← Book details Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 93

Sashe 67

Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya Adam ya ma rasa abinda zaiyi masa shi kuma ya juya ya kalli Ameena da take tsaye a wajan yace, “eh Yusuf a wajan ki mai laifi ne babba, Yusuf a wajan ki mai kuskure ne, Yusuf a wajan ki abin ja baya ne, Yusuf a wajan ki dodo ne ni na sani Ameena. Amma ki yarda wancan Yusuf din da wannan Yusuf din akwai banbanci, wancan Yusuf din ya jima da mutuwa wannan wani sabo ne a gaban ki wanda yake so ki bashi dama shima ya wanke kuskuren wancan Yusuf din Ameena. Ameena bana iya bacci saboda tunanin ki, bana iya cin abinci, na daina zuwa ko ina ko yaushe ina kwance kece abincina kece ruwana kece kuma aikina. wani kuskuren sai bayan mun aikata muke ganewa munyi, wani kuskuren sai wani abun ya same mu muke ganewa mu dawo mu gyara, in muka gyara kuskuren kuma sai kiga yafi baya kyau. Allah yana sake bawa bayin sa dama a lokaci da suka yi laifi suka tuba yana sake basu dama ta biyu har ta babu adadi ma domin su wanke laifukan su. meyasa baza ki sake baki wannan damar ba Ameena? Meyasa baza ki amince ki yarda wancan Yusuf din yanzu bashi bane ba? Ko badan ni ba ki kalli y’ar mu gata a kusa dake dan Allah kar ki bari ta tashi ta girma a ba’a tsakanin iyayen ta ba.”

Muryar sa ta sarqe yayi shiru muryar na rawa yace, “ki yafe min dan Allah, ba dan ni ba koi sake bani wata damar ba, dan ni ba kodan saboda Zaytun gata a kusa dake.” Zaytun da ta fito a lokacin ta k’arasa ta zauna a jikin sa tana kallon fuskar sa tace, “mummy jini.” Yusuf ya rik’e ta a jikin sa yace, “ita kanta tana so ta kasance a tsakanin mu Ameena, meyasa kike so ki raba ta da iyayen ta tun tana karama?. Dan Allah ki bari ta tashi a cikin mu tasan dadin iyayen ta guda biyun in kika farraqa ta shikenan kin raba ta da Jin dadin da ko wanne da yake ji in yana cikin iyayen sa. Ameena na yarda ko dukana zaki yi kullum na yarda indai zaki sake bani dama, Ameena ko baza ki yi min magana kullum ba na yarda ki sake bani wata damar, Ameena koda zaki saka wuta ki kona ni na yarda na mutu a matsayin mijin Ameena ba’a tsohon mijin ta ba.”

Yayi murmushi yace, “kuskure nine kuskure da kansa ma ba aikata shi nayi ba. Amma dama ta k’arshe kawai Ameena ki taimaka kafin hankalina ya bar jikina” ya juyo ya kalli Yaya Adam da fuskar sa da take a jiqe da hawaye ga jini a gefen bakin sa yace, “na yarda na sab’a alqawarin Baba, amma a yanzu bazan sab’a alqawarin ka ba, zan cika dukkan alqawarin da kake so akan kula da ita kuma na tabbatar zanyi bazan sab’a ba, rana d’aya in na sab’a na amince ka sake raba mu da ita rabuwa ta har abada” ya dafe kana da yake sarawa sosai ya sake kallon Ameena da take hawaye tana tsaye a har lokacin bata zauna kafin ya sake magana tace, “ka daina wahalar da kanka Yusuf, ka daina b’ata bakin ka Yusuf, ka daina asarar hawayen ka, ni Ameena bazan koma gidan ka ba, ni Ameena bazan sake zama dakai ba, ni Ameena na barka har abada. Ga mijina nan a tsaye kana kallo shine wanda zan aura koda wasa kar ka sake kuskuren cewa kana sona domin zai d’auki mataki mai tsauri a kanka.”

