ba daidai ba." Yusuf ya kalli Abbah yace, "Abbah Usman yana yin komai kamar Ina wajan."
"Yaushe zaka je ka dawo da matar ka ne? Kayi shiru da maganar bayan nasan sakin na gargad'i kayi mata." Yusuf ya d'an rufe ido ya bud'e ya kalli Abbah yace, "bazata dawo ba."
"Meyasa? Kaje gidan nasu zaka dawo da ita din ne Kaga bata ta dawo ba?."
"Bazan je ba Abbah." Abbah ya kalli Ammah dukkan su haka suke so su ji amma basa nuna masa baso ya dawo da ita Abbah ya sake cewa, "ai kuwa dole kaje matar kace fa. Kuma nasan saki d'aya kayı mata meyasa baza kaje ka dawo da ita ba?." Kallon Abbah yayi yace, "na yanke igiyar aurena da ita gabad'aya, bana son zancen ta dan Allah Abbah" yana fad'a ya tashi ya fita.
Ammah tayi dariya tace, "Alhamdulillah, kai naji dad'i sosai Allah ya karb'i kuka na Yusuf ya dawo hayyacin sa." Abbah yayi murmushi yace, "babban tashin hankalina bai wuce yace zai dawo da yarinyar nan ba, dan wata rana wallahi sai ta siyar da gidan da suke ciki ko ta jawo masa bala'kn da bazai fitar da kansa ba."
"Tashin hankali d'aya ma kenan Alhaji, wallahi da yace zai dawo da yarinyar nan ni ban San ma halin da zan shiga ba. Yarinya ba tarbiyya, ga sata meye amfanin zama da ita?."
"Babu kam, yanzu ya dawo hankalin sa ya cigaba da harkokin sa ta inda Allah ya taimaka ma ya daina shan wannan abar tun daga lokacin da ta fad'a a wajan nan, kinga a wannan b'angaren taimakon sa ma tayi ta silar fad'ar da tayi gashi ya daina. Itama Ameena da ta fad'a tun lokacin zai iya dainawa."
Ammah tayi murmushi tace, "Ameena mata ta gari kenan, yayi asarar matar da bazai mayar da ita ba har abada." Abbah yace, "a yanayin yaron nan tsaf zai iya cewa zai dawo da Ameena fa." Ammah tayi murmushi tace, "ga hanya nan ai, Yayan ta daidai dashi ne babu wanda zai hana shi yaje ga hanya nan." Abbah yayi dariya yace, "Ni kaina Adam kwarjini yake min balle Yusuf."
"Gani nake bazai ma fara ba, yadda ya rabu da Asiya ya rabu da Ameena sai ya sake binciko wata kuma in baiyi sa'a ba ya d'auko y'ar damfara." Abbah yayi dariya itama Ammah dariya take dan farin cikin ya rabu da Asiya ya cika musu zuciya sosai.
Yusuf yana fita mota ya hau kai tsaye gidan Usman ya wuce yana tafiya yana tunani zuciyar sa tayi masa nauyi sosai ya rasa abinda yake masa dad'i kuka ma yake so yayi dan abinda yake ji bana wasa bane ba yana daurewa ne kawai amma zuciyar sa kamar an d'ora masa dutse. Har cikin gidan Usman ya shiga da motar ya ajjiye motar ya shiga gidan ya samu Umssn din a zaune yana jiran sa kamar yadda yace masa.
Yana ganin sa yace, "na shirya zan fita Allah yasa dai Lafiya." Yusuf ya zauna ya kalle shi yace, "Usman ban san ya zanyi da raina ba wallahi."
"Rabuwa da Asiyan shine baka san ya zaka yi ba?." Yusuf yace, "na rufe shafin rayuwar ta a tare dani, ku daina min wannan zancen dan Allah." Usman ya tab'e baki yace, "to an daina, Meya faru?." Yusuf yace, "nayi nadamar abinda na aikata a baya Usman, nayi dana sanin abinda na yi wallahi." Usman yace, "me aikata da kayi dana sani?."
Ya runtse idanun sa ya bud'e ya kalli Usman shima kallon sa yake da mamaki yace, "Yusuf hawaye fa kake yi." Bai daina ba sai ma fin na baya yawa da suka yi, sauka suke shar-shar yace, "na rasa da wa zanyi magana Usman, kai kad'ai zan iya fad'awa abinda yake zuciyata. Usman ina so nayi magana da Ameena dan Alalh ka taimaka min." Usman ya bishi da kallon mamaki yana yi masa kallon sama da k'asa yace, "kana so kayi magana da Ameena fa kace? To meye had'in ka da ita da zakayi magana da ita?. Ko dai Asiya kake so kace min kace Ameena?."
"Ameena nake nufi, bani da karfin guiwar tunkarar kowa na gidan mu da maganar ta, na sare domin nasan baza su bani had'in kai ba. Kai kad'an ne last hope d'ina dan Allah ka amince ka taimaka min. Wallahi in banyi magana da ita ba ban san halin da zan shiga ba."
Usman yace, "da yake ni ka raina ko dole kace haka ai. Tun lokacin da abin ya faru baka so had'uwa da ita kayi maganar ba sai yanzu da ka rabu da y'ar gwal?."
"Wallahi tun lokacin baya ina son aikata hakan ban san me yake hana ni ba, sai a cikin kwanakin nan na samu damar furta abinda yake bakina. Dan Allah ka taimaka min nayi magana da ita."
"To kace mata me?."
"Na bata hak'uri."
"Sai yanzu zaka bata hak'urin? Tun lokacin baya baka yi tunanin bata hakuri ba sai yanzu da duniya ta tafi da kai Yusuf?. Ai kayi asara wallahi wacce baza ka mayar da ita ba har abada, kaje ka dawo da yar gwal din mana ka kyale Ameena tunda baka sonta ga wacce kake so?."