Sashe 56
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tana shiga wanka tayi maganar tak’i barin zuciyar ta amma wallahi ita darıya abin yake bata tana shiryawa tana murmushi ta zauna a gefen katifar ta tace, “Yaya Al’ameen rigima kamar yaro k’arami, yanzu nace bana ra’ayi ma ai shiga uku” Tayi dariya a bayyane tace, “zamu gani dai” ta fad’a tana tashi ta fito falo dan ayi hira da ita. Tana jiyo maganar sa shida Yaya a bakin k’ofar falon haka nan taji kawai tana so taga fuskar sa sai ta koma d’aki ta d’auko karamin mayafi ta yafa ta fito Zaytun ta biyo bayan ta sai ta juyo tana kallon Zaytun kamar bata san suna wajan ba tace, “ki tsaya a nan abu zan duba mota nayi mantuwa.”
Motar ta nufa sai kuma ta tuna motar ma a kulle take ta kalli inda suke nan take suka had’a ido dashi da alamaa kallon ta yake yi sai tayi murmushi ta k’araso tace, “ina wuni, Yaya ina key din motar nan kamar nayi mantuwar littafi.” Mik’a mata key din yayi ya nufi motar ta bud’e tana ta dube-dube kamar gaske shi kuma yana yiwa Yaya Adam magana.
Rufe motar tayi ta dawo ta wuce ciki bata bashi key din ba ya kalli Adam bayan ta wuce yace, “Dan Allah ka taimakawa marayan nan ka bashi auren yarinyar nan.” Adam yace, “taya zan hana ka auren Ameena ne wai? Nayi mata magana da ita tace na b’ata lokaci ka jira muji ne zata ce mana.” Ya sauke Ajiyar zuciya yace, “Allah yasa.” Ya amsa da amin kafin ya fita.
Washe gari Yusuf da Usman da safe suka d’auki hanyar bauchi Usman bai tambaye shi abinda zasu ba tunda yasan akwai Yayar Ameena a can bai damu ba yasan can zasu je. Basu shiga ba sai gab da azahar a k’ofar gidan ta suka tsaya yana fitowa daga motar Ameera na sauka daga adaidaita sahu ta bawa mai napep din kud’in ta juyo ta kalli Yusuf ya sake kallon sa ta tabbatar shine kafin tayi magana yace, “Amira.” A ciki tace, “Na’am, ina wuni.”
“Lafiya lau, dan Alalh ki fad’awa Yayan zuwan mu.” kai kawai ta girgiza ta shiga ciki tana mamakin zuwan sa.
A tsakar gida ya same ya ita kad’ai Kasancewar lokacin makaranta duk basa nan ta kalle tace, “Mama kin San waye a waje a k’ofar gidan nan?.”
“Waye?.”
“Yusuf tsohon mijin Anti Ameena wai yana son na sanar dake zuwan sa.” Yaya ta kalle ta tace, “Yusuf kuma Amira?.”
“Eh wallahi, gashi can a tsaye shida wani. Ko uban me ya kawo shi ma oho.” Yaya tace, “gashi mai gidan baya nan, amma jeki kice ya shigo.” Ta ajjiye aiken da aka yi mata ta fita ita kuma Yayan ta tashi ta shiga ciki ta saka hijjabi ta shinfid’a tabarma.
Da sallama ya shigo bayan sa Usman Yaya tace, “Ashe da gaske kai din ne, bismillah ku k’araso.” Yusuf suka k’arasa suka zauna ta kalli Amira tace, “kawo musu ruwa da lemo, ki kawo Abinci.” Amira ta bar wajan Yusuf ya gaida Yaya ta amsa haka Usman ma Amira ta kawo ruwa ta ajjiye musu a gaban su Yaya tace, “kawo musu abincin mana.” Yusuf yace, “A’a a barshi Yaya, Alhamdulillah iya ruwan ya isa.” Yaya tayi shiru dan ita batayi tunanin daga kano suke ba tayi tunanin aiki ne ya kawo shi ya biyo su gaisa. Yaya tace, “naji dad’i da ka biyo muka gaisa sosai.” Yusuf yace, “Yaya ai daga kano muke kai tsaye nan muka zo.”
Da mamaki tace, “kano! Kaii ashe doguwar tafiya kuka yo, na d’auka aiki ne ya kawo ka nan din ka biyo mu gaisa. Kai kai ashe a gajiya kuke sosai.” Yusuf yace, “babu komai ai Yaya. Magana nazo muyi.”
“To baka huta ba kuma sai magana?.”
“Babu komai ai Yaya.”
“To ina ji, Allah yasa dai Lafiya.”
“Ba Lafiya ba.” Tace, “to me ya faru?.” Ya sauke numfashi yace, “Yaya dan girman Allah abinda ya faru a baya wanda na aikata dan Allah ayi hakuri a yafe min. Nasan nayi kuskure ni kaina wallahi, nayi abinda baza ki manta dani ba, amma ki yi hak’uri na gane kuskurena nayi nadamar abubuwan dana aikata.”
