Sashe 87
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ameena tace, “kunga dai bamu jima sosai da komawa ba amma in zaman mu ya d’ore a haka wallahi yafi na baya dad’i da kwanciyar hankali, domin yadda aka d’auko wannan ma daban da yadda aka d’auki wancan. Sannan a yanzu soyayyar da yake min tafi ta baya yawa nesa ba kusa ba. Ke ni indai haka komawa mijin da aka rabu yake zan iya cewa mata su koma su daina la’akari da baya sun kawar da komai daga ransu watakila silar canjawar su ne ya kawo kaddarar sakin.”
Fiddausi tace, “wallahi kuwa. Tsoro da fargaba halin da ka bari shine yake saka mata basa son komawa gidan wanda suka bari, amma wani lokacin in kika koma sai kin fi baya farin ciki domin sun gane kuskuren su. Musamman ma ke Ameena da ya damu sosai akan lamarin ki harda ciwo dasu kwanciya a asibiti, nadamar sa a bayyane take kowa yasan yayi nadama akan abinda yayi dole zaman ku yayi dad’i ynzu.” Zakiyya tace, “Gaskiya ne, Allah ya d’orar da zaman Baku har abada.” Ta amsa da amin tana kallon Fiddausi tace, “wallahi kema Kinyi kyau hasken ki ya dawo sosai, Allah ya kawo mana miji na gari kiyi aure ki huta kema.”
Fiddausi tayi murmushi kawai Rukayya tace, “ya kusa zuwa in sha Allah.” Suka amsa gabad’ayan su suka dinga hirs har Rukyyan ta koma daki ta kwanta tayi bacci mai kula da ita kanwar Umma ita kuma yarinyar na hannun ta. Sai dare yamma Fiddausi da Zakiyya suka tafi ita kuma tana zaman jiran Yusuf bai zo ba har ibrshim ya dawo sannan yazo ya shigo har gidan yayi mata barka da abinda aka samu ya bata kudi sannan suka tafi da Ameena.
Ranar suna yarinya taci sunan Umman ta ake kiran ta da Noor su Ameena anzo anyi suna tare dasu ko wacce akwai abinda ta kawo matsayin ta ta gudunmawar ta samun noor a matsayin yar su.
Washe garin suna da daddare Rukayya tana zaune a d’aki wacce take kula da ita ganin İbrahim ya dawo sai ta bar d’akin ya shigo ya zauna yana kallon ta da Noor din a hannu yana murmushi ga Amir a gefe ma hana ta tab’a kumatun yarinyar. Kallon Amir yayi yace, “Amir nayi k’anwa ko?.” Yayi dariya dan murna yake yi sosai sai kuma ya fita a guje jin k’anwar Umma tana kiran sa ibrshim ya kalle ta yace, “Habibty bani ita.” Ba musu ta bashi ita yana kallon ta yace, “kin San meyasa nake son ta?.” Ta girgiza kai alamun A’a yace, “saboda tana kama dake sosai.” Tayi murmushi tace, “ni bana gane kamannin jarirai, ka bari ta girma tukunna.”
Yayi murmushi yace, “haihuwar ta tazo mana da alkhairi Habibaty.” Ta kalle shi tace, “meya faru?.”
“Mai gidan mu, wanda bai bawa saudia ba su kuma ya saka niyar su zai basu mota amma wanda suke jajircewa a aiki. Ina fad’a miki ya sake saka sunana ga mota can sabuwa dal a ajjiye a waje.” Rukayya ta wara ido tace, “da gaske kake wai?.” Ya d’aga kai yace, “da gaske nake wallahi, kinga ma key din” ya fad’a yana nuna mata makullin tace, “wannan bawan Allah wanne irin so yake maka Khalil? Ka duba kayan da ya baka aka kawowa Noor.”
Yayi murmushi yace, “in ka rik’e gaskiya a duk inda kake sai Kaga abinda zai same ka. Yana sona sosai shiyasa na tara makiya a wajan kowa baya sona, hatta baban yaron sa a da yanzu yafi ji dani akan sa. Ana ta cewa asiri nake yi basu san ni addu’ar iyaye ce take d’awainiya dani ba.”
Rukayya tace, “kar ka wani damu da wannan daman dole a samu makiya duk inda cigaba yake sai an samu masu bak’in ciki. Allah yana tare dakai babu abinda zai iya yi.”
“Ki cigaba da taya ni addu’a basa sona a tare dashi zasu iya yin komai dan su raba mu.”
“Allah ya fisu wallahi.”
“Bayan motar fa yace min in kin yi kwari zamu tattara mu koma Abuja inda babban kamfanin sa yake ya kuma ya bar min ragamar kamfanin gabad’aya Rukayya. Ni na rasa me zan yiwa bawan Allah nan da zan nuna amsa na gode da abubuwan da yake min ba walalhi.”
“Addu’a zaka masa Khalil bayan wannan bamu da abinda zamu biya shi.” Ya girgiza kai yace, “Gaskiya be wannan. Yanzu ga sabuwar mota can zaki iya zuwa ki gani?.” Ta kalle shi cikin farin ciki tace, “zan iya mana.” Yayi murmushi yace, “to ki zauna dai Kya gani gobe dare yayi gobe.”
Sai murmushi yaga Tana yi yace, “ya kike ganin za’a yi da tsohuwar?.” Ya kalle shi tace, “ka siyar mana kawai.”
“Bayarwa nake son nayi, yadda aka bani nayi murna nima na bayar.”