Ya kalli Al’ameen da yake kallon sa gabad’aya ma shi bai gane fuskar sa ba har a lokacin dan ba tashi yake ba yace, “matakin da zaka d’auka d’aukar rai ne? To ka zama silar d’aukar raina a yanzu amma bazan fasa fad’ar ina son Ameena ba, bazan fasa fad’ar Ina son na mayar da ita ba.”
“Baza ka samu ba! Baza ka tab’a samun wannandamar ba Yusuf!!. Ta riga ta kubce maka kai da ita kuma har abada. Wacce irin dama ce ban baka ba a rayuwar ka? Wanne irin lokaci ne ban baka ba a zamana da kai?, duk wannan lokacin bai ishe ka ba wani sabo kake so na sake baka?. Ka manta dukkan abubuwan da ka aikata min ne Yusuf?.”

“Ban manta ba ina sane, ina sane Ameena shiyasa nake ce miki nayi kuskure amma zan gyara kuskuren in kika sake bani dama.”
“Bazai gyaru ba ka riga da ka lalata shi wallahi, bana sake fatan zama dakai a inuwa d’aya, ka rok’e ni Akan na yafe maka na kuma yafe maka matsayin ka na baban y’ata, amma ka cire wannan kudurin naka a zuciyar ka domin lokaci ya k’ure maka tuni ma.”

Ya ja numfashi ya sauke har lokacin yana rik’e da Zaytun yace, “shikenan Ameena, shikenan naji lokaci ya k’ure min na yarda nayi wasa da damata. Amma ki sake bani wani lokacin da wata damar.”
“Bazan bayar ba saboda na tsane ka! Bana sonka bana son mai sonka Yusuf, ka fita daga gidan nan ganin ka yana b’ata min rai, ganin ka yana sakawa naji kamar ana soya min zuciyata saboda tsanar ka da nake ji.” Kallon ta yayi da idanun sa jajaye dan har kukan ya k’afe yayi murmushi yace, “shikenan to Ameena, na gode da yafe min din da kika yi, zan tafi bazan so ganina ya dinga k’ona miki rai ba zan koma inda na fito yanzun nan. Amma ina so ki fad’a min kalma daya da ko na mutu a yanzu zan tafi da ita a zuciyata a matsayin kece kika fad’a min ita ba.”

Ameena ya sake fusata tace, “tsana, na tsane ka bana sonka shine abinda zance.” Yayi murmushi ya d’auke Zaytun daga jikin sa ya kalli Usman da yake hawaye shima ya kalli Al’ameen da ya cire glasses din fuskar sa ya kalli Yaya Adam yace, “kayi hak’uri Yaya zan tafi, ban dawo dan sab’a abind aakace min ba na dawo ne saboda zuciyata ta kasa hak’uri. Amma yanzu zan tafi tunda Ameena tace bata son ganina zan tafi watakila tafiya ce ta har abada, domin rasa ta daidai yake da rasa hankalina ni nasan da haka” ya fad’a yana tashi tsaye dakyar ya kalle su yace, “Kiyi hak’uri duk na b’ata muku rai da kuma lokaci, na gode da damar da kuka bani ta magana daku. Allah ya saka muku da gidan aljanna. Yaya na gode Allah ya jikan iyayen ka.” Ya juya ya kalli Al’ameen yace, “fatan nasara” daga nan ya kalli Usmsn yace, “muje Usman, yanzu na tabbatar da abinda kake cemin, lokaci na ya wuce dama ta ta k’are komai ya lalace min, bazan sake samun wata damar ba, nayi sake komai yazo k’arshe.” Usman ya rik’e hannun sa zasu fita kukan Zaytun ya karad’e falon ta bishi a guje ta rik’e shi ya d’ago ya kalli su sai ya rik’e hannun ta suka fita tare da ita.

