← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 93

Sashe 8

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nice ranki ya dad'ega abinci ma na kammala. Akwai shayi, akwai kunu, akwai dankali akwai doya da kwai, akwai kunun gyad'a da farfesun Kaji." Fiddausi ya sake yin murmushi tace, "to na gode."

"Aikina ne ranki ya dade, akwai abinda kike so?." Fiddausi tace, "eh, ki shiga ki gyara min daki a wanke bandaki."

"To hajiya" ta fad'a tana tashi ta wuce zuwa d'aki da Fiddausin ta fito.

Fiddausi tayi dariya ta tafa hannu tace, "Duniya sabuwa" ta d'ora kafa akan center table ta kad'awa tace, "Allah ya ka bamu kud'i." Tashi tayi zuwa inda abincin yake taja kujera ta zauna ta had'a tea shegen kauri tana sha tana danna waya suna gaisawa da mutanen gidan su. Tana cikin karyawa ta fito tace, "Hajiya na gama, akwai abinda za'a yi?." Fiddausi ya kalle ta kalle ta tace, "No kije in akwai zan kira ki."ta amsa da girmamawa zata bar wajan Fiddausi tace, "ina ne wajan ku?." Ladidi tace, "Nan baya ne, ga waya nan a ajjiye in kina nemana zaki danna sifuli zan d'auka." Fiddausi ta d'aga kai Ladidi ta tafi ta cigaba da cin abincin ta . Sai da taci ta koshi sannan ta taso tana sake kallon falon ya fito zuwa babban falon ta.

Tana fitowa mata guda biyu suka shigo da sallama ta amsa tana kallon su d'aya daga cikin su tace, "Amarya barka da warhaka, zamu iya zama." Fiddausi tayi murmushi tace, "barka dai, bismillah ku zauna." Dukkan su suka zauna harda ita ta bisu da kallo ganin su kyawawa farare kamar ta dan a shekaru ma baza su wuce sa'anin ta ba. D'aya daga ciki tace, "Amarya ya kwanan bak'unta?."

"Alhamdulillah" ta fad'a da murmushi tana kallon su.

D'aya tace, "Ni sunana Aliya mata a wajan mijin ki nice ta biyu a yanzu." D'ayar ma tace, "Ni kuma sunana Naja'atu nice mata ta uku a wajan mijin ki, ke kuma kin kasance da hud'u kenan" ta fad'a tana kallon sa tana murmushi.

Fiddausi ta bisu da kallo tace, "wai da gaske ko da wasa?." Sukayi dariya Aliya tace, "Wallahi da gaske muke, kinga kamar ba haka ba ko?." Fiddausi tace, "amma ni ai matan sa uku na sani." Naja'atu tayi murmushi tace, "eh ta uku har ke ba, ai ta farko ba'a saka ta a lissafi domin itace uwar gida uwar yaran sa ita daban damu, ko nace itama ba matar sa bace amma akwai ta farko kafin Aliya."

Fiddausi tace, "ban gane ba." Aliya yayi murmushi tace, "Zaki gane sai nan gaba. Baki fad'a mana sunan ki ba." Fiddausi tace, "Sunana Fiddausi nazo daga Kano." Aliya tace, "Ma sha Allah, Allah ya bamu zaman Lafiya , daman shigowa mukayi mu gaisa kuma mun gaisa zamu koma b'angaren mu" ta fad'a suna mikewa itama ta mike Fiddausi tace, "muje na raka ku nima sai naga wajan naku." Tare suka fito zuwa babban falon ta bi falon da kallo ganin yara k'anana dukkan su kusan kansu d'aya su biyar suna wasa.

Kallon yaran take yi ta kalli Aliya sai tayi murmushi tace, "Duka yaran kine, y'ay'an sane." Fiddausi ta sake kallon yaran tace, "Y'ay'an sa? Ba yaran sa bakwai ba?." Aliya sukayi dariya tace, "Zaki fahimci komai sai a hankali yanzu ko Mun fad'a miki baza ki yarda ba." Girgiza kai take yi tana kallon yaran zuciyar ta cike da wasi-wasi akan abinda suka fad'a mata amma bata nuna ba ta share zancen kawai.

