Sashe 14
Mai Daki Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Amin Baba" ta amsa a hankali yace, "Tashi kije zuwa gobe zaki gane wanda na zab'a miki a cikin su." Ta tashi ta fita Umma ta kalli Baba tace, "Nasan zab’in ka Ibrahim ne ko?." Yayi dariya yace, "Kamar kin shiga zuciyata, daman bana so naji ta ambaci akasin Ibrahim wallahi, inda tace Umar zan amince mata saboda shine zab’in ta saboda babu yarda zanyi, amma yanzu da ta bani dama Ibrahim shine mijin ta in sha Allah." Umma tayi murmushi tace, "Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Ya amsa da amin yana cin abinci yana ji a zuciyar sa matsayin sa na uba na gari ya zabarwa y'ar sa miji na gari wanda baza tayi kuka ba ko bayan babu ransa zai mata miji kuma uba.
#Mai daki
#Book3
#Paid
#Nana Haleema
Book3
009
Rukayya haka ya koma d’aki jiki a sanyaye ta zauna ta dafe kanta cikin rashin sanin abinda zatayi Zuhra da yake gefen ta tace, “Yaya wa kika d’auka a cikin su?.” Rukayya ta kalle ta tace, “Zuhra ban san za d’auka wa zan bari ba.”
“Nidai nffi so ki d’auki Umar dan yafi Ibrahim din nan kudi.”
“Ba kudi ne a gabana ba Zuhra, kawai ki taya ni da addu’a Allah ya zab’a min wanda yafi alkhairi.”
Zuhra tace, “To Amin. Allah yasa a had’a bikina da naki.” Murmushi kawai tayi ta tashi ta shiga band’aki. Haka ta kwana cikin tunani kuma cikin ikon Allah a daren babu da wanda suka yi magana dashi a cikin su babu wanda ya Kira ta sai hankalin ta yafi kwanciya tayi bacci cikin tunanin wa Baba zai bata a cikin su?.
Tana zaune akan kujera tana kad’a k’afar ta kamar Kullum jikin ta kaca-kaca riga daban zani daban tana danna waya, Yusuf ne ya shigo kallo daya zaka yi masa ka tabbatar da ramar da yayi a bayyane ya kalle ta yace, “bakya ji ina yi miki magana ne?.” Ta d’ago ya kalle shi tace, “naji kawai babu amfanin na amsa ne, amma yanzu da kazo da kanka ai Gashi kasan ina jin ka.”
Mamaki shi hana shi magana yake yi in tana yin wani abun kamar itace mijin shine matar haka take masa gadara Akan komai yace, “Kina ji babu amfanin kiyi magana haka kika ce fa.” Ta sake cewa, “to meye amfanin ka maimaita min nasan abinda kaji shine abinda nace.”
“Asiya wannan wanne irin iskanci kika d’auko ne? Ni zaki dinga yiwa rashin kunya an fad’a miki sa’an ki ne ni?.” Kallon sa tayi sai ta juya tayi tsaki ta cigaba da abinda take yi.
Kwace wayar yayi daga hannun ta a fusace yana kallon ta yace, “Dan iskanci ni kin yiwa tsaki?.” Ta sake yin wani tsakin bai ssn ya tsinke ta da Mari ba sai ganin ta yayi ta mik’e tsaye a fusace tana kallon sa shima haka tace, “Ni ka Mara Yusuf?.”
“Na mare ki ko zaki rama ne?.”
“A yanzu bazan rama ba wallahi ka sake dukana sai na rama, ai ba’a kawo ni dan ka dinga dukana ba.”
“Allah yasa ki sake yin abin dukan ki gani in ban mare ki ba, ni zaki mayar dan iska ki dinga yi min tsaki kamar kece mai gidan nice matar?. Ya zan dinga ajjiye kud’i a gidsn nan daga ni sai ke na dinga neman su ina rasawa? Ina suke zuwa?.”
“K’afa ce dasu fita suke yi. kaga malam ni ba irin uwar gidan ka da ta fita bace bana sata ban iya sata ba. Kaje can ka nemi inda ka ajjiye kud’in ka amma ba a wajena ba.”
Yusuf ya bita da kallo ganin sai wani jijjiga jiki take yi cikin rashin kunya yace, “in bake ce kike d’auka ba to waye?.” A fusace tace, “Wannan kuma kai ka sani, ni dai ba barauniya bace ba kaje can ka samu b’arauniyar ka. Haka kawai kaje a b’ata maka rai ka zubar da kudin ka zaka zo ka wuce a kaina? To wallahi nidai ka sake mari na sai na ra….” Kafin ta gama fad’a ya sake tsinke ta da mari dan yaga zata rama din ta tsaya tana kallon sa shima ya kalle ta sai kuma yayi tsaki ya juya ya fita ransa a b’ace sosai.
Ransa a b’ace yake sosai ko kallon gaban sa bayayi yadda ya kamata ya fita zai shiga b’angaren Ameena mai aikin Ameena Baba Habi ta tsayar dashi tace, “Alhaji barka da Rana.” Ya tsaya ya kalle ta yace, “Baba Habi an tashi lafiya?.”
“Lafiya lau Alhaji. Dama akan maganar zaman gidan nan, Tunda hajiya bata gidan nan gaskiya zamun mu a gida…..” kafin ta k’arasa magana suka ga Asiya ya fito wajan a fusace tana fadin, “wallahi ka sake saka hannu ka dake sai na nuna maka ni ba irin wacce zaka daka ta kyale bace, ni zaka kalla kace nayi maka sata? Kudin me zaka shigo dashi da zan d’auka?. An fad’a maka ni irin banzar Uwar gidsn kace da zaka dinga yiwa abinda Kaga dama tana kyale ka? To wallahi ni baka isa ba domin kuwa daidai nake dakai.”