Yaya tayi murmushi tace, “to Yusuf ni ai bani ya kamata kazo ka bawa hak’uri ba, Adam da Ameena zaka je ka samu bani ba. Ameena aka yiwa laifi wanda zai biyo bayan ta kuma Yaya ne, meyasa ni kazo wajena kai tsaye?.”
“Na kasa tunkarar ta da maganar nan, na kasa zuwa gidan balle nayi magana. Dake nake so nayi kamun k’afa ki yi min iso domin gyara abinda na b’ata.” Yaya ta kalli Amira da da take aikin kallon Yusuf ta sake kallon Yusuf din kafin tayi magana Amira tace, “wai ni ban gane ba, ayi hak’uri akan me? Wai ta koma gidan ka?” Sai tayi dariya tace, “lallai ma Daddyn Zaytun din nan, ai har abada Anti Ameena ta bar gidan ka wallahi, duk abubuwan da suka faru tun lokacin baka zo bada hak’urin ba sai yanzu da lokaci ya k’ure maka?.”
Yaya ta kalle ta tace, “Amira meye haka?.”
“Mama ki barni nayi magana, baki San komai ba nice nasan waye shi a cikin gidan sa. Bai tab’a jin kunyar idanuna ya d’agawa Anti k’afa akan fad’an da yake mata ba, bai tab’a jin nauyi na ba a gabana zai mata tsawa sai dai ita ta bar wajan saboda tana jin nauyin faruwar hakan a gabana. Bai san ya ta tashi ba bai San ina kika je ba ko bata da lafiya baya damuwa amma in akace Zaitun ce babu lafiya daga wannan lokacin kwana zatayi tana kuka. Anti Ameena ta kasa cin abinci, Kullum a tunani da damuwa take har hakan ya saka mata hawan jini amma ban tab’a gani ko naji yace ya kika kwana ba. Tun Anti Ameena na b’oye min bata so na fahimta har na gane saboda itace mai b’oyewa shi baya jin nauyin mata fad’a a gabana. Duk abinda matar sa tace dashi yake yi amfani bai tab’a yin nazari akan abubuwan da take fad’a masa ba komai hawa kai yake yana zama ko yaushe Aunty ce mai laifi.”
Ta kalli Yaya tace, “har wajan ta suka zo suka zagi Mama da take kabari amma Anti tace min Amira mu bar wajan nan kare ya fara haushi suka sake ambatar sunan Mama suka d ma itace karya. A wannan lokacin ne Anti ta Mari matar sa tace kar ta sake kasa mata uwa a lamarin ta. Ashe plan ne sai d’ayar ta fita tayi masa waya yana zuwa bai san hawa ba bai san sauka ba a kan idona ya mari Anti Ameena. Ni kuka ita kuka haka muke kwana, ita take tilasta min cin abinci amma ita ta kasa cin abincin.” Yaya ta kalle ta tace, “Malama kiyi mana shiru ki bar wajan nan kafin ranki ya b’aci.”
Amira bata ji me ma take cewa ba ta sake cewa, “Kamar yadda Zaytun ka sani itace mutum in babu Lafiya hankalin ka yake tashi haka mu ma hankalin mu yake tashi in bata da lafiya. Sai yanzu da aka kusa shekara sannan zaka zo kace ayi hak’uri? Ai wallahi kayi sake Anti Ameena ta Yaya Al’ameen ce babu wanda zai raba ta dashi a wannan lokacin.” Ta kalli Yaya tace c “kiyi hak’uri Mama abin nan ya jima a zuciya sai yanzu na samu damar fad’a, ni kad’ai nasan meye a gidan daddyn Zaitun domin ni na zauna da ita dashi a cikin gidan. Kiyi hak’uri ban fad’a dan na b’ata miki rai ba.” tana kuka ta bar tsakar gidan da sauri ta shiga d’aki.
Yusuf yayi shiru zuciyar tayi sanyi haka jikin sa ma Usman ya tab’e baki kawai baice komai ba dan baiga laifin Amira ba gaskiya ya fad’a duk abinda aka aikata laifin sane, kuma tun lokacin meyasa bai bayar da hak’urin ba sai yanzu?. Yaya tace, “kiyi hakuri da abinda Amira tayi akwai yarinta a lamarin ta.” Usman yace, “Gaskiya ta fad’a Yaya, duk abinda tace yayi ne da ba’a yi ba da zata fad’a ba ai.” Yusuf ya kalli Yaya da idanun sa jajaye yace, “na fad’a naki nayi kuskure Yaya nasan da hakan, amma in neman afuwar ta amma bani da karfin guiwar tunkarar ta wallah. Duk abinda Amira tace nasan gaskiya ne Yaya, amma Allah nayi nadamar duk abinda na aikata.” Yaya tace, “hak’uri ita zaka je ka samu in ka b’ata hakuri ta hak’ura kaga shikenan sai kowa ya kama gaban sa kai kasan babu hakkin ta a kanka saboda ta yafe maka. Amma ni ai ba ni aka yiwa laifi ba bazan ce an yafe maka ba ba tare da Kaji ta bakin ta ba.”