Fiddausi ta sake kallon su tace, "Ina mijin namu kuma?." Naja'atu tayi dariya tace, "Ai ked ganin mijin nan naki yanzu kuma ai sai Allah." Fiddausi ta sake kallon su tace, "kuna yi min maganar da bana fahimta wallahi, ban gane ba fa.." Aliya ta dafa ta tace, "Zaki gane nan gaba ke zaki yiwa wata bayani in bama nan" ta fad'a tana shiga b'angaren ta ta bar Fiddausi a tsaye tana kallon su. Mamaki take ganin su ko kishi ma basa yi kamar y'an uwa sannan ga maganar da suke yi abaibai bata ganewa.

Juyawa tayi ta koma zuwa mata b'angaren ta d'auki wayar ta ta shiga kiran lambar sa dan sun jefa mata wasi-wasi a zuciyar ta, kusan sau biyar ta kira ba'a d'auka ba sai a na shidan aka d'auka kafin ayi magana tace, "Baby kana ina ne ina ta kiran ka baka d'auka? Na dawo gida kace min kuma jiya meeting zakayi har yanzu ba'a gama ba?."

Daga can b'angaren aka ce, "Ohh kece sabuwar amaryar kenan, Allah sarki baki san komai ba ai. Anyway bacci yake ki jira in ya tashi zan fad'a masa kin kira in da lokaci sai ya kira ki." Gaban Fiddausi ya fad'i jin muryar mace tana mata magana hankali kwance kamar wata matar sa ko kuma yar uwar sa kuma tana ce mata wai yana bacci Fiddausi tace, "wacece ke?." Tayi dariya tace, "shiyasa nace miki ke sabuwa ce ai,kar ki damu da sanin wacece ni zan zo na kwanta har a kan gadon ki, sai anjima" ta fad'a tana yanke wayar Fiddausi tabi wayar da kallo zuciyar ta na bugawa.

Hannun ta har rawa ta sake kiran sa ba'a d'auka ba ta sake kira aka d'auka kafin ayi magana tace, "Wacece ke kike tare da mijina har kike fad'a min wannan maganar?. Meye had'in ki dashi da zaki cemin yana bacci?."

"Ke Fiddausi! Tunda ta riga ta fad'a miki bacci nake ki yarda mana, bana son takura itama bata son takura da. haka kar ki sake kirana sai na neme ki. İn kud'i kike so ki duba account din ki zan saka miki yanzu amma bana son yawan yin waya."

Daga cikin wayar taji yarinyar tayi dariya tace, "Wallahi Sugar kana da abin dariya, Wato in kud'i take so..." duf taji an yanke wayar Fiddausi ta zame ta zauna a akan kujera kirjin ta na bugawa a bayyane tace, "Wai me yake faruwa ne haka?." Babu mai bata amsa tayi shiru tana tunani kafin ta tashi zuwa daki zuciyar ta duk ta cika da abubuwa iri-iri.

Yana yanke wayar yarinyar Alhaji Bello da yake dariya tace, "Naga alama yarinyar nan tana da rawar kai, in ban da raini da rashin mutunci bata yarda da abinda nace bane sai da ta kuma kiran ka?." Alhaji Bello ya taso daga inda yake daga shi sai karamin wando ko riga babu ta saka kusa da ita tana zaune tana busa sigari ya jawo ta jikin sa ko warin sigarin baya ji yace, "Haba Sugar, kin San sabuwa bata san wacece ke ba shiyasa, amma nan gaba in akace ta sake aikata abinda tayi bazata yi ba."

Ta hura masa hayakin a fuska tace, "ohh! Kenan har son da kake mata yayi yawan da zaka kare ta?." Yayi murmushi yace, "Ai kaf duniya in akwai wacce nake so to kece. Ina fad'a miki gaskiya ne da tasan matsayin ki baza tayi ba."

