← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 93

Sashe 71

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf yace, "haka ne na amince na yarda, na gode Allah ya saka da alkhairi." Al'ameen ya amsa gabad’aya jikin sa yayi masa sanyi sosai zuciyar sa nayi masa wani iri ya rasa me zaice masa ma. A haka  Yusuf ya fito ya shiga mota ya tafi yana tafiya Adam ya fito ya shiga gidan ya samu Al'ameen a tsaye ya hard’e hannun sa a kirji yana kallon k'asa yace, "Yusuf dai naga yana neman canja maka ra'ayi daga auren Ameena." Al'ameen ya kalle shi yace, "nawa Yusuf din yake da zai canja min ra'ayi? A shekaru na girme masa kai ka sani. Kawai ya bani tausayi ne sosai soyayya tana d'awainiya dashi sannan kuma ya gane kuskuren sa, gashi babu damar sake mallakar ta a wannan lokacin Ameena tawa ce."

Adam yayi shiru na wani lokaci hakan ya saka Al'ameen yace, "ka bibiyi Ameena indai har Ameena tana son komawa gidan sa ka sake bashi dama soja, yayi nadama a idanun sa zaka hango hakan, yayi dana sani sosai, kuma da gaskiyar sa meye amfanin raba yara gidan maza guda biyu da k’ananun shekarun Ameena?. Indai Ameena tana son sa a karo na biyu ka bashi dama na tabbatar in sha Allah baza ka yi dana sani ba. Ni yanayin da ya fita ma ban amince dashi ba wallahi.” Adam ya rufe ido ya bud'e ya kalle shi yace, "bana jin zan sake bawa Yusuf Ameena Al'Ameen, bana son ta sake maimaita rayuwar da tayi a baya gaskiya. Dan haka a bar maganar sa kawai a cigaba da abinda yake gaban mu."
Al'ameen yace, "shikenan Allah yasa mu dace." Ya amsa da amin sannan suka fara maganar da ta kawo Adam din wajan sa.

         "Ni wallahi bazan ci shinkafa da manja babu yaji ba, wannan wanne irin bala'i ne da safe na sha shayi babu sugar na kirki ko madara ma babu yanzu kuma da rana an bani shinkafa da manja ace naci kuma ko yaji babu wai na saka maggi?.” Maimuna ta kalli Asiya tace, "kar kici mana ba cikin ki ba." Asiya tace, "Nidai wallahi na gaji, an cuce ni an raba ni da mijina da gidana mai kyau kullum cikin haske da a.c amma tunda nazo gidan nan sau d'aya aka kwana da wuta. Zafi, sauro, kyankyaso babu abinda babu a gidan nan Nidai na gaji wallahi."

Momi tayi dariya tace, "sai ki tashi ki koma ai tunda ba a nan kika rayuwa ba, y’ar wahala kawai.” Fauziyya ce ta fito daga d’aki a fusace tana hawaye tace, "Umma! Umma!!." Umma da take zaune tace, "Lafiya kike min wanna kira kamar makauniya?."
"Wai Umma wanne hali muke dashi ne a unguwar nan da ake cewa bamu da tarbiyya mun raina kowa? Wai Umma wacce tarbiyya kika bamu har Surajo yace ya fasa aurena Umma?. Wai yaji labarin an kama ki akan bashi an kama Asiya akan sata shi bazai iya had'a zuri'a dani ba, Umma na hud’u kenan yana cewa ya fasa aurena wacce irin tarbiyya muke da iya haka da suke gudun had’a zuri’a damu?.”

Momi taja numfashi tace, "nima na gaji Fauzy, kowa yazo sai an kora shi ace bani da tarbiyya daga ranar banza sake ganin sa ba, gaskiya nima ina d a tambayar akan tarbiyyar mu, wacc iri ce damu da muka kasa auruwa Umma? Wacce tarbiyya kika yi mana haka?.” Duk kallon Umma suke yi suna jira suji abinda zata ce sai tace, "da kuka zuba min ido kin manta abinda yake gaban mu ne? Bashin Sakina an ina zamu samo kud’in da zamu bata ?."
"Umma fasa aurena yafi bahsin ta, Umma wacce irin tarbiyya kika bamu da ba’a son auren mu?." Umma ta kalle ta tace, "Allah zai kawo miki wani kinmanta da batun sa." Ta zube a wajan tana kuka tace, "nidai Ina son Surajo wallahi, ina son zama dashi a san yadda za'ayi ya aure ni kawai. Yace min yanzu zasu zo wajan Baba Karb’ar kudin auren da suka kawo, Nidai a San abinda za’a yi min kar na sake rasa mai sona.”

Asiya tace, "ni dai an gama da rayuwata, na smau mijin an raba ni dashi yanzu gashi ke baki samu ba balle ni bazawara." Umma kallon su kawai take yi sai ta mik’e ta fita tsakar gida dan bata san me zata ce musu ba. Da aBaba suka had'u ya kalle ta ta gyara tsayawa kafin tayi magana yace, "dangin masu neman auren Fauziyya ne suka zo, sun fasa suna buk’atar a dawo musu da kud'in auren da suka kawo. Kawo a basu suna waje suna jira."

