← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 93

Sashe 58

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Sau nawa zance miki bana son wannan batun? Sau nawa zance a daina min in ina cikin gidan nan?. Saboda abinda yake zuciyar ki na dawo baki kula da yanayin da nake ciki ba kawai burin ki ki issr min da maganar k’awar ki, to kin isar sai me kuma na gaba?.” Ganin yana kallon ta da alama ransa a b’ace yake ta bud’e baki zatayi magana yace, “bana so, maganar nasan zaki sake yi ko to bana so, kamar yadda nace miki na manta din na manta da batun ta, amma hakan ba yana nufin a ko wanne yanayi zaki dinga min maganar ba kin gane ko?.” Zatayi magana yace, “tashi ki bani waje.” Ta rausayar da kai tace, “Kayi hak’uri ban fad’a dan na b’ata maka rai ba saboda gudun hakan tun jiya na kasa fad’a maka, dan Allah kayi hak’uri.”
“naji, amma ki bani waje tunda maganar tafi mahimmaci a wajan ki akan kula da yanayin da nake ciki.”
“Dan Allah…..” kallon ta yayi sai tayi shiru ta tashi ta fita yayi kmaramin tsaki gabad’aya ransa a b’ace yake yana mamakin mutane kiri-kiri dan Allah yayi maka arzuki a dinga yi maka bak’in ciki ko kunya ba’a ji. Bai bi ta kanta ba dan haushi yake ji in tayi masa maganar Fiddausi, gashi duk sanda zatayi hakan akwai abinda ya dawo dashi ko b’acin rai ko farin ciki.

Bayan sallar i’sha Usman yazo gidan Ammah ya samu Abbah da Ammah da kuma Mubakar suna falo gabad’aya suka gaisa Ammah tace, “Abokin naka tunda ya fita d’azu tun safe bai dawo ba sai yamma, sannan ya sake fita yayi sallah ya dawo ko abinci bai ci ba.” Usman yayi murmushi yace, “tare muke tun safen ai Ammah.”
Abbah yace, “ka dinga masa fad’a ya dinga addu’a fa.” Usman yace, “yana yi Abbah, ai Yusuf din baya wallahi ba shine yanzu ba, bawai dan ina bayan sa ba da gaske nake wallahi.”

Abbah yace, “ai haka ake so.” Ammah tace, “amma meyasa yanzu yake zama shiru-shiru ko abinci baya ci? Ka masa fad’a ya dinga cin abinci wannan ranar da yayi tayi yawa.” Yayi murmushi yace, “to Ammah in sha Alalh.” Suna cikin maganar sai ga Yusuf din ya fito ya kalli Usman yace, “kana nan bayan kasan jiran ka nake.”
“To ai gani nazo, ina zamu je?.” Ya kalli mutanen falon yace, “muje dai kawai” ya fad’a yana fita Usman ya musu sallama ya bishi a baya.
A bakin mota ya ganshi yace, “wai ina zamu je haka ka kira ni da daddaren nan?.” Yusuf yace, “Zamu je gidan su Ameena ne, ko yankar naman jikina zaiyi na amince zan tunkare shi a yanzu, in banje a dare nan ba wallahi yau bazan iya bacci ba. Shiyasa na kira ka muje ko meye zai faru ya faru na amince na yarda zan jure ko meye.”

#Mai daki
#Nana Haleema
#Paid
#500

Book3
031

Usman ya bishi da kallo daga dawowar su daga Bauchi zuwa yanzu ya sake susucewa kamar ba shi ba, shi har mamaki ma yake yi ya girgiza kai har zuciyar sa yanzu tausayin sa yake amma baya nuna masa saboda ko meye ma shine ya jawowa kansa ba wani ba. Usman yace, “kana ji, kayi hak’uri ka bari zuwa gobe k’arfe tara yanzu har tayi baza mu shigar masa gıda yanzu ba, ka bari gobe sai muje ko da safe ne.” Yusuf ya girgiza kai yace, “Usman wallahi bazan iya bacci ba, ni kad’ai nasan abinda nake ji bani da wanda zai taimake ni kuma sai kai, dan Allah ka d’aure muje Yanzun mu dawo.”

Usman yace, “Bawai nak’i bane Yusuf ka tuna zamu d’auki dogon lokaci a gidan ana magana ga dare yayi yanzu ka jira gobe in muna da rai sai na raka ka, ina son duk abinda kake so kuma ina fatan ka samu abinda kake so.” Ya d’ago ya kalle shi yace, “da gaske kana yi min fatan na sake samun Ameena a karo na biyu?.” Usman ya girgiza masa kai cikin tausayin sa yace, “kwarai kuwa, domin kuwa na tabbata baza ka yi mata rik’on banza ba a wannan lokacin, amma sai kana addu’a in ka kasa baccin a yanzu ka tashi kayi alwala ka tayar da sallah ka tuba ga Allah sannan ka fad’a masa buk’atar ka na tabbata zai biya maka ita. Inda da rabon Ameena zata sake zama da kai zata dawo rayuwar ka.”

“Usman bana bacci yanzu kullum cikin addu’a nake na tabbata shiyasa na fara dawowa hankalina, nasan nayi kuskure sosai amma komai ya faru ne tun daga lokacin da na kai kaina wajan Asiya,komai kuma ya k’are daga lokacin da na rabu da ita.” Usman yace, “Yanzu dai ka koma ciki gobe zan zo muje mu same shi indai ka shirya.” Yusuf ya sauke numfashi yace, “na shirya Usmsn, koda zai k’ona min farar jikina na shirya tunkarar sa wallahi.” Usman yayi murmushi yace, “dakyau. Amma kuma naji ana cewa Ameenan zatayi aure fa.”