"Itama kana son ta tunda ka d'auko ta kawai dan ka kasa samun abinda kake so ne ya saka ka shata mata layi kamar sauran."

"Ke kin San ta badan ce a wajena." Ta kashe sigarin ta kalle shi tace, "Ban yarda ba, inda ni daban nake da bazata sake Kiran ka ba kamata yayi taji magana ta kamar yadda zata ki maganar ka, dan taga na bata dama Kun zauna a New York shiyasa take kokarin raina min hankali, Sugar ni yarinyar nan bata yi min ba sam."

Alhaji Bello yace, "Me kike so ayi mata? İn so kike a kora ta gıda yanzun nan wannan mai sauki ne." Ta girgiza kai tace, "Zan fad'a maka abinda za'a yi mata ina so ya banbance ta tabbatar ni ba sa'ar ta bace."

"An gama Sugar." Tana ji yana yawo da hannun sa jikin ta tace, "Sugar wai meye kake shafa ni?."

"Sugar Kari nake so, a taimaka min." Ta kalle shi tace, "kaje wajan amarya mana."

"Ai ni kece amaryar ta." Tayi dariya kad'an tace, "dadin baki." Ganin tayi dariya sai ya samu damar abinda yake so a lokacin suka aikata Zina suka aikata luwadi duk a lokaci d'aya.

Tare suka fito daga wanka a lokacin wayar Alhaji Bello ta sake yin k'ara yarinyar da take amsa suna Nabila ta k'arasa wajan wayar ganin mai kiran sai tayi dariya tace, "Sugar amarya ce fa, bara naji ne zata ce" ta fad'a tana d'aukar wayar. Daga can bangaren Fiddausi tace, "Baby wai kana ina ne? Ina son ganin ka yanzu dan Allah kazo. Wacece wacce kuke tare har take fad'a min magana?."

Dariya Nabila tayi jin abinda take cewa tace, "Ke wai bakya jin magana ne? Sau nawa zan maimaita miki in lokacin neman ki yayi zai neme ki?." A fusace Fiddausi tace, "Wai ke wacece da zaki dinga d'aukar wayar mijina in na kira shi? Wacece ke din sa da zaki cemin bana jin magana? Kin San wacece ni kuwa?."

Cire wayar daga kunne Nabila tayi tana kallon sa tana yamutsa fuska alamun maganar tayi mata k'arfi tace, "ni kike d'agawa murya?."

"Na d'aga miki, me zaki yi min?. Dallah malama ki bawa mijina waya ba ke nake nema ba." Nabila ya kalle shi tace, "Sugar kana jin abinda amaryar ka take cewa min ko?." Ya matso yace, "Sugar na fad'a miki sabuwa ce bata san wacece ke ba, bata san ma labarin ki ba amma yanzu zata sani kiyi hak'uri."

Fiddausi da take jin me yake cewa tace, "Baby wacece ita wai? Meyasa za'a bani labarin ta? Meyasa kake bata hak'uri?." Tayi murmushi tace, "Zaki gane wacece ni, ki shirya amsata a gidan ki ganin nan zuwa" tana fad'a ta yanke wayar ta kama k'ugu tare da daure fuska.

Hankalin sa ya tashi sosai ya m rud'e yace, "kinga Sugar nifa zan iya rabuwa da ita akan wannan b'acin ran naki, Kiyi hakuri dan Allah ki saki ranki ganin damuwar ki tana tayar min da hankali sosai." Ta kalle shi tace, "Ina so na nuna mata ni ba sa'ar ta bace da zata fad'a min magana haka har tana yi min tsawa."

"To me kike so ayi mata?."

"So nake yau mu kwana a gidan ta a kuma kan gadon ta nake so mu kasance da kai." Ya rike fuskar ta tace, "in akayi hakan zaki huce?."
Chapter 8 · 0% Book details