Umma ta marairaice tace, "ina naga naira dubu d’ari balle na fito da ita? Ina na ganta malam?. Dan girman Allah ka rufa min asiri ka bayar zan biya ka wallahi." Baba yace, "me nake dashi da zan bayar? Kin manta ni mai musu bak'in ciki ne? Me na ajjiye da zan d'auko na bada naira dubu Dari Atika?." Umma tace, "nidai kayi hak'uri dan girman Allah ka bayar." Baba ya girgiza kai yace, "yau ni kike bawa hak'uri Atika? Lallai duniya ta bi dake. Kin manta ajjiye kudin ma hanawa kika yi a hannun Yayana? Kuma kika dinga  wulakanci akan dubu d’ari sai an baki ke kika haifa ba wani ya haifar miki ba. To yanzu sai ki bayar tunda ke kika haife su ba wani ba."

Umma tace, "kayi min rai walalhi bani dashi bani da inda zan samo su wallahi.”
"Zan fad'a musu babu, amma gobe sai su zo su karb'a" ya fad'a yana ficewa Umms ta zube a wajan tace, "na shiga uku wai me yake faruwa dani ne lokaci d’aya haka?.”

"Bake mara mutunci wacce bata san mutunci ba, ai yanzu kika fara gani" Umma Sakina ta fad'a tana shigowa tana kallon ta. Umma ta d’ago ta kalle ta kafin tayi magana ta nuna mata zobe tace, "wanda aka siya da kudin da Asiya ta sato a wajan mijin ta, jiya na tuna dashi a wajan mai siyarwa naje na cika masa kud’in na bashi takarda ya bani zobe da takardar shaidar biya. Gashi a hannu na naira dubu d’ari biyar da hamsin muka siya, in kin bani kudina zan baki in baki bani ba zan rik'e bazan ce zan siyar ba rik’ewa zanyi duka ya zama nawa in akwai abinda zaki iya sai kiyi, in kina da hujjar da zata nuna naki ne sai kije ki kaini kara." Ta fad'a tana fi cewa tare da yin tsaki ta bar Umma a wajan tana kallon ta.

Umma baya tayi t kwanta a k’asa dan ta manta da batun zoben a hannun Sakina, a bayyane tace, “shikenan komai ya k’are, meyasa na amince na bar mata receipt din a hannun ta? Meyasa nayi wannan gangancin ni Atika?.” Umma dai tana neman fita daga hankalin ta dan komai ya k’are mata bata da komai ta dawo matsiyaciyar ta kamar yadda take a baya, gashi babu Asiya balle a sake tarawa.

        Yusuf zagaye yake kawai a mota bai San inda yake nufa ba tafiya yake yi kawai amma hankalin sa da tunanin sa basa tare dashi, horn ake masa ta ko ina sai aka sake rud'a shi ya gigice yana kaucewa kafin ya farga wata mota da tawo daga gefen sa ta daki motar tasa tayi baya ta juya ya daki fitilar titi.
 Usman da ya ga motar ya tsaya da sauri ya k'araso wajan mutane sun fara taruwa ya bud'e motar aka fito da Yusuf daga motar Usman ya saka shi a tasa hankali tashe ya wuce asibiti dashi.

Emergency aka kai shi aka fara duba shi dan ya bubbuge a fuska, Usman hankalin ya tashi sosai ya kire Abbah ya fad'a masa halin da ake ciki ba jimawa sai ga y'an gidan su da Abbah amma babu Ammah ya kalli Usman yace, "yana ina? Yaushe yayi accident din?." Usman yace, "ban sani ba naga motar tasa a hanya sai ban amince da tuk’kn da yake ba na kira shi akan nace yayi parking gani a bayan sa bai d'auka ba, shi ya wuce sai danger ta tsare ni wallahi ina zuwa na ganshi a gefe wata mota ta daki motar sa kuma ban ga motar da ta daki tasan ba.” 

"Innalillahi wa'inna ilahiri raji'un! Ina yaje to?." Usmsn yace, "yayi yayi dani akan na raka shi wajan abokin Adam Yayan Ameena nak’i shine yace zai tafi da kansa, kuma wajan abokin Adam din da yaje shine zai auri Ameenan shiyasa nace bazan je ba dan naga alamaa shi bai ma gane shi ba lokacin aka nuna mana shi a matsayin miji. Wallahi Abbah yana son Ameena na tabbata tunani ne ya saka shi yayi accident, in ya rasa Ameena gabad’aya wanne hali zai shiga kenan?.”

Abbah ya kalli y'an uwan sa da suke jin abinda yake cewa Mubakar yace, "Abbah na amince Yusuf ya saduda, dan Allah a bashi dama a karo na biyu." Abbah yayi shiru baice komai ba sai a lokacin likita ya fito ya kalli Usman yace, "kar ka damu ya samu bugawa ne kawai a hannun sa sai fuskar sa da ta ji ciwo amma bayan wannan babu komai." Usman yace, "na gode Dr." ya tafi suka shiga d'akin suka ga sun d'aure masa hannu ga fuskar sa an saka flasta a goshin sa da kuma gefen fuskar sa da kuma wuyan sa.

Abbah ya d'aga goshin sa yace, "Yusuf kayi hak'uri bazan iya shiga maganar Ameena ba, bazan sake shiga maganar ba balle nace a sake baka dama. Kayi hak’uri ka rungumi k’addara a yadda tazo maka.” Shiru sukayi dukkan su kowa yayi shiru amma zuciyar kowa babu dad'i kowa yana kin tausayin  sa a zuciyar sa har Abbah din.
Chapter 71 · 0% Book details