#Mai daki
#Book3
#Nana Haleema
#paid
#500

Book3
035

Ameena zama tayi akan kujera tana kuka wanda ta kulle fuskar ta da hannun ta Anti Aysha da tun zuwan Yusuf ta fito ta zauna kusa da ita tace, “to meye na kukan kuma Ameena? Badai shikenan ba an rabu to meye na kukan?.” Ameena tace, “haushin sa nake ji walalhi, bana so naga yana kula koda Zaitun ne balle ni.” Anti tayi dariya tace, “to ya isa, Zaitun ai y’ar sace baki da ikon da zaki saka ya daina kuka ta, ya isa ki daina kuka.”

Yaya Adam yana tsaye har lokacin yana kallon Ameena kafin ya kalli Al’ameen da yake tsaye ya mayar da glasses din sa kafin yayi magana akayi kiran sallah suka fita Anty ta rik’e Ameena suka shiga ciki. Har suka idar suka tawo daga masallacin babu mai  magana a cikin su  sai Adam ne ya katse shirun yace, “Muna magana d’azu, ya kake ganin za’ayi da lokacin bikin nan?” Al’ameen ya sauke numfashi ya kalle shi yace, “ai bata kai ga fad’ar lokacin jarabawar ba.”
“Ko tana cikin jararbawa za’a d’aura auren, ka gama gyara gidan nan da y’an kwanaki kawai ayi a wuce wajan.” Al’ameen yace, “Allah ya nuna mana.” Ya amsa da amin suka cigaba da tafiya kowa amma akwai abinda yake cikin zuciyar sa.

      Usman kuwa kai tsaye asibiti ya wuce da Yusuf dan jikin sa  yayi zafi sosai baya cewa komai sai idanun sa da ya kulle kawai amma kana ganin sa kasan bashi da lafiya. suna zuwa kwantar dashi akayi aka yi masa allura da ruwa dan a samu zazzabin ya sauka a kuma samu jinin sa  da ya sake hawa ya sauka. Usman yana zaune a gefen sa Zaytun na kusa dashi tace, “daddy bashi da lafiya?.” Ya d’aga mata kai alamun eh tace, “daddy yana kuka?.” Ya girgiza kai alamun A’a ya kalli Yusuf da yake kwance tace, “an yiwa Daddy allura.” 

Sai ya rik’o ta jikin sa kawai baice mata komai ba ita kuma tana ta tambayar sa. Abbah ya iya Kira ya fad’awa halin da ake ciki bai fad’awa Ammah bama daga wajan aiki kai tsaye asibitin yaje ya samu Usman a zaune da Zaytun da tayi bacci tana hannun sa yace, “Usman me ya sake faruwa kuma?.” Usman yace, “Wallahi Abbah Yusuf yana son Ameena, wallahi ya gane kuskuren da in aka bari ta kubce masa zai iya rasa hankalin sa gabad’aya. Duk wannan halin ya shiga ta dalilin ta, ban tab’a ganin nadama a idanun Yusuf ba kamar cikin kwanakin nan, dan Allah Abba ka taimakawa Yusuf kafin ya zauce.”

Abbah yayi Ajiyar zuciya yace, “yau ma gidan Adam din kuka je kenan?.” Ya d’aga Abbah kai alamun eh Abbah yace, “ni ban san me zance ba gaskiya dan banza shiga maganar ba wallahi, in rabon sace zata sake dawowa in ba rabon sa bace ba yaje can ya samo wata in ya rasa hankalin ma daman Allah ya rubuta zai rasa hankali sa akan Ameena, hakan yana cikin littafin k’addarar sa.” Usman yace, “Abbah ayi wani abun dan Allah.” Abbah yace, “zan sanar da mahaifiyar sa tazo a ganshi” ya fad’a yana fita shi kuma ya zauna gadin Yusuf.
Chapter 67 · 0% Book details