Jikin Yusuf sanyi yayi sosai ya kalli su Baba Habi da suke tsaye suna kallon Asiya ya kalli mai gadin sa yaga duk suna kallon abinda yake faruwa sai ya kulle ido ya bud’e jikin sa gabad’aya ya mutu domin kuwa ba’a tab’a wulak’anta shi a duniya ba kamar yadda Asiya tayi masa yanzu. Ba’a tab’a yi masa tozarcin da tayi masa ba a wannan lokacin, ba’a tab’a yi masa abinda ta aikata masa ba shiyasa ya kasa yin ko motsin kirki ya kulle idanun sa kawai.
Bai kula ta ba ganin baiyi magana ba tace, “kayi magana mana ko ka sake dukana kaga in ban rama ba, Aikin banza aikin wofi, na d’auka rashin kunyar taka taje inda taje take, na d’auka zaka kuma dukan nawa dana nuna maka yadda ake zallar hauka wallahi.” Kallon ta yayi yace, “Koma ciki.”
“Bazan koma ba ai ba kai ka fito dani ba daman, ka jira duk sanda naso komawa zan koma.” d’auke kai yayi daga kallon ta kawai ya shiga b’angaren Ameena ba tare da ya sake cewa komai ba dan ya Lura in ya cigaba da kula ta zata iya yin kokawa dashi a gaban ma’aikatan gidan sa.
Koda ya shiga rasa abinda zaiyi ma yayi gabad’aya komai baya yi masa dad’i ransa a b’ace yake sosai, kamar shi Asiya zata fito gaban masu aiki tana yi masa hauka dan kawai ta wulak’anta shi?, abinda bai tab’a faruwa dashi ba tun da yake zaune a gidan. Falon yake k’arewa kallo kamar mai neman wani abun komai yana nan yadda yake sai k’ura da falon yayi amma babu komai da yake ajjiye komai yana mahallin sa hatta khamshin turaren falon bai fita ba dan ya Riga ya kama d’akin sosai.
Hoton sa da ita da Zaytun ya gani dukkan su sunyi dariya yayi saurin d’auke kansa zuciyar sa na mugun harbawa ya bar wajan yana ji kamar ya zubar da hawayen da bai san dalilin su ba.
Asiya tana komawa gida waya ta kira Umma na d’auka tace, “Umma na gaji da d’agawa Yusuf wallahi, yau mari na yayi har sau biyu na rantse da Allah ya kuma dukana Umma sai na rama.” Umma daga can b’angaren tace, “Me kika yi masa da ya mare ki?.”
“Wai ina kudin sa da ya ajjiye suke zuwa in ya ajjiye baya ganin su, kuma ta kud’in dana turo miki ne aka yi hidimar kawo kudin Fauziyya shine fa yazo yake d’aga min murya harda mari na.”
Umma tace, “kuma kina jinina namiji ya d’aga hannu ya mare ki ki zauna kina kallon sa?, ai kafin ya sauke hannu kema yaji naki hannu a fuskar sa. Ke dan fa Muna son zaman ki da Yusuf ba hakan yana nufin ya saka hannu dake ki mu kyale shi bane, ai duka baya cikin zaman aure, in ya dake ki tabbatar kafin ya sauke kema Kinyi abinda zai ji zafi a tasa fatar shine ya jawo. Na Riga nayi masa abinda bazai iya yi miki ko barazanar komai ba bazai tab’a iya sakin ki ba ko yace kije gida, kar ki sake kuskuren Bari ya dake ki koda nan gaba domin zai samu lagon sake dukan naki a nan gaba.”
Asiya tace, “Ai na fad’a masa wallahi ya sake dukana sai na rama, nifa Umma so nake na mayar dashi tamkar Keda Baba, sai abinda kike so za’a yi amma ni naga yak’i koma min haka.”
“Sai a hankali, shima baban naki ai ba lokaci d’aya ake samu abinda ake so ba, zaki same shi fiye da yadda na samu mahaifin ki kedai kar ki cigaba da yin abinda nace sannan koda wasa banda duka.”
Umma ta sake cewa, “shinkafar mu fa ta kare ki san abinda zaki yi.” ASiya tace, “yak’i koya min mota ne wallahi da yanzu na zubo su a baya na kawo babu wanda yasan meye na kawo miki har gida, amma zan aiko da kud’i sai a siya.” Umma tace, “yayi” Daga nan ta kashe wayar Asiya na sake girgiza jiki da tabbatar da ya sake dukan ya wallahi sai ya rama.
Bayan kwana biyu.
Fiddausi ta rame sosai tun bayan da suka rabu da Alhaji bata sake ganin sa ba har aka kwana biyu kullum sai ta Kira shi amma baya d’auka sai dai taga gajeren text in taci sa’a yace ta duba account ya saka mata kud’i. Tun abun baya damun ta har ta kawo damun ta yake yi ta kasa sukuni har ta kai ga ta fara ramewa. Duk abinda ya faru a baya ta d’auka mafarki ne tak’i gasgawata ko zuciyar ta naso gagagata abun sai ta kawar da tunanin.
A daren ranar tana zaune a falon ta tsahon kwana biyun su Aliya basu zo ba itama kuma bata je ba tana zaune ita kad’ai cikin tunanin da ta fara saka kanta a ciki.