Yusuf ya runtse idanun sa ya bud’e ya kalle shi yace, “babban tashin hankalina kenan, wallahi Usmsan a yadda nake ji in na rasa Ameena zan iya mutuwa.”
“To wai da duk kana sonta irin wannan son da kake fad’a ka dinga mata iskanci iri-iri?. Har cewa kayi alfarmar Ammah take ci fa kenan karya kake?.”
“Na fad’a ne kawai saboda wani dalili nawa amma Wallahi babu macen da nake so kamar Ameena, na sota kuma Ina sonta har gobe da jibi na tabbata da sonta zan mutu.” Usman yace, “to Allah ya daidai in da rabo, in babu kuma….” Da sauri ya dakatar dashi yace, “akwai ma rabon in sha Allah.” Yayi murmushi yace, “na wuce sai goben.” Kai kawai ya d’aga ya koma cikin shi kuma ya hau mota ya fita.

“Wallahi Umma ni na gaji da daman gidsn nan ga zafi ga sauro ga tuwon daren, duk laifin kine akan me zaki ce ya sake ni? Gashi yanzu ko waya bai yi min ba haka kawai kin kashe min aure kin cuce ni” Asiya ya fad’a tana hawaye tana zaune da hannun ya da yake d’aure tana jinyar kanta. Umma ta kalle ta cikin mamakin abinda take fad’a tace, “nice ma na cuce ki Asiya? Duk abubuwan da nayi a kanki baki gani ba sai yanzu da komai ya lalace?.” Asiya tace, “to Umma in ba cutata ba me kika yi? Kece kawai kika ce wai ya sake ni shi kika ya sake ni, da baki ce muje gidan ba ai da hakan bata faru ba. Nidai wallahi an cuce ni an raba ni da gıdana kuma wallahi sai na koma. Bazan zauna a wannan gidan ba ha zafi ko wuta ba’a kawowa,”

Maimuna ta mare ta tana kallon ta tace, “Umma kike fad’awa wannan maganar? Rashin kunyar taki kenan gaba yayi ba baya ba.” Ta kalle ya a fusace tace, “ina ruwan ki danj da zaki dake ni? K’arya nayi da Umman bata je ba ai da bai sake ni ba, dan kina farin ciki na dawo gida kamar ki shine zaki saka hannu ki mare ni?. To wallahi aka sake marina sai na rama kuma na rantse da Allah sai na koma gidan mijina duk bak’in cikin mutum.” Maimuna ta girgiza kai tace, “kice zaki ci uban ki a daren nan wallahi, ni zaki fad’awa wannan maganar?” Ta fad’a tana sake tsinke ta da Mari Asiya ta mik’e ga hannu a d’aure tana kuka tace, “Umma kice mata babu ruwan ta Dani wallahi ta same dukana zan rama Umma, wallahi zan rama.”
“İn na dake kin sai ki rama dan uban ki” ta fad’a tana sake dukan ta, Asiya da hannun ta mai Lafiya ta bud’e shi ta dake ta itama a baya.

“Kutmar uban nan” Maimuna ta fad’a tana fara dukan Asiya ta ko Ina tana ihu an fama mata hannu amma bakin ta baiyi shiru ba tana sake zazzaga mata rashin kunya Umma dai kallon su take ta kasa magana zuciyar ta zafi take mata sosai akan abinda suke yi ta kuma san ko zatayi magana sau goma baza su daina ba.” Sai da Maimuna taga Asiya jiki yayi sanyi sannan ta kyale ta tace, “nan gaba in akace ki sake min rashin kunya ki sake yi na gani, gwara ma da Yusuf din ya koro ki ai kizo mu gwabza dani dake aga waye mai nasara. Shashasha mahaukaciya k’azamar banza da wofi wacce ko pant bata canjawa.”

Momi da Fauziyya suna zaune suna kallon su babu wacce ta motsa dan gwara da ta zane Asiyan iskanci take ji dashi daman a gidan. Asiya jiki yayi tsami sai kuka take gata a kwance hannu nayi mata ciwo sosai a haka ta tashi ta shiga d’aki tana kuka tana cewa, “wallahi gıdana zan koma bazan cigaba da zama a nan ba, kuma wallahi na koma naga k’afar wata shegiya a gidan sai naci bu** uban ta.” Umma kallon ta yake har ta shige ciki sannan ta sauke numfashi Momi tace, “Umma ai kad’an kika gani indai daga rashin tarbiyyar Asiya ne, wannan da kike gani Umma hmmmm.” Umma dai ta kasa cewa komai domin abin yafi k’arfin ta ta tashi ta shiga d’aki kawai bata iya magana ba.

Washe gari Umma Sakina tazo tun safe Asiya na zaune sai da aka kira mai gyara ya duba hannun aka tabbatar lafiya yake dan sun d’auka ya goce, tana zaune sai kunbure-kunbure take yi Umma ta kalli Umma Sakina tace, “Ya ake ciki da lamarin nan dan Allah? Abin nan ya fara damuna shiru har kwana hud’u ba waya babu zuwa?.” Umma Sskina tace, “Ai kawai ayi hak’uri auren nan nasu ya mutu, duk inda naje abinda ake fad’a min kenan auren ya mutu bazai mayar da ita ba.”
“K’arya suke wallahi sai na koma gidan mijina” Asiya ta fad’a tana daga gefe Umma Sakina ta kalle ta bata ce komai ba Umma tace, “Sakina wacce irin magana kike haka? Kamar ya auren ya mutu kuma?.”
Chapter 58 · 0% Book details