“To ka bawa Alhaji mana kawai.” Yayi dariya yana jin dad’in yadda komai na alkhairi iyayen sa take fara sakawa kafin kanta hakan yana k’ara mata matsayi sosai a zuciyar sa yana kuma saka shi farin ciki girman ta na sake yin sama a idanun da yace, “ban da Alhaji.”
Tace, “to wa zaka bawa?.”
“Ke bakya so?.” Ta kalle shi jin abinda yace tace, “ina so mana. Amma ni ban iya ba ai Alhaji shi ya kamata a bawa bank ba.” Ya bud’e hannun ta ya saka mata muku kin motar yace, “nima ban iya ba koya min akayi. Rukayya ke na barwa halak malak, makarantar koya kawai ta zaki shiga ki koya ki fara tuk’awa kina zuwa duk inda zaki je.” Rukayya ta rasa abinda zata ce ta gigice saboda farin ciki zatayi magana yace, “kar kice komai Rukayya, nasan kin gode Kinyi farin ciki, iya ganin farın cikin naki yafi min komai.”
Sai ta saka kuka ya kwantar da noor agefe ya runtgume ta yana cewa, “meye na kukan kuma? Kin cancanci kyautar ne, in ina da duniya zan iya mallaka miki domin kin cancanci koma meye daga wajena. Ki daina kuka kinji?.” Ta rik’e shi sosai tana kuka tace, “na gode Khalil, Allah ya k’ara bud’a maka ya kare ka daga dukkan sharrin mak’iya.” Ya amsa da amin yana cigaba da rarrashin ta domin shi a duniya indai zai samu goma to zai d’auki biyar ya bata biyar, haka d’abi’ar sa take sai kuma ya samu mace ta gari mai sake d’ora shi akan hanyar alkhairi shiyasa yake son kyautata mata a ko yaushe indai zatayi farin ciki shine burin sa.
#Mai daki
#Nana Haleema
#Book3
Book3
043
Umma ce zaune sa a gaban Baba tana jira ya gama cin abinci ta gabatar masa da abinda tazo dashi ya kalle ta yace, "kin zo kinyi shiru ki fad'a min abinda yake tafe dake. Lafiya kika saka ni a gaba kina kallo?." Umma tace, "daman akan maganar yaran nan ne, Maimuna, Fauziyya, Asiya ga Momi dukkan su suna zaune babu mazajen nema. Su biyun can ma zawara ne a ajjiye batun su, amma Fauziyya da Momi sune y’an mata har yanzu babu wani wanda yake zuwa wajan su. Wallahi abin nan dashi nake kwana nake dashi dan Alalh malam ka taimaka."
Baba ya girgiza Kai cikin mamaki yace, "Atika yau ni kika samu kina yiwa maganar da ta shafi yaran ki? Kamar ke kika ce babu ruwa na ko wando ban tab'a basu ba ke kike da iko dasu ko?."
"Malam a daina tuna baya dan Allah, yanzu muyi abinda yake gaban mu kawai. Nace cikin wanda suka ce suna son su a dangin ku a lalubo su su zo ayi auren a rufawa juna asiri." Baba yayi dariya yace, "inaaa wane mutum! Ai y'ay'an ki ba kalar dangina bane ba su, sun fi karfin dangina da basu ajjiye ko sisi a banki ba, yaran ki ai ba tsaran auren su bane, ki bari su samu daidai su su aura amma banda naki."
Umma tayi shiru kafin tace, "Malam duk maganar nan ta wuce bai kamata ace anyi ta ba, dan Allah a bar zancen nan ayi abinda ya kamata. Momi ce k'arama a cikin su ita kanta ta haura shekara ashirin balle su. Dan Allah a san abinda za'ayi."
"Baki ji me nace miki bane? Yaran ki ba daidai suke da auren wanda kike magana Akan su ba, dan haka ki bari daidai su suzo sai ayi magana ta auren su amma banda dangina. Nan na same ku akan mai son Maimuna kika yi tsallake kika dire kika ce baza’a yi ba ba wani a duniya da ya isa ya aurar miki da yara, a lokacin kaina a jure yake ban cika gane daidai ba sai Allah yayi ni kuma na kyale ki, amma in da yanzu ne ke kin isa? Ba sai dai ki bar gidan nan ba wallahi.”
Umma tace, "a bar batun baya dan Allah malam."
"Ke kika sani kuma, kin yiwa yaran tarbiyar da ke kanki yanzu gagarar ki suke balle kuma wasu. Kije kiji dasu babu abinda ya shafe ni wallahi komai ya faru ke kika jawowa kanki. Asiya ke kika kashe mata aure dan da baki dinga d'ora ta akan turbar da kika dora ta ba da yanzu tana Idan mijin ta. kud'i ake nema a yiwa Asiya waya, abinci Asiya waya, kayan sawa Asiya, komai ita gashi sai da kika b'alla auren hankalin ki ya kwanta. Babu ruwana da lamarin ku wallahi kije can ku k'arata" ya fad'a hana tashi ya bata wajan Umma ta d’ora hannu aka ya bata san ya zatayi da yaran ba gashi tashen rashin kunya suke ji da ita ko ita din ba kyale ga sukayi ba balle wani daban.
Fitowa Umma tayi taga Asiya a tsaye ita da Maimuna Umma ta kalle su dan tasan fad'an ake tab'awa Maimuna Tce, "Umma ki yiwa yarinyar nan magana a ko yaushe burin ta muyi dambe a gidan nan, ta raina ni gabad'aya ki Tuna mata akwai Fauziyya kafin ita." Asiya tace, "ni ina ruwana? Ko mata dubu ne kafin ni akayi min sai na mayarwa da mutum. Kar a sake cemin b'arauniya kuma dan ba'a ajjiye na d'auka ba."